Sakonnin Masu Karatu (2014) (16)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

71

Assalamu alaikum Malam, don Allah me ke sawa a gajeren zangon sadarwa na kwamfuta, wasu kwamfutocin na iya hawa Intanet, amma wasu ba su iya hawa?  Meye dalilin hakan?  Daga: 08036823562

Wa alaikumus salam, wannan na iya faruwa sanadiyyar cirewar wayar kebul da ke like da kwamfutar, ko cirewar wayar kebul da ke like da na’urar Router da ke sadar da zangon da giza-gizan sadarwa ta Intanet, ko kuma daukewar yanayin sadarwa gaba daya daga kamfanin da ke sadarwa da zangon da Intanet, wato “Service Provider” kenan.  Idan dukkan wadannan lafiya lau suke, ana iya duba kwamfutar da  ba ta iya hawa Intanet a gani, watakila matsalar daga kwamfutar ce, ko da kuwa wayar kebul din na makale a jikinta.  Uban zangon sadarwa, wato Network Administrator, shi ne kadai zai iya yin hukuncin karshe kan matsalar.  Da fatan an gamsu.


Allah gafarta Malam, wai da gaske ne idan aka dora laptop a kan cinya hakan kan haddasa wata cuta? Daga: 07031648855

A gaskiya ban sani ba.  Na sha samun tambayoyi makancin wannan, kuma a iya bincike na, ban taba cin karo da wasu bayanai masu alakanta hakan da kwamfuta ba kai tsaye daga kwararru kan harkar lafiya da kwamfuta.  Ire-iren wadannan bayanai galibinsu jita-jita ne, ciki har da wanda ke cewa yawan amfani da wayar salula na haddasa cutar sankara (Cancer).  Har yanzu babu wani bincike na musamman, abin dogaro a wajen kwararru kan ingancin wannan ikirari.  Da fatan ka gamsu.


Salaamun Alaikum, gaskiya na yaba da kokarinka.  Kuma don Allah ka mini bayanin yadda zan samu haruffan Hausa masu lankwasa a kwamfuta ta.  Allah saka da alheri, amin.  –  Muhammad Sani Garba.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Muhammad Sani.  Bayani kan haka ya gabata a kasida ta musamman mai take: “Akwai Haruffan Hausa Masu Lankwasa a Cikin Kwamfutocin Zamani.”  Amma ga alama baka ci karo da wannan kasida ba.  Bayan kai akwai da yawa cikin masu karatu da suka sha mini wannan tambaya a wurare da dama da muka hadu dasu.  Wannan yasa nace zan samar da lacca ta musamman ta bidiyo mai dauke da dukkan hanyoyin, wanda zan dora a Intanet ga duk masu bukata, in Allah ya yarda.  Ga dai bayanin nan a takaice.

- Adv -

Idan kana da masarrafar taskance bayanai mai suna: “Microsoft Word 2007,” ko “2010,” ko “2013,” (duk tsarin iri daya ne) ka bude, sai kaje bangaren “Insert” dake sama, hagu maso dama, ka matsa.  Da zarar bangaren ya budo, sai kaje can kuryar dama a karshe, za ka ga sashen “Symbols”, mai dauke da abubuwa biyu; “Equations” da “Symbols”.  Ka matsa na karshen, wato “Symbols” kenan.  Da zarar ka matsa wani dan karamin shafi zai budo, mai dauke da wasu haruffa ko alamomi wadanda a baya ka taba amfani dasu, a can kasansu kuma za ka ga: “More Symbols”, sai ka matsa.  Shafi babba zai budo, mai dauke da dukkan haruffan da kwamfutarka ke dauke dasu baki daya.  Wannan cibiya ce ta musamman, wacce ke dauke da haruffa da kuma alamomin rubutu, da isharorin da kwamfutarka ke iya fahimtarsu da bayyana su a duk sadda aka shigar mata da bayanai masu dauke dasu ko irinsu.

Idan wannan babban shafi ya budo mai dauke da wadannan haruffa, za ka ga bangarori guda biyu ne a sama.  Bangaren farko shi ne: “Symbol”, wanda ke bude kenan.  Bangare na biyu kuma shi ne: “Special Characters,” wato alamomi da isharori na musamman da kwamfutar ke dauke dasu.  A bangaren farko, wanda shi ne inda damuwarmu take, ka duba can kasa, za ka ga: “Character Code,” wato isharorin da kowane harafi ke wakilta kenan.  Wannan mahalli shi ne hanya mafi sauki na samun haruffan Hausa masu lankwasa, idan ka san lambobin dake ishara ga kowane harafi kenan.  Amma idan baka san lambobin ba, sai ka rika bin haruffan dake shafin daya-bayan-daya, don nemo harafin da ya dace da abin da kake nema.

Amma don sawwakewa, na ciro maka dukkan lambobin dake wakiltar dukkan haruffan Hausa masu lankwasa. Don haka, ka zarce wajen “Character Code” kai tsaye, sai ka shigar da 0257 a inda lambobin nan suke, sai ka matsa “Enter” a jikin allon rubutunka, nan take za a kawo maka karamin harafin d mai lankwasa, cikin shudin launi.  Sai ka matsa “Insert” dake can kasar shafin, za ka ganshi a shafin masarrafar “Microsoft Word” dinka dake bude.  Sai ka sake shigar da 0253 don samun karamin harafin b mai lankwasa, ka shigar da 0199 don samun karamin harafin k mai lankwasa.  Wadannan kananan haruffa masu lankwasa kenan.

Idan kana bukatar manyan haruffa masu lankwasa kuma, sai ka shigar da 018A don samun babban harafin D mai lankwasa, ka shigar da 0198 don samun babban harafin K mai lankwasa, sannan ka shigar da 0181 don samun babban harafin B mai lankwasa.  Wadannan su ne haruffan Hausa masu lankwasa gaba daya, kuma duk suna cikin babban manhajar “Windows,” tun daga “Windows Vista” har zuwa “Windows 8.”  Dukkansu suna rukunin “Latin Unicode Character” ne.

Ga hoton dukkan wuraren da kake bukatar shiga nan cikin sauki; hoton farko daga dama, bangaren “Insert” ne, na biye dashi kuma na bangaren “Symbol” ne, na kasa daga hagu na bangaren haruffan da kayi amfani dasu ne a baya (idan ka lura za ka ga haruffan Hausa masu lankwasa, haka ya faru ne saboda ban jima da yin amfani dasu ba), a bangaren karshe kuma za ka ga babbar cibiyar haruffa, inda a nan ne za ka zabi dukkan haruffa ta hanyar bincike daya-bayan-daya, ko ta hanyar shigar da lambobin dake ishara gare su, kamar yadda muka yi.

A karshe, kana iya cewa ai hanyoyin suna da yawa kuma ga nisa, idan doguwar kasida nake rubutawa yaya zanyi?  Na dinga kai-komo kenan wajen shigar da kowane harafi idan nazo kansa?  Amsar ita ce eh, amma kuma akwai hanya mafi sauki da za ka iya amfani da ita wajen “koya” wa kwamfutarka fahimtar kowane harafi a yayin da ka matsa wasu maballai dake jikin allon shigar da bayananka, wato “Keyboard.”  Dabarar dake sawwake haka ita ake kira “Macros,” kuma hakan na cikin bayanan da zanyi cikin bidiyon da zan fitar ba da jimawa ba in Allah yaso.  Domin abu ne dake bukatar a karantar dashi a aikace, kana gani.  Amma ta hanyar rubutu kadai bazai gamsar ba.  Da fatan za ka yi hakuri da abin da ya samu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.