Sakonnin Masu Karatu (2014) (19)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

61

Assalamu Alaikum Abban Sadik, ni so nake ka bambance mini tsakanin “Windows” da “Android” wacce ce tafi sauri wajen shawagi a duniyar Intanet?  – Dalibinka, Aminu Muhammad

Da farko dai wadannan sunaye da ka kawo duk sunayen babbar manhajar wayar salula ne, wato Mobile Phone Operating Systems, wadanda a wannan zamani ake ji dasu a matsayin manyan manhajojin da wayoyin salular zamani ke amfani da su wajen aiwatar da sadarwa ta kowace hanya.

Babbar manhajar Android asali na kamfanin Google Incorporated ne dake kasar Amurka, ta hadin gwiwa da wasu kamfanonin waya da harkar sadarwa kusan goma. Tana daga cikin shahararrun babbar manhajar wayar salula da ake ji dasu a duniya a yau. Sadda kamfanin Nokia ya saye kamfanin Symbian da ke baiwa sauran kamfanonin waya irin su Samsung da LG da Motorola lasisi, sai suka koma kan wannan babbar manhaja ta Android. Ga dukkan alamu, wannan na daga cikin abin da ya daga su, har a karshe suka shallake kamfanin Nokia a kasuwar wayar duniya baki daya. Nau’in wannan babbar manhajar waya dai ita ce Android Jelly Bean 4.3.

- Adv -

Ita kuma babbar manhajar waya ta Windows Mobile na kamfanin Microsoft ne dake kasar Amurka, wato babban kamfanin kera manhajar kwamfuta da yafi kowanne girma da kudi da tasiri a harkar sadarwar zamani a duniya kenan. Wannan babbar manhaja a halin yanzu tana kan manyan wayoyin salula na kamfanin HTC, da Nokia. Kuma galibin wayoyin salula na kamfanin Nokia da ake ji dasu a duniyar yau irin su Lumia 1020, da Lumia 920, da Lumia 720, da Lumia 620, da Lumia 520 duk suna dauke ne da wannan babbar manhaja ta Windows Mobile. A halin yanzu wannan kamfani na Microsoft ya saye bangaren kera wayoyin salular kamfanin Nokia baki daya. Wannan ke nuna cewa nan gaba duk nau’ukan wayoyin salula masu dauke da sunan kamfanin Nokia za su rika zuwa ne da babbar manhajar Windows Mobile.

Bambancin da ke tsakanin wadannan manhajoji dai a fili yake, duk da cewa akwai abin da ya hada tsakaninsu. Abin da ya hada tsakaninsu shi ne, dukkansu manhajojin wayar salula ne masu dauke da siffofin da ke baiwa wayar salula dabi’un kwamfuta, wato Smartphone. Ire-iren wadannan dabi’u kuwa su ne; manhajar Imel dawwamammiya mai iya isar da sakonnin Imel ga mai waya nan take ba sai ya shiga manhajar ba. Sai manhajar hadawa da tarawa da kuma tura bayanai masu inganci, irin su hanyoyin karanta jaridu, da shafukan abota – irin su Facebook, da Google+, da Instagram da sauransu – da nagartacciyar fasahar Bluetooth, da nagartattun hanyoyin aika sakonnin tes da hotuna da bidiyo, da kuma hanyoyin mu’amala da kwamfuta kai tsaye, musamman ta hanyar tsarin Mini USB Ports, sai uwa uba nagartacciyar hanyar sadarwa ta Intanet.

Abin da ya raba tsakaninsu kuma shi ne; kowanne daga cikinsu na da wasu masarrafai ko tsare-tsare wadanda suka kebanci kamfanin wayar da ya kera su. Misali, babbar manhajar waya ta Android da ke kan wayar salula na kamfanin Samsung, da wanda ke kan wayar salula na kamfanin LG, asalin tsarinsu daya ne.

Ingancinsu wajen mu’amala da fasahar Intanet kuma wannan ya danganci abubuwa da dama.  Kowannensu na da inganci wajen sadarwa, tunda dukkansu manyan manhajar “Smartphones” ne; duk da cewa mataki-mataki suke.  Bambancin bai da wani girma sosai.  Wannan kan wayar hakikanin wayar kenan. A daya bangaren kuma, dole mu lura da yanayin sadarwa na kamfanin waya, da yanayin sadarwa na Intanet din kamfanin waya.  Domin idan babu inganci a bangarensu, duk girma da ingancin kwarangwal din wayar salula ba za ta iya tabuka komai ba a fagen sadarwa ko alaka tsakaninta da giza-gizan sadarwa na duniya.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.