Sakonnin Masu Karatu (2014) (3)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

49

Assalamu alaikum Baban sadik, da fatan ka wuni lafiya.  Dazu na kalli shirin Kimiyya da Fasahar Sadarwa a Sunna TV, shi ne na samo adireshinka a Dandalin Facebook.  Yanzu haka na zama mamba na shafinka.  Na ji dadi sosai Allah ya saka da alheri bisa wannan kokari da kake yi wajen wayar dakan musulmai da ma duk mai jin harshen Hausa.  A karshe, ina so ka dan yi mini karin bayani game da wasu manhajoji  na Google Store.  Idan inaso in sayi manhaja, sukan tambayeni “Credit Card Number,” idan nasa sai abin yaki yi; alhali katin ATM di na nau’in Mastercard ne.  Yaya zan yi ne?  – Nafiu Sabo Katata, Azare, Bauchi State

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Nafi’u. Ina godiya da addu’o’inku, Allah karba, ya kuma saka muku da alheri baki daya.   Dangane da batun sayan hajoji kamar su masarrafai ko manhajoji ta cibiyar cinikayya na Google Store ko Play Store misali, dole ne ya zama ka taskance bayanan katinka a wayar, ta hanyar manhajar da kake amfani da ita wajen kaiwa ga wadannan manhajoji.  Ma’ana, idan ka fara amfani da waya mai dauke da Android, kafin ka shiga Play Store sai ka sa adireshin Imel dinka, da kalmar shiga (Password).  Daga nan za a riskar da kai zuwa inda manhajoji suke.  Akwai wata ‘yar karamar manhaja  mai suna Google Wallet da ke dauke cikin tsarin Android.  Da ita za ka yi amfani wajen shigar da sunanka, da adireshinka, da kuma bayanan da suka shafi katinka.

A duk sadda ka tashi sayan wata haja, nan take za a riskar da kamfanin da zai sayar maka da hajar zuwa wannan lalita ta Google, wato Google Wallet, don ya dauki bayanan da suka shafi katinka kafin a aiwatar da cinikin.  Idan kuma baka taskance wadannan bayanai a Google Wallet ba, to shi ne dalilin da ke sa idan ka tashi sayan haja, sai a bukaci ka sake sa kalmomin sirrinka (Password) na Imel, sannan a bijiro maka da dan karamin fam da ake son ka sa lambar katinka na ATM, da kuma lambobi guda uku ko shida dake bayan katin.  Wadannan lambobi su ne ake son ka shigar dasu a inda aka rubuta “CSV” misali.

Bayan ka shigar da bayanan katinka da sunanka, nan take za a tuntubi kamfanin da ya bayar da katin (misali, Mastercard, ko Visa).  Idan kamfanin ya tantanceka ba matsala, sai kuma kamfanin da kake son sayan hajarsa ya sako maka hajar, a daidai lokacin da kuma ake cire farashin hajar da ka saya. Kusan lokaci guda za ka samu hajar da kuma sakon sanarwa daga banki cewa an cire dala kaza daga taskarka.  Domin cinikayya a wannan yanayi yana faruwa ne cikin dalar amurka ba nairan Najeriya ba.

A wasu lokuta kuma kana iya cike wadannan bayanai gaba daya, amma a ce maka cinikayya bazai yiwu ba.  Manyan dalilai guda biyu ne ko uku.  Na farko, watakila babu isasshen kudi a cikin taskarka da zai iya sayan hajar.  Idan akwai isasshen kudi da zai iya sayan hajar amma cinikayya ya ki yiwuwa, sai dalili ba biyu.  Shi ne, ta yiwu kamfanin da ya buga katinka ba shi daga cikin kamfanonin da ake karbar katukansu wajen cinikayya a wannan mahalli.  Idan yana daga cikin kamfanonin da ake karban katukansu, amma kuma cinikayya bai yiwu ba, to, ta yiwu kamfanin da zai sayar maka da hajar ba ya karbar kwastomomi daga Najeriya.  Domin ba dukkan masu sayar da hajoji ta Intanet ‘yan kasuwa ke yarda da masu sayan haja daga Najeriya ba, saboda dalilan tsaro, kamar yadda na san ka sani ba sai na yi wani karin bayani ba.  Domin bai wuce shekaru 5 da suka gabata ba da aka fara yarda da ‘yan Najeriya a yanar gizo wajen harkar kasuwanci.


Assalamu alaikum, Allah ya gafarta wa Malam. Ina da tambaya! Ta yaya kamfanin sadarwa wato (Telecom network) suke gane kalar wayar da mutum yake amfani da ita, kuma har suke turo wa mutum sakon Settings na Intanet?  –  Uzairu Abdullahi

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Uzairu. Ina godiya matuka da addu’a. Allah saka da alheri.  Da farko dai, sabanin yadda ka fada, kamfanonin waya ba su iya gane kala ko launin wayarka, sai dai nau’in wayar.  Wannan kuma na faruwa ne daga irin na’urar da suke amfani da ita wacce ke aikin sadar da mutane ta hanyar lambobinsu, da kuma tsarin da na’urar ke amfani da shi mai suna USSD, wajen aiwatar da sadarwa tsakanin kamfanin waya da mai waya.  Misali, idan ka bukaci sanin balas dinka, da zarar ka latsa *556# a MTN misali, nan take wannan na’ura za ta cillo maka yawan kudin da ya rage a layinka.  Haka idan ka bukaci wani abu daban ta hanyar shigar da wasu lambobi da kamfanin waya ya bayar, wannan na’ura ce ke da alhakin maido maka da jawabi.

- Adv -

Ita wannan na’urar, an gina ta ne ta yadda duk wata wayar salula idan tana dauke da katin wayar kamfanin waya, nan take wannan na’ura za su fahimci juna tsakaninta da wayar, kai mai rike da waya ba za ka sani ba.  Sannan kuma tana iya taskance bigiren da kake dauke da wayar, wanda ke dauke da layin kamfanin wayar.  Shi yasa, da zarar ka tura lambobin bukatar tsarin mu’amala da Intanet, wato Configuration Settings, nan take sai wannan na’ura tai amfani da bayanin nau’in wayarka, ta zabo wanda ya dace da ita, ta cillo mata.

Idan wayar da kake dauke da ita ba ta daga cikin jerin wayoyin da ke iya karban sako daga kamfanin waya, nan take wannan na’ura za ta sanar da kai.  Amma a wannan karon, maimakon ta cillo maka tsarin, sai dai ta sanar dake cewa: “Wannan waya ba za iya karbar sakon tsarin mu’amala da fasahar Intanet ba.”  Da fatan dai ka gamsu.


Assalamu alaikum Malam, ni shawara ce nake so in baka wadda za ta taimaka ma alummar arewacin Najeriya.  Malam, ya kamata ka bude makarantar koyon kwamfuta.  Domin ci gaban mu matasa na wannan yanki. – Umar Musa Barde

Wa alaikumus salam, Malam Umar wannan shawara ce mai kyau, kuma duk da cewa ina da wannan kudiri, amma a halin yanzu ba abu bane mai yiwuwa a gare ni.  Akwai mai gidana mai suna Malam Salisu Webmaster dake garin Kaduna.  Ya bude makaranta na musamman wacce ke tallafa wa matasa maza da mata wajen tabbatar da wannan kudiri.  Don haka, duk wanda ke da sha’awa yana iya tuntubarsa; ko dai ta shafin Facebook ko kuma ta inda makarantar take. Allah sa mu dace, amin.


Assalamu alaikum, ina gyaran kwamfuta ne, amma na kasa shiga Set Up na Toshiba. Na yi amfani da F2 da F12 amma ina!  Kuma ba laifin allon shigar da bayanai bane. Dan Allah a taimaka  –  Musa KB

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Musa KB. Sabanin yadda kace ka yi amfani da maballan “F2” da “F12” amma abin ya ki, galibin kwamfutocin Toshiba ana iya shiga BIOS Setup dinsu ne ta hanyar matsa maballin “F1” ko “esc” a daidai lokacin da ta fara kunnuwa.  Idan kuma nau’in “Toshiba Equium” ce sai ka matsa maballin “F12.”  Wadannan shahararrun maballan da ake amfani dasu wajen shiga BIOS Setup na kwamfuta nau’in Toshiba kenan.

Bayan haka, yana da kyau ka san cewa, galibin kamfanonin kera kwamfutoci a yanzu sukan canza tsare-tsaren da suke wa kwamfutoci daga wadanda aka sani a baya zuwa wasu daban.  Don haka, idan sabuwa ce kana iya duba kundin da tazo dashi, wato System Manual, don ganin yadda ake shiga.  Idan kuma tsohuwa ce ko mai matsakaicin shekaru, sai ka yi amfani da maballan da na zayyana a sama. Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.