Sakonnin Masu Karatu (2016) (13)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

269

Assalamu alaikum, barka da warhaka, ina fatan kana lafiya.  Allah ya kara basira, amin. Tambayata ita ce, don Allah yaya ake “Flashing” din waya ba tareda an hada ta da computer ba?  Sannan, ta yaya za ka samu kudi daga amfani da gidan yanar sadarwarka na ka ta hanyar samar da tallace-tallace? Daga: Auwal Adam SJ: auwaladammaisaga@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Auwal.  Ina godiya da addu’o’inku.  Zan fara da tambayarka ta biyu, kan yadda mutum zai iya samun kudaden shiga na halal ta hanyar gidan yanar sadarwarsa ta Intanet, wato: “Website.”  Hanya mafi sauki kamar yadda ka ayyana kai kanka, shi ne ta hanyar sanya tallace-tallace a shafinka.  Kana iya yin haka ta dayan hanyoyi biyu; ko dai ka nemo tallace-tallace daga kamfanonin da ka sani, a nan Najeriya ko a waje, sai ka kintsa bayanan tallace-tallacen da ka samu, tare da dora su a shafinka.  Ko kuma, a daya bangaren, ka karbi wannan aiki daga kamfanin Google ta amfani da tsarinsu mai suna: “Google Adsense.”  Wannan tsari na biyu shi yafi sauki.  Domin ba ruwanka da kamfanonin dake bayar da tallace-tallacen, sai dai ka karbi tallar ta hanyar dillancin kamfanin Google.  Idan lokacin biyan kudi yayi, su za su biyaka kai tsaye.  Ba ruwanka da wadancan kamfanoni da aka sanya maka tallarsu a shafinka.

Idan wannan tsari kake son bi, sai ka shirya.  Da farko dole ya zama kana da adireshin Imel na kamfanin Google, wato “Gmail” kenan.  Domin da shi ne za ka yi rajista.  Abu na biyu, sai ka zarce shafin da aka tanada don aiwatar da wannan kasuwanci, don yi rajista.  Za ka samu shafin ne a wannan adireshin: www.google.com/adsense.  A wajen rajistan ne za a bukaci ka bayar da sunanka, da adireshin gidan yanar sadarwarka (Website Address), da kuma bayanin taskar ajiyarka ta banki.  Idan ka gama mika wadannan bayanai, za a bukaci ka dakata na wasu ‘yan takaitattun sa’o’i.  Abin da za su yi shi ne, za su aika manhaja ce ta musamman tayi nazarin shafinka, da irin bayanan da shafin ke dauke dashi, da harshen da ka rubuta bayanan, da kuma irin jama’ar da suke ziyartar shafin.  Amfanin wannan shi ne, zai basu damar sanin wasu irin nau’ukan tallace-tallace ne za su baka kasa a shafin, don samun natija.

Da zarar sun gama za su tuntubeka kai tsaye (ta hanyar Imel kenan), don sanar da kai mataki na gaba.  Wannan mataki kuwa bai wuce kaje shafin da suka tanada maka a wajen rajista ba (wato “Profile”) don karbar gundarin bayanan da za ka zuba a shafinka.  Wadannan bayanai suna siffar yaren manhajar kwamfuta ne (wato: Codes).  Daman kafin wannan lokaci, za su tambayi a ina kake son sanya tallace-tallacen a shafinka?  Ma’ana, a bangaren shafinka a sama, ko kasa, ko bangaren gefen hagu ko dama?  Kowane bangare yana da nau’in bayanan da suka dangance shi.  Da zarar kwafi wadancan bayanai ka zuba a inda aka umarceka, nan take kana hawa shafinka za ka ga tallar da aka sa.

A yayin da wadannan tallace-tallace ke makale a shafukanka, haramun ne, zan maimaita, haramun ne ka matsa ko latsa kowanne daga cikinsu.  Babu ruwanka dasu.  Masu ziyarar shafinka ne ake son su gani, idan ya birgesu, su latsa.  Da zarar sun matsa wadannan tallace-tallace, nan take za a zarce dasu shafin mai tallar, kai tsaye.  Wannan latsawa ko matsawa da masu ziyara keyi, da shi ake lissafa maka hakkinka.  Haka kudin zai ci gaba da taruwa, kadan-kadan.  Da zarar ya kai dala 100 ($100), sai su antayo maka su cikin taskar ajiyarka ta banki da ka basu.

Don haka, iya yawan jama’ar da suka latsa wadannan tallace-tallace, iya yawan abin da za ka samu.  Sharadin biya shi ne, na farko, kada ka matsa tallace-tallacen dake shafinka.  Idan ka matsa, za su gane.  Kada kaga kamar ba ka kusa dasu.  Ko da wace irin na’ura kake amfani, a hankali za su gane.  Idan kuwa ka yarda suka gane cewa kana matsa tallace-tallacen dake shafinka da kanka, ko kana aiko mutane da nufi suna matsawa, za su kore ka daga tsarin gaba daya.  Kuma ba za su kara karbarka ba har abada.  Sharadi na biyu kuma shi ne, sai adadin hakkinka sun kai Dala 100 ($100) sannan za a biyaka.  Don haka, ko wata biyar aka yi, kai ko shekara za a yi, muddin kudin basu kai Dala 100 ba, ba za a biyaka ba.  Sharuddan kenan.  Sai a kiyaye; kada ka matsa.  Kuma kada ka tura wasu su rika matsawa.  Sannan kada ka rika canza wayoyin salula ko kwamfuta don ka matsa.  Suna da hanyoyin ganewa da dama.  Ko ba wannan, a matsayinka na Musulmi dole ne ka kiyaye ka’idojin kasuwanci dake tsakaninka da abokan kasuwancinka, muddin bai saba wa shari’ah ba.  In kuwa ya saba wa shari’ah, to, rashin shiga ma tun farko shi yafi, misali nake bayarwa.  Wannan kenan.

Dangane da dayar tambayarka kan “Flashing” kuma, shi tsarin “flashing” na waya wani abu ne da aka dade ana yi, kuma yana da fa’ida amma bisa wasu sharudda.  Kafin mu kai ga yadda ake gudanar da wannan aiki dai zai dace mu fahimci me ake nufi da “Flashing” tukun?  Kalmar “Flashin” a fannin kimiyyar sadarwar wayar salula na nufin “Farke babbar manhajar wayar salula ne da cire mata dukkan kaidin da kamfanin wayar ya sanya mata, don baiwa mai amfani da wayar damar yin yadda yaga dama da ita, wajen kayatarwa da ingantawa.”

A asali, duk da cewa mai waya na iya aiwatar da abubuwa masu yawa a kan wayarsa, wajen sanya mata kyale-kyale da samar da hanyoyin inganta ta ko kayatar da ita yadda yake so, sai dai wannan dama da aka bashi dama ce nakasasshiya.  Akwai abubuwa da dama da bazai iya gudanar dasu ba.  Sai dai ba kowa yasan hakan ba.  Misali, a yayin za ka iya saukarwa tare da kara wasu manhajoji (Applications) daga cibiyar manhajojin wayarka (irin su Store, ko Play Store, ko Google Play Store) misali, kuma in kaga baka gamsu da manhajar ba ka sake cire ta, sai dai kuma a daya bangaren, manhajojin da wayar tazo dasu baza ka iya cire su ba.  Misali, baza ka iya cire manhajar adanawa da taskance sunaye da lambobin waya ba (Contacts), baza ka iya cire manhajar rubutawa da karbar sakonnin tes ba (Message), baza ka iya cire manhajar dake dauke da cibiyar manhajoji ba (irin su Google Playstore misali), da dai sauransu.  Abu daya kawai za ka iya yi, shi ne ka dakile su har su daina amfani, wato ka matsa: “Force Stop” idan nau’in Android ce.  Amma ko ka matsa alamar “Uninstall” don cire manhajar, sai dai kawai a cire bayanan da wayar ta saukar don kara wa manhajar karfin aiki, wato: “Update Data.”

Ba wannan kadai ba, baza ka iya ganin wasu bayanai da suka danganci bayanan manhajojin wayar ma ba, balle ka san dabarar da za ka yi don cirewa ko goge su.  Har wa yau akwai nau’ukan manhajoji da kamfanin wayar ya dora mata, wadanda suka kebance kamfaninsa don kara inganta wayar ko kara tallata hajojinsa, irin su manhajar: “Galaxy Apps” na kamfanin Samsung, da manhajar kalanda mai suna: “S Planner”, duk ba ka iya cire su.  Daman kamar yadda muka karanta a doguwar kasida ta musamman da muka gabatar a baya mai take: “Tsarin Babbar Manhajar Android,” mun fahimci cewa dukkan wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Android suna da manhajoji nau’i uku ne; da wadanda ke zuwa dauke a babbar manhajar, tun ran gini ran zane.  Su ne wadanda asalin manhajar Android tazo dasu a matsayinta na babbar manhaja.  Sai wadanda kamfanin waya ya kara dora wa wayar da ka saya, don bambance nau’in wayarsa daga sauran wayoyin da wasu kamfanoni suka kera.  Sai kuma nau’in manhajar da kai mai wayar ka dora mata; ko dai wadanda ka saukar daga cibiyar Play Store, ko wadanda ka dora mata kai tsaye daga katin SD (Memory Card).  To me yasa kamfanonin waya ke “kulle” wadannan hanyoyi?

Suna yin haka ne don wasu dalilai.  Na farko, don kariya ga wanda zai saya kuma yayi amfani da wayar.  Domin idan ya zama kowa na iya cire komai da wayar tazo dashi, to, wani na iya cire wata manhaja mai mahimmanci cikin kuskure ko ganganci, wacce idan babu ita a kan wayar, wayar baza ta tashi ba ko kadan.  Wannan kuma ba sabon abu bane.  Domin hatta kamfanonin kera kwamfutoci su ma suna yin haka.  Akwai nau’ukan bayanai da yawa wadanda kwamfuta tazo dasu, wadanda idan ba kwararre bane kai, ba za ka iya goge su ba.

Kai ba ma wannan ba, akwai wasu wurare (locations) a cikin kwamfuta inda idan kayi kuskuren ajiye bayananka a cikinsu, baza ka iya sarrafa su yadda kake so ba – ko dai ta hanyar canza musu suna ko kuma goge su.  Saboda suna cikin wani mahalli ne mai matukar mahimmanci.  Anyi hakan ne don kare masu amfani da kwamfutar daga kuskure ko gangancin da zai iya haifar da hadari mai girma ga rayuwar kwamfutar gaba daya.  Saboda ba kowa bane ya san kan na’urar.  Cikin kashi 100 na masu amfani da wayar salula, kashi 5 ne ko ma kasa da 5 suka san kan wayar hakikanin sani.  Sauran duk ‘yan abi-yarima-a-sha-kidi ne.

Dalili na biyu shi ne don baiwa hajar kamfanin wayar kariya daga satar fasaha.  Domin idan ya zama ko a bude yake, wani kamfani na iya “juye” dukkan tsarin da kamfanin wayar yayi, ya karance shi tsaf, sannan ya saci abin da zai sata ba matsala.  Duk da cewa wannan bai hana ayi hakan ba yanzu, amma a asali, wannan na cikin dalilan.  Wadannan su ne manyan dalilai dai a takaice.

- Adv -

Shi tsarin “farke” babbar manhajar waya (Flashing) wani ilimi ne mai zaman kanshi wanda a baya idan ka shiga halin bukatarsa, sai ka kashe kudi mai dimbin yawa.  Domin kwararrun masu gyaran waya ne ke aiwatar dashi, kuma sai da kwamfuta sannan.  Amma a halin yanzu abin ya sawwaka, saboda samuwar wasu manhajojin wayar salula (Mobile Phone Apps) dake sawwake hakan.  Ni kaina na sha amfani da wannan tsari wajen yin wasu gwaje-gwaje akan wayata.

A asali, akan “farke” babbar manhajar waya ne idan ta samu matsala; ta kasa gaba ta kasa baya.  Ko ta rikice ta kasa tashi.  Ko kuma ta rika kunna kanta tana kashewa (ta sha kwaya kenan).  Ko kuma ta kamu da kwayoyin cuta (Virus) da suka mata illa har a karshe ta haukace.  Bayan wadannan dalilai, wasu kan “farke” babbar manhajar waya don wasu manufofi na kashin kansu, musamman kwararru.  Misali, kwanakin baya na cire babbar manhajar da wayata tazo dashi (wato na asali – “Stock ROM”, ko “Firmware” kenan a turance), na dora mata na sama dashi (wato “Custom ROM”), don yin wani gwaji.  Dalili na uku kuma shi ne idan mai waya na son samun gamammen ‘yanci, don gogewa da saukar da duk irin manhajar da yake so.  Su dai a samu ‘yanci kawai.  Wannan ya fi shahara a tsakanin daliban jami’a masu karatun kimiyyar sadarwa da kwamfuta.

Kamar yadda ka bukata, tabbas kana iya “farke” babbar manhajar wayar salula ba tare da ka yi amfani da kwamfuta ba.  Duk da yake hakan ya danganci nau’in wayar da kake son yin hakan a kanta.  Amma kafin nan, shi tsarin “Flashing” ya kasu kashi hudu ne.  Na farko shi ne wanda za a iya mayar da wayar ta koma kamar yadda kamfanin waya ya samar da ita.  Wannan shi ake kira “Factory Default Resetting.”  Shi wannan tsarin ko a kan wayarka kana iya yi, ba sai ka saukar da wata manhaja ba.  Sai dai duk abin da ke kan wayar na bayanai da tsare-tsaren mai waya (User Settings) za su goge, sai ka sake tsara su.  Sai dai yana da nakasu, domin bazai iya baka damar yin wasu abubuwa sama da yadda irin damar da kamfanin waya ya baka ba; an sumar da ita ne kawai aka sake busa mata ruhinta na asali.

Nau’i na biyu shi ake kira: “Rooting”, wanda ke baka damar iya gogewa da dora duk irin manhajar da kake so, muddin ya dace da mahallin wayarka.  A baya wannan tsari bai yiwuwa sai da kwamfuta.  Amma a yanzu shi yafi komai sauki, wai cire wando ta ka.  Amfanin wannan tsari shi ne za ka samu karin ‘yanci, amma bazai goge maka bayanan dake kan wayarka ba.  Sai dai kuma, “garanti” (Warranty) da wayarka ke dashi in dai sabuwa ce, ya baci kenan.  Ko ka mayar shagon da ka saya sanadiyyar wata matsala, baza su karba ba; sai in basu san kan waya ba.  Idan kuwa suka karba suka mayar wa kamfanin ko dillalin da ya sayar musu a farko, zai gane, kuma bazai canza musu ba.  Matsala ta biyu da wannan tsari ke tattare dashi kuma shi ne, daga ranar da ka “farke” babbar manhajar wayar salularka ta hanyar “Rooting,” ka daina samun bayanan karin tagomashi kenan daga kamfanin wayarka, wato: “Updates.”  Domin da zarar ka yi kokarin jonuwa dasu don saukar da bayanan, zasu ce maka: “Ga alama an canza tsarin babbar manhajar wannan waya.  Hakan yasa baza ka iya saukar da bayanan da kake so ba.

Don haka, kayi amfani da manhajar “Kies” don saukar da bayanan da kake nema.”  A harshen turanci za a fadakar da kai wannan bayani.  Manhajar “Kies,” ga masu amfani da wayar salula na kamfanin Samsung, ita ce manhajar da ake amfani da ita wajen loda wa wayoyin salular Samsung bayanai ko adana bayanan, don taskance su don nemansu nan gaba – wato “Backup.”  Idan ka jona wayarka don kokarin cika wancan umarni, nan take za a ce ka sake saukar babbar manhajar wayarka, don “wannan an gurbata ta.”  Wannan shi ne babban kalubalen aiwatar da “Rooting” a wayar salula.  To yaya za ka yi? Idan kwararre ne kai, sai ka nemo bayanan da kake so a Intanet, ka zuba su cikin katin Memory dake wayarka, kayi amfani da manhajar “Recovery” da zamuyi bayani nan gaba kadan, don loda mata kai tsaye.

Nau’i na uku shi ne amfani da kananan manhajojin farfado da waya, wato “Recovery Mode Applications,” don “farke” babbar manhajar wayar salula.  Masu amfani da wannan tsari galibi kwararru ne, kuma za ka samu ma suna yin hakan ne don samun damar kara wa wayar bayanan tagomashi (Updates), ko ma cire babbar manhajar wayar don dora mata babbar manhaja sabuwa.  Ana aiwatar da wannan tsari ne dai ta amfani da manhajar wayar salula, wadda ke nemo manhajar da ta dace da wayarka ta karasa aikin.  Shahararriyar manhajar wayar salula da ake amfani da ita don haka ita ce: “ROM Manager,” wacce za ka iya saukarwa kyauta daga cibiyar Play Store, idan kana amfani da Android ne.  Sai dai yana da kyau mai karatu yasan cewa ba dukkan babbar manhajar Android ke iya samun wannan tsari ba.  Wasu wayoyin ko ka saukar da manhajar ROM Manager, baza ka iya “farke” babbar manhajar wayarka da ita ba idan ta kasa nemo tsarin da ya dace da wayarka.

Tsari na karshe shi ne wanda ake aiwatarwa ta amfani da manhajojin “farke” babbar manhajar wayar salula na kwamfuta.  Wannan tsari yana da alaka da tsari na uku dake sama, sai dai ka fi samun ‘yanci ta amfani da wannan hanya.  “Farke” babbar manhajar wayar salula ta wannan tsari na bukatar a tanadi abubuwa da dama.  Dole kayi amfani da wayar musayar bayanai na asali (Original USB Cable), ka kuma saukar da “Driver” din wayar USB da ya danganci wayarka, sannan ka tanadi manhajoji irin su “Odin 3,” da “ClockWorkMod Recovery” (CWM Recovery) ko “TeamWinRecovery” (TWR Recovery).  Sannan, idan ta kure sosai, sai ka nemo babbar madaukin Android, wato: “Android ADB” dake dauke cikin “Android Studio.”  Wadannan karikitai su za kayi amfani dasu wajen sumar da wayar, da jefa ta cikin yanayin da zai baka damar “farke” babbar manhajarta.  Wani abin sha’awa ma shi ne, dukkan wadannan manhajoji da tsare-tsare, kyauta za ka same su a Intanet.

A karshe, “farke” babbar manhajar wayar salula ta hanyar amfani da manhajar waya abu ne mai sauki.  Abu na farko, ka saukar da manhajar da za ta baka damar yin hakan.  Abu na biyu, idan wayarka lafiya lau take, sai ka adana bayananka a kan katin memory ko kayi amfani da kwamfuta.  Wannan zai baka damar komawa gare su idan ka samu matsala.  Saboda ba tsari bane mai cike da garanti, kamar yadda ka san rayuwar yau take.  Daga nan sai ka bude manhajar, don aiwatar da abin da kake son aiwatarwa.  Misali, idan “Rooting” kake son yi, sai kayi.  Idan kuma kana son dora mata hanyar ceto waya ne, wato: “Recovery Mode,” sai kayi.  Kamar yadda na fada a baya, akwai nau’ukan tsare-tsare guda biyu shahararru: “CMW Recovery,” da kuma “TWR Recovery.”

Kowanne daga cikinsu kana iya “farke” babbar manhajar wayar dashi, kai tsaye.  Kuma zai baka damar aiwatar da abubuwa daban-daban a kan wayar, babu tarnaki.  Idan ka “farke” babbar manhajar wayarka ta amfani da dayan hanyoyin nan biyu (su ake kira: “Custom ROM Recovery”), a kowane lokaci kana iya jefa wayarka cikin yanayin, don aiwatar da wani abu.  Hanyar yin hakan kuwa ba wahala; ka kashe wayarka, bayan ta mutu, sai ka kunna ta ta hanyar danna maballin kunnawa (Power Key) da maballin farkar da waya, wato: “Home Key” da kuma maballin rage sautin waya, wato: “Volume Down Key,” a lokaci guda, ka rike, har sai ka ga tambarin sunan kamfanin wayar ya fara bayyana, sai ka saki.  Nan take za ta shiga yanayin da ake kira: “Recovery Mode.”

Har wa yau ka sani, kowace wayar salula na da yanayi biyu ne.  Akwai yanayi madaidaici, wannan shi ake kira: “Standard Mode.”  Shi ne yanayin da wayarka ke kasancewa a ciki a duk sadda ka kunna ta, ta hanyar danna maballin kunnawa, wato: “Power Key.”  Sai yanayi na biyu, wanda ake kira: “Recovery Mode,” ko “Donwload Mode”, ko kuma, a wasu lokuta, ake kira: “Fastboot.”  Wannan shi ne yanayin dake baka damar sumar da ita don aiwatar da wasu abubuwa na musamman.  Ba yanayi bane da ake iya amfani da ita wajen kira ko wata mu’amala na sadarwa ta al’ada.  Ta wannan yanayi za ka iya “farke” babbar manhajar wayar salula kai tsaye.  Ita wannan hanya ta “Recovery Mode” na da tsari biyu ne.  Na farko shi ne wanda kamfanin waya ya samar.  Wannan shi ake kira: “Stock Recovery Mode.”  Za ka iya aiwatarwa ba tare da wata manhaja ba.  Kawai ka kashe wayarka, sai kabi wancan mataki da na fada a sama don shigar da ita wannan yanayi tare da aiwatar da abin da kake bukata.

Ita wannan hanya tana baka damar “flashing” ne kadai, wanda zai goge bayananka da tsare-tsaren da kayi wa wayar gaba daya, ta dawo kamar yanzu aka kera ta.  Amma bayan shi, baza ka iya goge duk abin da kamfanin ya hana ka gogewa ba.  Sai hanya ta biyu, wacce za kayi amfani da wadancan manhajoji da nayi bayani a sama, don “farke” babbar manhajar wayar tare da samun damar jefa ta cikin yanayin ceto.  Wannan shi ake kira: “Custom Recovery Mode.”  Wannan hanya ce kadai ke baka damar sarrafa wayar yadda kake so, da dora mata duk abin da kake so, don kawatawa ko kayatar da ita yadda kake so.

Bazan iya ce maka ga manhajar da ta dace da wayarka ba kai tsaye, tunda ban san wayar ba.  Amma idan kana bukatar amfani da hanyar farko ne, to, ba ka bukatar amfani da wata manhaja ta musamman.  Sai dai kabi bayanin da nayi a sakin layin da ya gabaci wannan saki layi.  Idan kuma kana bukatar ‘yanci ne, sai kayi amfani da manhajojin wayar salula dake “Play Store.”  Ka rubuta: “Custom Recovery” kawai, za a antayo maka su kala-kala.  Sai kabi su daya-bayan-daya don zaban wanda ya dace da wayarka.  Kada ka mance dai, yin amfani da wannan hanya zai karya garantin wayarka, tare da hana ka samun bayanan tagomashi daga kamfanin wayarka, wato “Updates.”  Sannan ka adana kwafin bayanan wayarka duka kafin ka fara; domin idan ka kuskure, to, wayar ma na iya kasa tashi baki daya.

Wannan shi ne dan abin da zan cewa kan wannan tsari a halin yanzu.  Na kuma san bayanan da nayi sunyi tsawo matuka.  Na yi haka ne saboda akwai wadanda suka mini tambayoyi kan wannan tsari dake jiran amsa.  Don haka na tsawaita bayani don samun gamewa.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.