Sakonnin Masu Karatu (2016) (16)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

146

Assalamu alaikum.  Dafatan kana lafiya; yaya Sadik, kuma yaya aiki? Na gode sosai, da kasidar (Bermuda Triangle) din, da ka turo mini. Allah ya saka maka da Aljannar firdaus, ya kuma kara maka basira.  Bayan haka Don Allah ina so ka turo mini wasu kasidu kamar haka: Binciken malaman kimiya akan yadda barci ke samuwa da mafarki, Tsarin gadon dabi’u da siffofin halitta a kimiyance, Tsakanin kimiyar al-Kur’ani da ta zamani ina aka hadu? da kuma kasidar jirgin ruwa mai suna (Titanic). Ta akwatin Imail di na: Mjunaidu92@gmail.com.  Sannan kuma idan akwai kasidu a kan na’ura mai kwakwalwa (Computer) da abin da ya shafeta don Allah ka turo mini saboda suna da amfani a gareni sosai.  A taimaka mini don Allah.    A aiko mini ta wannan Imel din. Mhmmdshmsdn8@gmail.com, da na turo maka sakon dashi na manta password din shi. saboda haka na bude wannan sabon. Dan Allah dan Allah malam ka taimaka. Na gode. – Junaidu Musa

Wa alaikumus salam, Malam Junaid ina godiya da addu’o’i, Allah saka da alheri.  Ina fata ana karuwa da dan abin da nake aikowa.  Babban burina a rayuwa shi ne ya zama abin da nake yi yana amfanar jama’a.  A halin yanzu na tattara wadannan kasidu da ka bukata kuma na aika maka ta adireshin karshe da ka aiko.  Tabbas na ga sakonka na karshe, inda kake nuna ka mance kalmar sirrin akwatin Imel din farko da ka aiko mini.  Sai ka duba na biyun.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, ina karatun amsoshin tambayarka ga jaridar AMINIYA. Don Allah ina son in canza sunan da nake amfani dashi wajen hawa shafin Facebook (Facebook Username) di na daga Imel zuwa lambar waya, amma na kasa.  Don Imel din ya daina aiki amma ina amfani dashi har yanzu wajen hawa shafin Facebook. Ina iya yin hakan?  Nagode.  Daga Shafi’i Kilgori, Jihar Sokoto:  shafiialiyu203@yahoo.com

Wa alaikumus salam, Malam Shafi’i.  Idan na fahimci tambayarka, kana son sanin ko zai yiwu mai shafi a Facebook ya iya canza sunan da yake hawa shafinsa dashi ne, wato: “Username.”  Eh, wannan abu ne mai yiwuwa.  Daman, ko dai ya zama adireshin Imel ne kake amfani dashi wajen hawa, ko kuma lambar waya.  Hanyar hawa facebook ta uku ita ce ta amfani da lakabin mai shafi, wato: “Facebook ID,” wanda ba kowa bane ya san wannan.  Lakabin mai shafi dai hadakar suna ne ko sunaye ko kuma wasu lambobi da adadinsu yakai 15, wadanda manhajar Dandalin Facebook ne ke baiwa kowane mai shafi bayan yayi rajista.  A takaice dai wadannan su ne hanyoyin kuma kana iya canzawa iya gwargwadon yadda kaso.

Idan kana amfani da wayar salula ne, da zarar ka hau shafinka, ka gangara can kasa daga gefen hagu ka matsa: “Settings” idan ta “browser” kake hawa, ko kuma bangaren dama daga sama, idan kana amfani da manhajar Facebook ne (Facebook App).  Da zarar ka shiga bangaren “Settings”, sai ka shiga “General Account Settings.”  Ka isa wurin za ka ga jerin bayanai kamar haka: “Name”, “Username”, “Contact” da dai sauransu.  Tsakanin wadannan ne za ka iya gudanar da abin da kake so.  Ka je bangaren “Contact”, za ka lambar wayar da kake hawa shafinka da ita.  Sai ka matsa, shafi zai budo.  A nan za ka inda aka rubuta: “Add another email or mobile number.”  Kana matsa wannan alama za a budo maka inda za ka shigar da adireshinka na Imel.  Da zarar ka shigar sai ka matsa alamar “Save Changes” dake can kasa, za a bukaci ka shigar da kalmar sirrinka (Password) don tabbatar da cewa lallai kaine mai shafin.  Da zarar ka sa, za a turo maka wasu lambobi guda 4 ko 6 zuwa akwatin Imel dinka, tare da budo wani wuri da ake son ka shigar da zarar ka dauko lambobin.  Sai kaje can ka dauko su, ka shigar a inda aka tanada.  Kana shigarwa shikenan!  An gama (sunan tsohuwa a wani yare).

A duk sadda ka tashi hawa shafinka sai ka rubuta adireshinka na Imel maimakon lambar wayarka.  Sai dai kuma wani fadakarwa.  Yana da kyau ka san cewa, don ka kara adireshin Imel, wannan na nufin baza ka iya kara hawa da lambar ba kenan.  A a.  ka kara hanyoyin hawa shafinka ne kawai.   Fa’idar hakan shi ne, a duk sadda ka samu matsala da shafinka har aka kulle aka hanaka hawa, za ka iya bukatar a turo maka lambobi ta Imel dinka, musamman idan ka daina amfani da lambar wayar da ka sa a farko, don tantanceka tare da bude maka hanya.

Idan har ba ka son ka ci gaba da amfani da lambar a shafin, da zarar k agama dora adireshin Imel din, sai ka koma bangaren “Profile” a shafinka, ka gangara bangaren “Contacts,” sai ka matsa inda aka rubuta: “Edit Contact,” za a budo maka lambar wayar.  A kasa za ka ga inda aka rubuta: “Remove Number” ko wani abu makamancin hakan.  Da zarar an cire lambar wayar shikenan.  Allah sa a dace, amin.


Baban Sadik da fatan ka yi sallah lafia.  Ina neman alfarmar da ka turo mini kasidar da ka rubuta kan fannin “Genetics”, da ta Samuwar Mafarki a Kimiyya.  Daga mai kaunarka Sulaiman Yunusa Gumel: suleimanyunusa7@gmail.com

- Adv -

Malam Sulaiman barka dai.  Ina matukar godiya da kaunarka.  Allah tara mu cikin rahamarsa baki daya, amin.  Ka duba akwatin Imel dinka, na aika maka wadannan kasidu da ka bukata.  Allah amfanar damu baki daya, amin.


Assalamu Alaikum Baban Sadik, ya kamata ka ja hankalin matasa akan yadda ta kamata mu gudanar da rayuwarmu a kafafen sadarwa na zamani.  Nasiru Kainuwa Hadejia.  08100229688: naseeryaaky@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Nasiru barka dai.  Lallai wannan shawara ce mai kyau matuka.  Alal hakika ga dukkan masu bibiyar shafukan da nake rubuce-rubuce ko wannan shafi na jaridar AMINIYA, hada har da kasidu da makaloli da na gabatar da laccoci da aka gayyace ni a wurare daban-daban cikin kasar nan, zai ga lallai babu maudu’in da nafi bayar da mahimmanci a kansa irin wannan bangare.  Bayan haka, lokaci zuwa lokaci nakan tabo wannan maudu’i, ko dai yayin amsa tambayoyi masu alaka dashi ko ta hanyar shafina na Facebook ga masu bibiyata a can.  Don haka, zan ci gaba da gabatar da fadakarwa a duk sadda dama ta samu.  Ina godiya da wannan shawara.  Allah saka da alheri, amin.


Salaamun alaikum, da fatan kana lafiya Baban Sadik.  Don Allah ina so ka yi mini cikakken bayani game da kalmar “Paypal,” kuma shin, sai lale ina da taskar ajiyar banki (Bank Account) ne kafin inyi amfani dashi ko a’a?   Daga masoyinka a yau da kullum:  Amiru usman: danbaiwa95@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Amiru.  Ina godiya matuka da kaunarka gare ni.  Ina rokon Allah yasa muyi tarayya cikin alheri baki daya, amin.  Dangane da tambayarka, shafin PayPal dai shafi ne dake baiwa mutane daman aiwatar da cinikayya ta hanyar biyan kudaden hajojin da suka saya a shafukan Intanet cikin sauki, tare da basu dama har wa yau wajen aika wa ‘yan uwansu kudade kai tsaye, watau “Instant Money Transfer” kenan.  Idan kana da rajista da wannan shafi har wa yau, za ka iya karban kudaden cinikin da kayi na hajojin da kake tallatawa idan kana da shafin sayar da kayayyaki a Intanet.  A takaice dai, kamfanin PayPal dai dillalai ne kan hada-hadar kudi a duniya ta hanyar Intanet.  Bai wai banki bane ai zaman kansa.

Asalin wannan shafi dai ne ya faro ne daga babban shafin sayar da hajoji a Intanet mai suna: “Ebay,” daga nan ya fara hada-hadar kudi ta hanyar baiwa jama’a masu sayan hajoji a shafin “Ebay” damar biyan kudin hajoji, da kuma baiwa ‘yan kasuwa damar karbar kudaden da ake biyansu na hajojin da suke sayarwa a shafukansu na Intanet.  Daga nan wannan shafi ya habbaka.  A halin yanzu dai akwai masu rajista sama da miliyan 188 a duniya.  Kuma shafin na samun kudaden shiga ne ta hanyar cajin hidima da yake wa masu rajista dashi.  A karon farko dai kamfanin yakan tara kudaden da yake karba a madadin masu rasjita dashi ne a bankuna, yana karbar kudin ruwa kai tsaye daga bankunan, tunda suna aiwatar da kasuwanci da kudaden, kamar yadda yake a tsarin hada-hadar kudade na zamani a kasashen Amurka da Turai.  Daga baya da masu rajista da wannan shafi suka gano haka, sai suka ta rufe “account” dinsu suna ficewa.  Domin wannan, a tunaninsu, ci da ceto ne.

Wannan bore da jama’a suka yi ne yasa ya canza tsarinsa.  Inda ya rika dora wa masu rajista haraji kan dukkan hidimar da ya musu.  Harajin masu sayar da hajoji daban da na masu karba ko aika kudade ga ‘yan uwa ko abokansu.  A halin yanzu da wannan tsari dai kamfanin ke rayuwa.  Idan ka kebe kasashen Indiya, da Ghana, da Japan, da Afghanistan, da Crimea, da sauran kasashen da kasar Amurka ta sanya wa takunkumi, duk sauran kasashen duniya na mu’amala da wannan shafi.  A halin yanzu an kiyasta cewa, shafin PayPal na iya karba tare da aika takardun kudade sama da 25 daga cikin nau’ukan kudaden duniya.

Yin rajista a shafin PayPal ba wahala.  Bayanan da za ka bayar sun hada da sunanka cikakke, da adireshin Imel, da adireshin inda kake zaune, da kasar da kake zaune, da lambar wayarka, sannan da lambobin katin ATM dinka.  Dangane da tambayarka cewa ko dole ne sai kana da taskar ajiyar banki sannan za ka iya yin rajista?  Amsar ita ce: eh!  Domin za a bukaci lambobin katinka na ATM, wanda ta hanyar lambobin ne za a iya zuba maka kudade a taskarka ta banki da ke kasar da kake.  Wannan shi ne takaitaccen bayani kan shafin PayPal.  Idan kana bukata kana iya ziyartar shafin a: www.paypal.com.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.