Sakonnin Masu Karatu (2016) (3)

Ci gaban sakonninku kamar yadda aka saba. A sha karatu lafiya.

91

Assalamu alaikum, don Allah, mai sunana, bayanin Tekun Atlantika zurfinsa da ake cewa ya kai  zurfin Mita dubu uku, a sanar dani kamar tsayin kilomita nawa kenan a tsaye?

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Lallai kamar yadda da karanta a baya, cewa zurfin Tekun Atlantika ya kai mita 3,926, kusan mita 4,000 dai kenan a takaice.   Idan aka kwatanta da nisa a kasa ko a tsaye kamar yadda ka bukata, daidai yake da kilomita 3.926, ko kuma kilomita 4 dai kenan.  Domin a ka’idar lissafi a fannin kimiyya, mita 1,000 shi ne kilomita 1.  Kenan, mita 3,926 zai zama daidai da kilomita 3.926 kenan.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban sadik, barka da warhaka. Da fatan kana lafia tare da dukkan iyalanka baki daya. Don Allah Baban Sadik, ina son ka taimaka mini da  bayani kan yadda ake dora hotuna a shafin Twitter? Kuma me ake nufi da kalmar  “Favourite”  a shafin Twitter? Na gode. Daga Dauda Shuaibu Luti, jihar Bauchi. 08036907090. 08056907090.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Dauda.  Da fatan kana cikin koshin lafiya.  Dora hoto daskararre (Still image/picture) ko mai motsi (Video) ba wani abu bane mai wahala a shafin Twitter.  Idan ka shiga shafinka, sai kaje inda ake rubuta sako, wato inda aka rubuta: “What is happening?”  Da zarar ka gama rubuta sakonka, sai ka matsa alama ko tambarin dake kasan inda ka rubuta bayanan, na farko daga hagu kenan, mai take: “Media”  nan take za a budo maka ma’adanar waya ko kwamfutarka mai dauke da inda aka ajiye hotuna ko bidiyo, sai ka zabi hoto ko bidiyon da kake son makalawa ko dorawa.  Shikenan ka  gama.  Ga misalin nan cikin hoton dake wannan shafi na kawo maka, wanda na dauko daga shafina dake Twitter.  Hatta a waya na tabbata haka tsarin yake.  Ba abu bane mai wahala.

Dagane da ma’anar kalmar “Favourite” kuma, wannan kalma ba wai a Twitter kadai ba, a duk inda ka ganta a na’ura ko hanyar sadarwa ta zamani, tana nufin “shafi ko abin da kake so” ne a ranka, na gani ko na karantawa.  A kan manhajar lilo kuma (Browser) tana iya nufin jakar bayanin dake dauke da shafukan da ka taskance wadanda kake son karantawa a wasu lokuta na gaba.  Da fatan ka gamsu.


Salaamun alaikum Abban Sadik.   Hoton jirgin Titanic, shin, ainihin wanda yayi hatsarin ne na fim ne? Daga Adamu Zaria

- Adv -

Wa alaikums salam Malam Adamu.  Ban san wanne ne ka gani ba daga cikin hotunan.  Domin kasidar ta kai kashi wajen 4, kuma kowanne daga cikinsu akwai hoton dake da alaka da bayanin da ake yi.  Amma duk da haka, hotunan da na lika shafin sadda nake rubutun sun kasu kashi biyu ne.  Akwai wadanda hotunan fim din ne, masu dauke da Jaruman fim din.   Sannan akwai hotunan da suka shafi lamarin gaba dayansa.  Su wadannan hotuna an zano su ne daga hotunan wancan jirgi a sadda lamarin ke faruwa.  Shi yasa za ka ga launinsu baki da fari ne, babu kala.  Wanda hakan ke nuna dadewa ne.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, ina son a mana bayanin wai shin, akwai kasashen da ba su amfani da fasahar Intanet ne a duniya?  Na gode: Hassan Isah Tk, Katsina

Wa alaikumus salam, Malam Hassan barka ka dai.  Dangane da kasashen da ba su amfani da fasahar Intanet a duniya, ina iya cewa babu wata kasa a duniya da fasahar Intanet bata kutsa ba.  Illa dai ya danganci karancin masu amfani da fasahar ne; ko dai sanadiyyar talauci ko dokokin kasa da hukumomin gwamnatocin kasashen ke kagaba wa fasahar, don karya kadarin tasirinta ga al’ummarsu saboda wasu dalilai na siyasa ko al’ada ko addini.

A halin yanzu an kiyasta ana da mutane sama da biliyan bakwai masu rayuwa a wannan duniya.  Cikin wannan adadi, kashi 40 ne kadai ke ta’ammali da fasahar Intanet.  Sauran kashi 60 din suna cikin duhu har yanzu.  Daga cikin wannan adadi na kashi 40 na masu amfani da fasahar Intanet, idan aka kasa su kashi 100 kuma, kashi 78 na kasashe masu duniya ne – tsakanin Amurka da Turai da wani bangaren Asiya – sauran kashi 32 kuma na kasashe talakawa.

Duk da haka, babu wata kasa da ba’a ta’ammali da wannan fasaha kamar yadda na sanar a sama, sai dai karancin masu amfani da ita.  Don haka sai dai a ce kasashe masu karancin masu ta’ammali da fasahar Intanet.  Masu dalilan talauci da karancin ci gaban fasahar sadarwa da tattalin arzikin kasa, galibi suna kasashen Afirka ne, musamman ta yamma.  A kasar Guinea misali, kashi 1.6 ne kadai na jama’ar kasar ke ta’ammali da fasahar Intanet.

Bayan ita akwai kasashen Saliyo (Sierra leone), da kasar Afirka ta Tsakiya (Central African Republic) da kuma kasar Liberia.  A wadannan kasahe duk, masu ta’ammali da fasahar Intanet basu kai mutum dubu dari biyu ba.  Wadannan kasashe dai ana ganin babban dalilin samuwar karancin masu ta’ammali da fasahar bai wuce talauci.  Amma a kasashe irin su Kuba (Cuba) da Myammar (Bama), bayan talauci, akwai dalilan siyasa da al’adu.  Daga cikin kasashe 207 da ake da alkaluman masu amfani da Intanet a cikinsu, Najeriya ce ta 9 a yawan masu ta’ammali da Intanet a duniya, domin tana da mutane sama da miliyan sittin da rabi, kashi 38 kenan na yawan ‘yan kasar wadanda suke ta’ammali da fasahar Intanet.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.