Sakonnin Masu Karatu (2016) (4)

Ci gaban sakonninku kamar yadda aka saba. A sha karatu lafiya.

63

Assalamu Alaikum barka da marece, dafatan kana lafiya.  Malam don Allah ya ake saukar da manhajar “Drivers,” sannan don Allah ko akwai gidan yanar sadarwa da ake saukar da manhajar wasan kwamfuta da manhajojin amfani na musamman masu kyau, kuma na kuata?  Sannan a karshe kuma, inaso in koyi dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming), wace hanya zan bi?   Ko akwai wani gidan yanar sadarwa da kake fahimtar da jama’a a wannan bangaren?  Nagode.  Daga ni almajirinka: Khalid Katsina

Wa alaikumus salam, Malam Khalid barka da warhaka.  Da fatan kana cikin koshin lafiya.  Tambayar farko kan inda ake saukar da kananan manhajojin kwamfuta masu suna Drivers, wadanda ke taimaka wa kwamfuta hada alaka tsakaninta da wasu na’urorin sadarwa ko wasu manhajoji, sai in ce ya danganci abin da kake nema.  Idan kwamfuta ce kake son nemo mata drivers dinta na musamman, hanya mafi sauki ita ce kaje shafin kamfanin da ya kera kwamfutar, kai tsaye, sai ka nemo.  Za ka samu kyauta ba da sisin kwabonka ba.   Idan HP ce, ko Dell, ko Toshiba, ko Acer, duk shafukansu za ka je.  Haka idan ma na’urar dab’i ce, wato: Printer, shafin kamfanin da ya kera na’urar za ka je.

Dangane da inda za ka iya saukar da manhajar wasan kwamfuta kyauta kuma, a gaskiya babu aminci ga kwamfutarka, yin hakan nake nufi.  Domin duk galibin manhajojin Games na kyauta da za ka kwasa a wani shafi da ba na kamfanin da ya kera manhajar ba, kana iya kwaso kwayoyin cuta ga kwamfutarka.  Don haka, idan kana son zaman lafiya ka shiga shafin Google ka nemi bayani kan nau’ukan manhajar Games na kyauta, irin wadanda suka dace da dandanonka, a nan za ka ga sunayensu da gidajen yanar sadarwar kamfanin da ya gina su, sai kaje shafinsa kai tsaye ka saukar.  Wannan zai fi samar da salama.  Su ma manhajojin kyauta na kwamfuta haka suke; ka tantance abin da kake bukata, ka san shafin kamfanin da ya gina manhajar, sannan kaje ka saukar a can.

Idan kuma manhaja ce ta kudi, ka tara kudinka ka siya daga shafin mai manhajar ya fi samar da kwanciyar hankali.  Domin na farko, ka samu manhaja ta hanyar halal.  Na biyu ka kawar da kanka da kwamfutarka daga fadawa cikin matsala.  Na uku, a duk sadda kake neman taimako wajen warware wata matsala da ta shafi manhajar, inda ka sayo za ka koma don a gamsar da kai.

Bangaren tambayarka ta karshe, cewa ko akwai wani shafi da na killace don koya wa mutane dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming)?  Amsar ita ce: a a.  A halin yanzu dai ban tanadi wani shafi don wannan aiki ba.  Sai dai nan gaba.  Amma a tare da haka, akwai shafukan koyon dabarun gina manhajar kwamfuta kyuata, kuma birjik, a intanet.  Sai dai, don samun tsari, dole ne ka tantance, tare da killace bangare ko fannin ko babbar manufar da kake son cin mawa, kan haka.  Wannan zai taimaka maka wajen sanin wace hanya ce kuma wace fasaha ce tafi dacewa da kai.  Amma yin talalabiya kawai don zama cikin “Programmers,” ba inda zai kai ka sai babban birnin rudu.

- Adv -

Idan kana son koyon fasahar gina manhajojin da suka shafi babbar manhajar kwamfuta ne, wato: Operating System kenan, kana iya koyon fasahar C, wato: “C Programming Language,” daga nan ka hada da kanwarta, wato: “C++ Programming Language.”  Idan kana son koyon fasaha da dabarun gina shafukan gidan yanar sadarwa ne, wato: “Web Programming Language,” kana iya zuwa shafin W3SCHOOLS.COM, inda ake karantar da mutane dukkan wadannan dabaru kyauta – irin su HTML, da XHTML, da XML, da PHP, da JavaScript, da CSS – babu ko sisin kwabonka.  Illa dai dole ne ya zama kana da data a kwamfutarka, domin darussan suna kan shafin ne.  Duk da cewa kana iya saukar da jerin darasin da ya shafi wani fanni na musamman a dunkule.  A takaice dai sai kana da Intanet a kwamfutarka.  Adireshin shafin shi ne: http://www.w3schools.com.

A karshe, idan kana son koyon fasahar da za ka iya yin dukkan wadannan ayyuka ne a wuri daya, kana iya zuwa shafin Python, wanda fasaha ce mai karfi, mai saukin koyo, kuma mai dauke da dabaru masu dimbin yawa wajen gina manhajar kwamfuta.  Fasahar Python iyaka ce.  Kana iya koyon fasahar a shafinsu dake: www.python.org, sai ka je bangaren DOCS dake tsakiya daga sama a shafin farko.  Kana iya isa shafin kai tsaye daga nan: https://docs.python.org/3  za ka ji ka tsundum a ciki.

Shawarata, ka sani, ya kai dan uwa, koyon wannan nau’i na ilimi abu ne dake bukatar sadaukar da kai, da karfin hakuri da juriya wajen karatu, da hakuri – ba a kwarewa cikin kwanaki ko makonni ko watanni, sai an kwashe shekaru ana yi.  Abin da zai dada taimaka maka shi ne yawan karatu da yawan kwatanta abin da ake koyo.  Kada ka ji tsoron kuskure.  Ba za ka taba kwarewa a wani fanni na ilimi ba sai ka ta tafka kura-kurai a sadda kake dan koyo.  Amma idan so kake cikin ‘yan kwanaki ka zama kwararre, a naka tunani, to, kada ma ka fara.  Ina maka fatan alheri, Allah baka nasara.


Salaamun Alaikum Baban Sadik, don Allah a taimaka mini da kasidar tsibirin bamuda ta wannan adreshin: napeeubala01@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Nafi’u.  tuni na aika maka da wannan kasida.  Sai ka duba akwatin Imel dinka.  Allah sa rai da al’umma su amfana dashi, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.