Sakonnin Masu Karatu (2016) (6)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

99

Assalamu Alaikum Baban Sadik, don Allah ina son in san yadda zan gane boyayyar lamba, wato masu boye lamba don su yaudari mutum, da kuma yadda ake rufe shafin Facebook din wanda ya mutu.  Na gode.   Daga Muhammadu Sani Galadima

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Muhammadu Sani.  Da fatan kana lafiya.  Dangane da yadda ake gane boyayyar lambar waya da aka kira ka da ita, akwai manhaja ta musamman wacce ake amfani da ita don yin haka.  Duk da cewa akwai su da yawa, amma wacce tafi shahara ita ce manhajar “TrueCaller.”  Ana samunta kyauta a cibiyoyin manhajoji dake Play Store, idan nau’in Android ce, ko a cibiyar App Store, idan wayar nau’in iPhone ce.  Wannan manhaja dai babban aikinta shi ne hankado suna da adireshin wanda ke kiranka da wata lambar waya wacce ba ka da ita a rajistar lambobin wayarka.

Bayan bakin lambobi, wannan manhaja tana da wata kanwa wacce ke taimakawa wajen gano suna da adireshin wanda ya turo maka sakon tes ta amfani da bakuwar lamba.  Idan kana da lambar a wayarka, ba sunan da zai bayyana sai wanda ka saka.  Idan mai kiranka bai boye lambarsa daga wayarsa ba, nan take, muddin akwai yanayin Intanet mai karfi a wayar, za a nuna maka sunansa da gari ko kasar da yake.  Wannan shi ne abin da yafi shahara wajen kudurar wannan manhaja ta TrueCaller.  Amma idan mai kiran ya boye lambarsa fa, wato: “Unknwon Number” ko “Private Number” misali, shin manhajar TrueCaller tana iya hankado maka lambarsa?  A nan ne gizo ke sakan.

- Adv -

A galibin lokuta manhajoji irin wadannan suna iya toshe mai kiran ne kawai, amma ba su iya nuna maka sunansa da inda yake.  Akwai dalilai kamar guda biyu dake haddasa wannan nakasa.  Na farko dai wannan manhaja kyauta ce, Hausawa kuma kan ce “Araha ba ta ado.”  Tabbas yana daga cikin kudurar wannan manhaja ta iya hankado maka lambar wanda ya boye lambarsa, amma tunda kyauta ka same ta, wannan aiki ba ya cikin wadanda take iya yi ga wadanda suka saukar da ita kyauta.  Kai, mu kaddara ma ka saya, dalili na biyu yak au tukun.  Dalili na biyu shi ne, ganowa ko hankado lambar wanda ya boye lambarsa daga wayarsa na bukatar wannan manhaja ta TrueCaller ta hada kai da kamfanonin wayar kasarku, don su bata dama ta rika shiga taskar lambobi da sunayen masu lambobinsu, wadanda ke da rajista, don nuna wa mai manhajar.

Mu fahimci wani abu, sunayen da manhajar TrueCaller ke hankadowa idan aka kira ka da bakuwar lamba wacce ba a boye ta ba kafin kira, sunaye ne na hakika.  Kuma daga taskar kamfanonin waya take samunsu.  Wannan su suka ba da dama, babu wata matsala.  Amma idan ka boye lambarka daga wayarka, wannan bai tsaya ga wayarka kadai ba.  Da zarar ka fara kiran wani da layinka, nan take kamfanin wayarka zai gane cewa ka boye lambarka ne.  Wannan zai sa manhajar dake kamfanin wayarka ita ma ta boye lambarka idan ta tashi isar da kiran mai wayar.  Kenan, kamar a kaikaice kana gaya wa kamfanin wayarka cewa “Ina bukatar sirri kan wannan kira.  Kada a nuna wa kowa lambata.”  Nan take za su boye lambarka.  In har kaga wani ya iya gano lambar wayarka bayan ka boye, to an samu hadin kai ne na musamman tsakanin kamfanin TrueCaller ko manhajar da aka yi amfani da ita, don yin hakan.

Don haka, abin da na sani kuma na tabbatar kenan, cewa muddin aka boye lamba, sai dai manhajar ta toshe lambar daga isowa, tunda mai shi ya nuna rashin amincewa da wanda yake kira kenan (haka ake daukan lamarin).  Amma muddin ba a boye lamba ba daga wayar mai kira, idan aka kira wani layi dake kan wayar dake da manhajar TrueCaller ko makamantanta, nan take lambar mai kira za ta bayyana.  Sannan ka sani, dole ne sai kana ma da yanayin Intanet mai karfi a wayarka sannan a iya bayyana maka lambar da ake iya bayyana ta kai tsaye.  Shi yasa za ka ga ana ce maka: “You Need 3G/4G…” misali, a yayin da manhajar ke kokarin gano maka lambar wani ko wata.

A tambayarka ta biyu ka bukaci sanin yadda ake rufe shafin mutumin da Allah yayi masa rasuwa a Facebook.  Wannan abu ne mai sauki.  Cikin shekarar 2012 in ban mance ba, hukumar Facebook sun samar da wani tsari da zai taimaka wa iyalai ko yan uwa ko abokan duk wanda ke da shafi a dandalin amma daga baya ya rasu.  Za ka iya samun wannan bayani a nan: https://www.facebook.com/help/contact/228813257197480.  Idan ka shiga za ka ga wani dan gajeren fom ne da ake son ka cika, dauke da bayanan da suka shafi mamacin, da alakar dake tsakaninka dashi, sannan a karshe za a bukaci ka loda hoton takardar shedar rasuwarsa da na haihuwarsa, don samun tabbaci kafin su rufe shafin baki daya.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.