Sakonnin Masu Karatu (2016) (7)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

124

Assalamu alaikum, ina da tambaya.  Shin, mene ne yake jawo girgizar kasa a wasu daga cikin sasannin duniya?  Kuma don Allah me ake nufi da “Boradcast Message” a kowace wayar salula kuma ta yaya ake amfani da shi?  Wassalamu alaikum.  Sako daga Bashir Mustafa – 08108729096

Wa alaikumus salam Malam Bashir, barka da warhaka.  Daga cikin manyan dalilan girgizan kasa na zahiri akwai gocewar farantan duwatsu dake karkashin kasa, wadanda ke dauke da wannan duniya tamu, wanda ke kasancewa a yayin da suke juyawa a kan sasanninsu.  Wadannan farantai (jam’in “faranti”) su ake kira: “Tectonic Plates” ko “Plates Tectonics” kamar yadda muka yi bayani a kasida mai take: “Tsaunuka Masu Aman Wuta.”  Bayan haka, daga cikin dalilai akwai samuwar babbar girgizar kasa da ya faru a wani mahali dake kusa.  Wannan girgiza na iya haddasa karamar girgizar kasa.

Wasu daga cikin kananan dalilai akwai aiwatar da gwajin makamin nukiliya, kamar yadda muka karanta a doguwar kasidarmu kan makamashin da makamin nukiliya, shekaru shida da suka gabata.  Yin gwajin makamin nukiya kan haddasa gocewar duwatsun karkashin masu juyawa a sasanninsu, wanda kuma hakan zai iya hadda girgiza mai girma.  Shi yasa kasashen duniya karkashin Majalisar Dinkin Duniya suka rattafa kan hana wannan gwaji.  Sannan akwai ruftawar manyan ramukar karkashin kasa sanadiyyar hako ma’adanai, wato aikin kuza kenan.   Bayan wannan, yana da kyau kuma mu fahimci cewa yawaitar girgizar kasa na daga cikin kananan alamomin tashin kiyama.  Allah mana jagora baki daya, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, sunana Muhammad Ghali daga Keffi jihar Nassarawa.  Ina Facebook sai aka aiko mini da bukatar abota (Friend Request).  Da na amince, sai ya rika turo mini da sakonnin batsa kuma ni ba na so.  Yaya zan yi in toshe shi daga layin abokaina?  Na gode.  –  08161744731

Wa alaikumus salam, bark aka dai Malam Muhammad.  Da farko dai yana da kyau, daga yau, duk wanda ya turo maka bukatar neman abota, ka dubi sunansa da kyau; ka taba saninsa a zahirin rayuwa?  In a a, sunansa yai kama da na irin mutanen da kake alaka dasu ko nahiyarsu?  In a a, yana da kyau ka kara duba shafinsa don ganin wasu irin abubuwa ne yake yadawa ko yake rubutawa, kafin karbar abotarta.  A nan ne za ka iya gane cancanta ko rashin cancantarsa ga bukatar da ya aiko maka.

- Adv -

Yanzu tunda haka ta faru, abin za ka yi shi ne, idan a kwamfuta kake hawa shafinka na Facebook, da zarar ka hau, ka nemi wannan abokin naka dake turo maka ire-iren wadannan sakonni na batala, sai ka matsa sunansa, za a kaika shafinsa kai tsaye, wato: “Timeline” kenan.  Sai ka dubi bangaren dama daga sama, inda aka rubuta: “Friends” da “Following” da “Message” da kuma wasu dige-dige guda uku a karshe, kamar haka: “…” (ban da alamun tsakure), sai ka matsa wadannan dige-dige. Idan ka matsa za a sako maka wasu bayanai daga sama zuwa kasa, sai ka matsa na karshe mai suna: “Block” nan take za a tambayeka ko da gaske kana son ka toshe shi, sai ka matsa: “Okay” ko “Yes”, ka daina ganinsa kenan.  Idan ma a waya kake hawa, duk ta wannan hanya za ka bi wajen toshe shi.  Wannan ita ce hanya mafi saukin bayani da fahimta.  Allah sa a dace, amin.


Salaamun alaikum, Malam don Allah ina so a mini bayani cikakke kan ma’anar “GPRS” da kuma “LNB”.  Na gode, ka huta lafiya.  Daga Ibrahim Muhammad, Zaria – 07035294071

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Abin da kalmar “GPRS” ke nufi shi ne, “General Packet Radio Service”.  Tsari ne da wayoyin salula ke amfani dashi wajen aikawa da karban sakonni tsakaninta da wasu na’urorin sadarwa, a tsarin Intanet.  Wayoyin da ke dauke da wannan tsari su ne wadanda ke dauke da siffofin tsarin sadarwa na zamani dake marhalar sadarwa ta uku da ta hudu, wato: 2G da 3G kenan, kamar yadda bayanai suka gabata a doguwar kasidarmu mai take: “Bayani Kan Wayar Salula.”  Wannan tsari, duk da cewa akwai wayoyin dake amfani dashi har yanzu, amma tsohon tsari ne.  Domin mizanin bayanai da yake iya karba ko aikawa dashi ba shi da girma ko yawa.  Daga 56kb ne zuwa 114kb.  Ka ga ko rabin 1MB bai kai ba.

Kalmar “LNB” kuma na nufin: “Low Noise Block” ne.  Bayan haka, akan kira shi da: “Low Noise Converter,” (LNC) ko “Low Noise Downconverter,” (LND), duk dai abu daya ake nufi.  Na’ura ce dake iya karbar siginar rediyon sadarwa daga jikin farantin tauraron dana dam (Satellite Dish), don sarrafa shi zuwa yanayin siginar da na’urar talabijin za ta iya karba da nuna sakon da ke cikinsa.  A takaice dai, wannan na’ura ta “LNB” na’urar “Receiver” ce.  Tana gudanar da ayyuka ne guda uku mahimmai: na farko shi ne karbar siginar rediyo a yanayin sinadarin haske na “Microwave” wanda shi ne nau’in haske mai dauke da bayanai da farantin tauraron dan adam ke karba daga na’urar tauraron dan adam mai shawagi a sararin samaniya.  Aikinta na biyu shi ne kambama wannan na’ura nah aske (Amplification) don bata damar sarrafa shi.  Na uku kuma shi ne sarrafa shi zuwa yanayin da na’urar harba bayanai ga talabijin za ta iya fahimta, wato: “Satellite Receiver” kenan.

Wadannan, a takaice, su ne ma’anonin wadannan kalmomi.  Da fatan ka gamsu.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.