Sakonnin Masu Karatu (2017) (28)

Ci gaban sakonnin masu karatu. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

94

Salaamun alaikum, barka da himma Baban Sadik; gaisuwar girmamawa dangane da shafinka na Kimiyya Da Kere-Kere.  Wallahi ni dai kaine ka ja hankalina na jibinci karanta AMINIYA saboda jin dadin bayananka mai ilmantarwa. Ina godiya.  Allah ya kara fasaha kuma da fatan ka yi sallah lafiya. Daga M. Bashir Zaria

Wa alaikumus salam Malam M. Bashir, ina maka fatan alheri, tare da jin dadin musamman ganin cewa wannan shafi ya yi tasiri a rayuwarka wajen afkar dakai cikin karatun jaridar AMINIYA.  Ina rokon Allah ya kara maka himma, da jajircewa, da kuma basira don fahimtar abin da kake karantawa.  Na kuma gode da addu’o’inka gaba daya.  Allah saka maka da alheri, amin.


Assalam da fatan an wuni kalau, Malam.   Daya daga cikin mabiya filin kimiyya ta jaridar Aminiya ne ke tafe da wata bukata.   Bukatar kuwa ita ce: ina neman shawara game da aiki da akeyi a yanar gizo wadda a kan yi a samu kudi wato Freelance. Na samu nasarar rajista a freelancer.com  a fannin Graphics Design, amma daga bisani suka bukaci in biya kudi kimanin dala biyar ($5) ta Mastercard dina. Mallam don Allah neman karin haske.  Luqman Suleiman Abbas daga Maiduguri

Wa alaikumus salam, Malam Lukman barka ka dai.  Tsarin “Freelancing” hanya ce ta yin aiki ta hanyar Intanet, ba tare da haduwa da abokan huldarka ba, kuma a biyaka kudinka bayan ka gama aikin da aka baka.  Hanya ce dake bukatar kwarewa a wani fanni na musamman.  Akwai gidajen yanar sadarwa a Intanet da dama dake bayar da wannan dama, tunda zai yi wahala ace kowa ya mallaki shafinsa don tallata kwarewarsa ga duniya.  Ire-iren wadannan shafuka ne suka baka dama kayi rajista, don tallata kwarewarka a ilimin zanen-hotunan kwamfuta.  Shafin freelancer.com na daga cikin shahararru a Intanet.

Dangane da bukatar da suka yi cewa sai ka biya dalar amurka biyar kuma ($5), wannan ladar hidimar da suka maka ne, wanda ya kunshi baka damar yin rajista, wanda hakan zai sa masu bukatar kwarewarka su sameka kai tsaye, ba matsala.  Bayan wannan, za ka rika amfani da manhajojin da suka tanada ne a shafinsu wajen musayar bayanai tsakaninka da wadanda zasu bukaci kwarewarka nan gaba.  Wannan kuwa, kamar yadda za ka gani, hidima ce mai girma da suke wa mutane irinka, kuma yana bukatar kudaden tafiyar da shafin gaba daya, wanda daga ire-iren wadannan hanyoyi ne suke tarawa.

Don haka, idan ka samu natsuwa da kuma gamsuwa da tsarin mahallin, da cewa yin rajista ko biyan kudin rajistan zai baka damar haduwa da kwastomomi ne nan gaba da za su iya baka aiki har ka samu kudaden shiga, kana iya amfani da katinka na ATM don biyan kimar wannan kudi, wato: $5.  Idan kuma baka gamsu ba, kana iya bari.  Amma ka sani, biyan kudin zai taimaka wajen bayyanaka ne, tare da tallata ka ga dimbin masu hawa shafin ne don neman masu kwarewa daban-daban.

Wannan shi ne dan gajeren bayanin da zan iya maka dangane da wannan tsari.  Ina maka fatan alheri da dacewa cikin abin da ka sa a gaba na alheri.  Kuma da fatan ka gamsu.  Na gode.


 

Assalamu alaikum, da fatan Malam ya wuni lafiya, Allah ya kara mana ilimi da basira.  Dan Allah Malam a taimaka min da takaitaccen bayani a kan Blogging da kuma Web Hosting.

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka dai.  Kalmar “Blogging” na ishara ne ga manhaja dake dauke da tsarin taskance bayanai a shafukan Intanet, musamman ra’ayoyinka kan harkokin rayuwa.  Wasu kwararru kan fassara kalmar da: “Taskar Intanet”  ko kuma “Mudawwana.”  Duk dai kokari ne na ganin an bayyana hakikanin abin da manhajar ta kunsa.  Akwai shafukan Intanet da dama dake bayar da damar yin rajistar Taska a Intanet, kyauta.  Shahararru daga cikinsu su ne: “Wordpress” (http://www.wordpress.org) da kuma “Bogger” (http://www.blogger.com) wanda kamfanin Google ya mallaka.  A farkon lamari, kamar shekaru goma da suka shude, kwararru a fagen sadarwa da aikin yada labaru (kamar ‘yan jaridu) ne kadai suke amfani da wannan tsari ko manhaja wajen isar da ra’ayoyinsu ga duniya.  Amma a halin yanzu an samu ci gaba, ta inda kamfanonin kasuwanci da hukumomin gwamnatocin kasashen duniya suka shiga cikin harkar tsundum su ma, don isar da sakonni kan abin da ya shafi manufofinsu na kasuwanci ko makamantan hakan.

A daya bangaren kuma, kalmar “Hosting” na ishara ne ga tsarin taskance bayanai da shafukan Intanet, don baiwa masu ziyara damar isa gare su, a wata kwamfuta ta musamman dake iya mika su ga kwamfutocin da suka bukata.  Wannan kalma tana da alaka ne na kai tsaye da fannin ginawa da tsara gidan yanar sadarwa, wato: “Web Design.”  Duk wani gidan yanar sadarwa idan aka gama gina shi, karshensa na karewa ne a tumbin wata kwamfuta da za rika mika wa masu ziyara duk shafin da suka bukata, ta hanyar adireshin dake zunguro shafin kai tsaye ko a kaikaice.  Akwai kamfanonin dake adana shafukan Intanet a duniya da dama, don baiwa masu ziyara damar isa ga bayanan.  Shahararru daga cikinsu dai su ne: “Hostgator” (http://www.hostgator.com) da kuma “GoDaddy” (http://www.godaddy.co.uk). 

Wannan shi ne bayani a takaice, kan ma’anonin kalmomin guda biyu.  Don neman karin bayani, kana iya ziyartar wadannan shafuka da na kawo don ganin abin a aikace, a misalce.  Fatan an gamsu.  Na gode.


 

Salamun alaikum Abban Sadik.  Dan Allah ni ba ni da waya babba balle ince a tura mini kasidun ta Imail.  Ina bukatar kasidar  Tsibirin Bamuda ne, don Allah a buga min a jarida ni ma in karanta.

Wa alaikumus salam, barka dai.  Tabbas an buga kasidar Tsibirin Bamuda a wannan shafi har sau biyu.  Kuma ganin cewa kasida ce mai tsayi, kuma ta maimaitu a wannan shafi mai albarka, ina iya cewa ma tana cikin kasidu da suka fi sauran shahara a tsakanin masu karatu, na sanya dokar tsayar da sake buga ta a wannan shafi na jarida.  Sai dai idan mai karatu na da adireshin Imel, ko kuma yana da wayar salula mai iya hawa Intanet, sai ya garzawa zuwa babbar Taskar Baban Sadik dake: https://babansadik.com don samun daman karantawa ko ma saukar da kasidar kai tsaye, ba tare da matsala ba. 

Don haka, idan kana da wayar salula mai amfani da kwamfuta, ba dole sai kana da Imel ba, kana iya zuwa wancan shafi namu, inda nake taskance dukkan kasidun da aka taba buga su a wannan shafi, shekaru 10 da suka gabata ko ma 11, don fa’idantuwa da duk abin da kake sha’awa na ilimi.  Da fatan za a gafarceni kan wannan doka.  Allah sa a dace, amin.


 

Assalamu alaikum warahmatullah.  Baban Sadik ga tambayata kamar haka: idan na shirya da masu “Cyber Cafe” kan cewa za su jona ni in rika amfani da siginar Intanet dinsu daga inda nake, kuma suka jona ni din; shin ba za su rika ganin duk wani motsina ko aikina ba, tunda da siginar Intanet dinsu nake amfani?  Na gode, Allah taimaka.

Wa alaikumus salam, barka dai.  Idan har masu shagon mashakatar lilo (Cyber Cafe) suka jona wayarka ko kwamfutarka da siginar Intanet din shagonsu, babu abin da za su iya gani na shafukan da kake hawa ko mu’amala dasu.  Ba ma su kadai ba, hatta kamfanin da suke basu siginar Intanet (MTN ko 9Mobile) ba su iya ganin shafukan da ake mu’amala dasu.  Abin  da zai sa su iya gani shi ne, sai in sun yi amfani da wata manhaja ta musamman don kutsawa cikin wayarka ko satan layin siginar Intanet din dake tsakanin wayarka da shafin Intanet din da kake mu’amala dasu.  Yin hakan kuma da kamar wuya.  Domin a ka’ida da dokokin mu’amala da Intanet, haramun ne; zan maimaita: HARAMUN NE ga kamfanin sadarwa ya yi amfani da wata na’ura ko manhaja don tatso abin da masu amfani da siginar Intanet din da yake bayarwa.  Idan har kuwa aka gano hakan, ana iya cajansu zuwa kotu kuma a yi nasara a kansu. 

Da fatan ka gamsu da wannan dan gajeren jawabi nawa.  Allah sa mu dace baki daya, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    Masha Allah

Leave A Reply

Your email address will not be published.