Sakonnin Masu Karatu (2017) (9)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

240

Assalamu alaikum Baban sadik, barka da kokari.  Ina cikin masu bibiyar kasidarka mai take “Mu Koyi Programming a Hausance” na Jaridar Aminiya.  Abin ya kayatar dani matuka.  Duk da haka ina da wasu shawarwari.   Da na fahimci dukkannin bayanan da ke kasidun gabatarwa ne.  Kuma lallai mutannanmu na Arewa na amfana da gudunmuwarka.   Amma ina ganin da zaka yi wasu darussa na musamman kan wani yaren gina manhajar kwamfuta na musamman cikin harshen Hausa, zai taimaka matuka.   Sannan zan so sanin ko kana da wani group or page naka da ma’abota programming ke halarta domin tattaunawa da masu koyo ko gwanayen programming a arewacin Najeriya? Idan babu, to lallai akwai bukatarsa.

Ni sunana Ibrahim Baba, dalibi a fannin “Computer Science” a jami’ar Lagos (University of Lagos).  Ina mika gaisuwa da godiya.  ibbaba234@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Ibrahim Baba.  Allah saka da alheri da wadannan shawarwari.  Lallai kam kamar yadda ka gani, wadannan kasidu na koyon “Programming” gabatarwa ne zalla, kuma na yi iya kokarin ganin ban cika bayanai da yawa  ba, tare da kokarin game dukkan bangarorin da suka shafi fannin.  Bayan haka, duk da cewa na yi ta kawo misalai musamman a kashi na 10 da na 11, daga wasu yarukan gina manhaja irin Python da kuma JavaScript, amma ban kebance wani yare na musamman ba.  Gamammen darasi ne kan tsari da kintsi da yadda ake gudanar da abin ne.

Sai bayan na gama bayani kan yadda tsarin fannin yake a jumlace, sannan daga baya zan fara darasi na musamman kan yaren “Python”.  Na dauki wannan yare ne saboda saukinsa da kuma takaitattun tsare-tsarensa.  Ba kamar “Java” ko “C++” da suke da ka’idoji masu yawa kuma da tsare-tsare masu tsauri.  Darasin “Python” din ma dauke shi a matakai uku ne.  Matakin farko zai kunshi sanayya ne kan yaren, da wani abu na tarihi, da kuma shahararrun ka’idodinsa.  A yayin da nake wannan kuma, zan ware wani darasi don karantar da yadda ake gina shafukan Intanet, ta hanyar HTML, da CSS, da JavaScript, ba wai ta amfani da manhajoji irin su “Dreamweaver” ba.  A tunanina koyon wadannan nau’ukan ilimi ta hanyar yarensu kai tsaye, shi ne abin da zai taimaka wa mutum wajen kwarewa a fannin.

- Adv -

Dangane da abin da ya shafi ko akwai wani shafi da na tanada don tattaunawa kan wannan fanni, amsar ita ce a a.  A halin yanzu dai akwai shafi da na dora a Intanet cikin watan Mayu da ya gabata don zuba dukkan kasidu da nake gabatarwa a wannan shafi dake jaridar Aminiya.  Na yi haka ne don adana su, tare da baiwa masu karatu daman kaiwa gare su a duk sadda suke bukata, maimakon inyi ta tura musu ta Imel lokacin daban-daban idan suka tashi bukata.  Na gina wannan shafi ne da hannuna, daga farko har karshensa, kuma za ka hawa shafin a wannan adireshi: https://babansadik.com.

A bangaren darussan bidiyo kan Programming kuma, ban fara tanadar komai ko ba.  Domin yanzu ne na fara dauko darussa kan Programming din.  Shi yasa nake daukan abin mataki-mataki.  Matakin farko shi ne karantarwa ta hanyar rubutattun darussa, kamar yadda ka gani.  Mataki na biyu kuma shi ne samar da darussan bidiyo din, wanda nake sa ran in fara kafin karshen wannan shekara, wato bayan gama darasin koyon “Python” kenan in Allah yaso.  A yayin da nake wannan kuma, a halin yanzu na fara gina wani shafin Intanet wanda zai kunshi darussa a matsayin azuzuwa na koyon Programming, da wasu nau’ukan ilmi da nan gaba zan kara.  Wannan shafi dai zan fara gina shi ne da turanci, daga baya sai in samar da sashi na musamman a harshen Hausa a kan shafin, wanda a cikin zan zuba wadannan darussa na koyon Programming amma a tsarin darasi irin na aji, wato: “Lessons”.  Wannan gidan yanar sadarwa dai zan gina ne ta amfani da manhajar koyon karatu a Intanet, “Learning Management System” (LMS), irin su “LearnDash” ko “LearnPress,” ko “CoursePress,” ko kuma “LifterLMS”; duk wanda na gamsu da kudurarsa wajen biya min bukatar abin da nake ganin zai taimaka wa al’umma a wannan fanni.

A kan wannan shafi ne har wa yau zan samar da Zaure na musamman don baiwa masu rajista a shafin damar tattaunawa da kwararru irinku da zan gayyata su rika taimakawa wajen warware ma dalibai abubuwan da suka shige musu duhu.  Zan yi amfani ne da manhajar “BuddyPress” ko “bbPress”; duk wanda naga zai dace da mahallin da na samar dai.  Ina sa ran shafin ya kunshi darussa gajeru masu fa’ida, wadanda masu karatu za su iya gamawa cikin kankanin lokaci kuma su samu takardar shedar gamawa, wato: “Certificate.”

Wadannan, a takaice, su ne kadan cikin abubuwan na shirya kuma nake rokon Allah ya bani damar aiwatar dasu don amfanin jama’a.  sai dai dole ne a yi hakuri dani saboda yanayin shagulgula na, ba lalai bane a lokacin da nake sa ran gamawa in gama.  Amma abin da ke tabbace shi ne, zan yi, kuma in sha Allahu zan yi din.  Da fatan ka gamsu da wannan takaitaccen jawabi.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.