Wannan mako za mu leko gidan yanar sadarwa na Gumel.com ne, wanda Malam Salisu Hashim Gumel ya dauki nauyin ginawa da tafiyar dashi. A sha karatu lafiya.
Daga wannan mako za mu fara kai ziyara ne zuwa wasu gidajen yanar sadarwa na harshen Hausa, don baiwa masu karatu daman ganin yadda suke, da irin tsarin dake cikinsu, da kuma fa'idar dake tattare da ire-iren wadannan shafuka.
A cikin makon da ya gabata ne aka gabatar da bukukuwa tare da tarurrukan bita da nazarin ci gaban da fasahar Intanet ta yi cikin shekaru ashirin da suka gabata; wato daga shekarar 1989 zuwa 2009. Wadannan tarurruka sun samu halartar masu…
Makonni biyu da suka gabata ne aka gabatar da bukuwa da tarurrukan bita da nazari da kuma tsokaci kan cikar fasahar Intanet shekaru ashirin (1989 – 2009) da bazuwa a duniya. Kamar yadda labaru suka gabata a wannan shafi kan tarurrukan da…