Tasirin Mu’amala da Wayar Salula (1)

Kashi na 24 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

300

Matashiya

A yau ina neman afuwan masu karatu, kan rashin ci gaba da silsilar da muka faro a baya kan asalin tunani tsakanin kwakwalwa da zuciyar dan adam.  Hakan ya faru ne saboda nisa da nayi da dakin bincike na.  Ayyuka sun dabaibaye ni, don haka na nemi uzuri.  Idan Allah ya kai mu mako mai zuwa za mu ci gaba.  A gafarce ni don Allah.  A yau za mu ci gaba da silsilar mu ne kan wayar salula da yadda ake mu’amala da ita.

A zangon baya idan masu karatu basu mance ba, mun tsaya da bayani ne kan  Nau’ukan Matsalolin Wayar Salula.  Muna kuma kawo wadannan bayanai ne filla-filla, kamar yadda na sanar a zangon farko, don jama’a su samu gamsuwa kan abin da ya shafi wayar salula gaba dayanta.  A zangon yau ya kamata mu yi magana ne kan Amfanin Wayar Salula, to amma saboda ganin cewa mun sha tattauna wannan maudu’i a baya, za mu wuce zuwa zango na gaba, wato Tasirin Wayar Salula Ga Al’umma.  Wannan matakin bincike ya kasu kashi biyu; kashin farko ya ta’allaka ne ga dalilin yaduwar wayar salula a duniya baki daya, musamman a kasashe masu tasowa.

To amma kwanakin baya na kawo kasidar da na gabatar a taron shekara-shekara na Kungiyar Tsangayar Alheri, inda na kawo dalilan yaduwar wayar salula a duniya, kamar: saukin mu’amala, da saukin farashi, da samuwar nau’uka daban-daban, da yawaitan kamfanonin sadarwa, da zumunci tsakanin kayayyakin sadarwa, da kuma bunkasar bincike kan hanyoyin sadarwa.  Bangare na biyu da ya shafi tasirin wayar salula a al’umma shi ne abin da za mu kawo a yau.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare da mu.

Gamammiyar Tasiri ga Al’umma

- Adv -

Tasirin wayar salula da tsarin sadarwarta na da gamewa matuka, kamar yadda na san da dama daga cikinmu zasu sheda.  Akwai gamammiyar tasiri kan al’umma baki daya, da kuma kebantacciyar tasiri da ya shafi mai mu’amala da wayar.  Sanin hakan na da muhimmanci don samun fa’idar da ke tattare da wannan makamin sadarwa ba tare da cutarwa ba.  Za mu fara da gamammiyar tasiri ga al’umma:

Abu na farko shi ne ci gaban tattalin arzikin kasa. Tasirin bunkasar fannin sadarwa yana da gamewa sosai, musamman kan tattalin arzikin al’umma. Domin  hakan na saukake tsarin kasuwanci, da tsarin karantarwa, da tsarin lafiya, da sauran fannonin rayuwa baki daya. Wannan na daga cikin abin da ke kara habbaka tattalin arziki a kasa. Abu na biyu shi ne yaduwar ilmi.  Akwai sanayya da wayar salula ke samarwa ko yadawa a al’umma. Jama’a kan aiwatar da sadarwa a tsakaninsu, musamman a lokutan azumi ko sallah ko wasu bukukuwa na addini. Har wa yau akwai nau’ukan ilmi da ake yadawa ta hanyar wayar salula.

A makarantu wasu dalibai kan yi amfani da wayar salula don taskance darasin malami na sauti ko na bidiyo.  Abu na gaba shi ne yaduwar akidu da al’adu.  Wannan shi yafi kowanne hadari daga cikin tasirin da wayar salula ke yi a tsakanin al’umma. Akwai al’adu na banza da wadanda suke masu kyau, da akidun addini ko wasu al’ummomi masu kyau da munana, wadanda ake yadawa ta wayar salula.

Bayan nan, ta bangaren addinin musulunci akwai hadisan karya da wasu ke turowa (watakila saboda rashin sani) kan falalan wasu ayyukan ibada (irinsu azumin watan Rajab – azumin tsofaffi – da sauransu), wadanda duk basu inganta ba a bincike na ilmi.  Sai a rika kiyayewa.  Duk wanda ya turo maka sako kan wani hadisi kuma kai baka san ingancinsa ba, kada ka tura wa wani sai ka tambayi malamai ingancinsa tukun.  Akwai sakonni da ake turowa ace idan ka samu ka tura wa wani, in baka yi haka ba za ka rasa abu kaza ko abu kaza zai same ka, duk wannan rudu ne, kuma masu yada su su ji tsoron Allah.

Abu na gaba shi ne yawan sace-sace a tsakanin al’umma.  Tabbas yaduwar wayar salula ta haddasa yaduwa ko karuwar sace-sace a tsakanin al’umma musamman a manyan biranenmu.  Cikin wannan makon aka fisge wayar salular wani ma’aikacinmu, yana rike da ita yana waya.  Kawai wani ya fisge.  Ka ji karfin hali.  Duk sadda barayi suka kutso gidajen jama’a ko suka darkake su a hanya, abu na farko da suke fara yi shi ne kwace wayoyin salularsu, don tsoron kada a musu cunne ga hukuma. Haka idan aka ganka da waya mai tsada, to, ka yi hankali, musamman idan a cikin birni kake.  Babban abin da ya fi tayar da hankali shi ne yaduwar kasuwannin da ake sayar da ire-iren wadannan wayoyi na salula.  Ya kamata hukuma ta binciki masu sayar da tsofaffin wayoyin salula, ta kuma basu ka’ida da za su rika amfani da ita idan an kawo musu tsohuwar wayar salula kafin su saya.  Domin a galibin lokuta ana kawo musu wayoyin sata suna saya sannan su sayar.

Akwai wata ‘yar uwa da aka sace wa wayoyinta guda biyu lokaci guda, a waje guda.  Nan take ta sanar da ni, nace to meye abin yi yanzu? Ta ce ta san inda za ta je ta gansu.  Tana zuwa inda ake sayar da tsofaffin wayoyin salula kuwa sai ga guda daya daga cikin wayoyin (watakila kafin ta zo an sayar da dayan).  Nan fa suka fara dauki-ba-dadi kan wayar, yace sam ba zai bata ba.  Ka ji karfin hali.  Abin mamaki har wajen jami’an tsaro aka je, amma a karshe mahaifinta yace mata ta bar maganar kawai; sai wata wayar aka saya mata.  A ka’ida ya kamata duk masu sayar da wayoyin salula tsofaffi su rika bincikan wanda ya kawo musu wayar sayarwa, domin akwai da yawa na sata ne. In kuwa basu yi hankali ba, to nan gaba za su samu kansu cikin rudu da tashin hankali.  Allah sawwake, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.