Tasirin Mu’amala da Wayar Salula (2)

Kashi na 25 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

241

Abu na gaba shi ne zamba-cikin-aminci, wato 419 kenan.  Akwai masu kiran mutane a waya ko su turo musu sakonnin tes cewa sun ci reful kaza, za a basu kaza da kaza, amma su turo katin MTN na dubu daya da dari biyar ko wani abu makamancin haka. Wadannan barayi ne.  Ko kuma irin sabon tsarin da ‘yan mata ke bi a yau. Sai mace ta kira ka ko ta dame ka da filashin.  Idan ka kira sai ta fara kiran sunan wata, ko wani daban.  Da zarar ka ce ba shi bane, sai ta ja ka da hira: “kai a ina kake da zama?  Ya sunanka?”  Da dai zantuka makamantan haka.  Da zarar ta ga ka fara sakewa da ita, tunda mace ce, sai a rika maka filashin ko ma kira ka, kana daukawa a ce: “don Allah ka kira ni mana.”  Kana kira, sai a ce ai an kira ne don a gaishe ka; an ji kwana biyu ba a gaisa ba.

A haka a haka, sai a fara bukatar ka turo katin waya, ko a fara karanto maka matsaloli.  Duk wannan zamba ne cikin aminci.  Don haka duk wanda ya kira ka idan baka sanshi ba, ko yace wani yake nema, ka ce baka sanshi ba.  Kada ka kuskura ka zama aboki da mutumin da baka san dabi’u ko yanayinsa ba.  In kuwa ba haka ba za ka sha mamaki. Wannan dabi’a ta yadu sosai.  A yau kam, ba irin daren da jemage bai gani ba; sai na mutuwarsa.  Allah dada kare mu.

Abu na gaba da yaduwar wayoyin salula ta haifar a tsakanin al’umma shi ne abin yi.  Jama’a da dama sun samu sana’ar yi sanadiyyar harkar wayar salula.  Wasu kan sayar da sababbin wayoyi ne, wasu tsofaffi, wasu kan sayar da bangarorin wayar ne, wasu kuma aikinsu shi ne gyara wayar idan ta lalace maka, wasu kuma aikinsu shi ne sanya wa masu wayar salula wakoki da hotunan bidiyo na wake-wake ko na karatuttuka, don shakatawa. Wannan, ta wani bangaren, ba karamin alfanu bane ga al’umma.  Illa dai nasiha ga masu sanya wakoki a wayar salula, su ji tsoron Allah kada su rika sayar wa jama’a abin da zai lalata musu tunaninsu ko ya cutar da imaninsu.  Amana ne a gare su, kuma sai Allah ya tambaye su ranar kiyama.

Abu na gaba shi ne ingantuwar zumunci.  Lallai an samu ingancin zumunci a tsakanin jama’a, musamman a kasar Hausa.  Yawan tafiye-tafiye don ziyara kadai sun ragu.  Domin kana iya buga waya ko ka rubuta sakon tes ka tura wa dan uwa, sai idan zama ya tsawaita ko wani tsananin bukata da ke sa a yi tafiya.  Bayan haka, hatta mutumin da baka taba ganinsa ba kana iya zumunci da shi muddin ka samu lambarsa ta hanyar da ta dace.  Kasancewarmu musulmi wannan ya dada bamu dama mai kyau kan haka.

Sai abu na karshe da nake son dakatawa a kai, wato saukin rayuwa.  Wayar salula da yaduwarta sun sawwake yadda ake tafiyar da rayuwa baki daya. Dukkan dalilan da na zayya a sama suna nuni ne zuwa ga hakan.  Kana kwance a dakinka ne, ko a tsaye kake, ko a kishingide, ko a shagonka kake, ko a harabar masallaci kake, ko a ina kake, za ka iya aiwatar da sadarwa.  Sannan kana iya mu’amala da fasahar Intanet ta wayar salularka.  Duk wannan ya dada saukake mana tsarin rayuwa musamman ta hanyar sadarwa.

- Adv -

Kebantattun Tasiri ga Mai Mu’amala

Bayanan da suka gabata kan tasirin wayar salula ne ga al’umma baki daya. Akwai wasu kebantattun tasiri da suka shafi daidaikun mutane da ke amfani da wayar salula.  Abu na farko shi ne tasirin wayar salula kan dabi’ar mai amfani da ita.  Amfani da wayar salula kan samar da wata sabuwar dabi’ar rayuwa ta musamman da mai yin hakan bai sani ba.  Abu na farko shi ne canza masa tsarin tunani, musamman wajen gaugawa da ci-da-zuci.  Wanda ya saba mu’amala da wayar salula gani yake kamar komai zai iya yi muddin ta hanyar sadarwa ne; da abu mai kyau da mara kyau.

Sannan  akwai sauyin tunani wajen tafiyar da rayuwa. Da dama cikin samari kan ji nakasa idan wayarsu tsohuwa ce ko ba wacce ake yayi ba ko  kuma idan ba su da wayar ma gaba daya.  Haka idan suna da waya mai tsada, sai su rika jin ai su wani ne.  Haka ma ‘yan mata su ke.  Nan gaba za mu karanta bayani kan irin nau’in wayar da ta kamata mutum ya saya.

Abu na gaba shi ne tasirin wayar salula kan lafiyar mai mu’amala da ita.  Da yawa cikin samari kan kashe dare suna waya ko suna 2go, ko BB Chat idan masu Blackberry ne; duk hakan kan yi tasiri kan lafiyar jikinsu, musamman idan dalibai ne su.  Haka kuma, yawan amfani da wayar salula musamman lokacin tuki ta hanyar karba kira ko rubuta tes, yana barazana ga rayuwa.  A kasar Kanada da Amurka an tabbatar da cewa kaso mafi yawa na dalilan da ke haddasa hadarurrukan mota a kan manyan titunan kasashen duk ta sanadiyyar mu’amala da wayar salula ne.  Sai abu na karshe, wato tasirin wayar salula kan tattalin mai mu’amala.

Da yawa cikin samari ‘yan karya sukan kashe galibin kudadensu ne wajen sayen katin waya don kiran ‘yan matansu ko don tura musu.  Hakan ba haramun bane a shari’ance idan mutum yayi da manufa mai kyau, amma sau tari za ka samu kundunbala ce ake yi. Sai a bar abin da ke da muhimmanci a yi wanda bai kai shi muhimmanci ba.  Har wa yau wasu sun fi son a duk lokaci a gansu da waya mai tsada ko wacce ake yayi.  Wannan ke sa dole su ci bashi ko su kure aljihunsu don ganin sun mallaki wayar da suke bukata.

Wadannan, a takaice, su ne gamammu da kebantattun tasirin da wayar salula da yaduwarta ke haddasawa a al’umma ko ga daidaikun mutane.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.