Tekun Atlantika, Da Albarkatun Da Ke Cikinsa (1)

A kashi na hudu cikin jerin kasidunmu kan tekunan duniya, yau za mu fara bayani kan teku na biyu a girma, wato tekun Atlankita kenan, wanda aka fi sani da Tekun Legas, a Najeriya. A sha karatu lafiya.

962

Wannan shi ne kashi na 4 cikin jerin kasidu masu take: “Tekunan Duniya da Abubuwan da Ke Cikinsu.”


Tekun Atlantika (Atlantic Ocean)

Matashiya:  Watanni uku da suka gabata mun fara silsila kan tekunan duniya da yanayinsu da irin abubuwan da suke dauke dasu na amfanin dana dam.  Mun dakata a kan bayanin tekun Pacific ne, wato teku na farko kuma mafi girma a duniya kenan.  Kamar yadda bayani ya gabata a baya, dukkan tekun nan na duniya asalinsu teku ne guda daya.  Dalilin rabuwarsu dai ko karkasuwansu bai rasa alaka da bigiren da bangaren tekun yake, da irin nahiyoyin da yake makwabtaka dasu, da tsibiran dake cikinsa.  Hakan ne yasa aka samu rarrabuwa.

A yau cikin yardar Ubangiji, bayan wani lokaci da muka kwashe muna tattaunawa kan tsarin mu’amala da Password da ka’idojinsa, mun sake dawowa don ci gaba da bayani kan tekunan duniya.  Za mu tashi da bayani kan teku na biyu wajen girma a duniya, wato Tekun Atlantika (Atlantic Ocean).

Tekun Atlantika, ko “Atlantic Ocean” kamar yadda ake ambatonsa a harshen Turanci, ko kuma “Tekun Legas” kamar yadda a al’ada muke kiransa a kasarmu, shi ne teku na biyu wajen girma a duniya, bayan tekun Pacific da bayaninsa ya gabata a baya.  kalmar “Atlantic” da ake danganta wannan tekun da ita dai ta samo asali ne daga kalmar “Atlas” wanda asali sunan wani ne daga cikin shahararrun mutanen tsohuwar Daular Romawa.  Daga sunansa ne ake danganta wannan teku.  Bayan nan, a bangaren gabashin Afirka kuma a baya ana kiran wannan teku ne da suna: “Ethiopian Ocean,” wato “Tekun Habasha.”  To amma bayan wasu lokuta sai aka tabbatar da suna guda don ishara ga wannan teku, wato: “Atlantic Ocean,” kamar yadda muke ambatonsa dashi yanzu.

Wannan teku, idan aka yi la’akari da girmansa, ya kai kashi daya cikin biyar (1/5) na fadin kasar duniya baki daya, wato kashi ashirin kenan cikin dari (20%).  Ta bangaren yawan ruwa kuma, idan aka tara ruwan duniya, tsakanin wanda ke tekuna da wanda ke koguna da rafuka da gulabu, kashi ashirin da tara (29%) na cikin tekun Atlantika ne.

Wajen fadi a iya haddinsa, Tekun Atlantika ya kai fadin murabba’in kilomita miliyan dari da shida da dubu dari hudu (106,400,000 sqkm) idan aka yi la’akari yawan ruwan da ke kwararo masa daga cikin kananan kogunan dake harabarsa kenan.  Shi ne tekun da ya mamaye fadin ilahirin inda ya faro zuwa karshensa, a siffar harafin “S”.  Ma’ana, idan ka hango Tekun Atlantika daga sararin samaniya, za ka ganshi ne a siffar babban harafin “S”.  Shi yasa wasu masana idan aka tambaye su, shin, wani teku ne Tekun Atlantika?  Sai su ce: “Tekun da ya mamaye mahallin kasa a siffar harafin “S”, daga nahiyar Turai-maso-Asiya (Eurasia) zuwa nahiyar Afirka.”

Makwabta

Kamar yadda tekun Pacific yayi makwabtaka da wasu kasashe ko nahiyoyi na duniya, haka ma Tekun Atlantika yayi.  Dalili kuwa shi ne, yana daya daga cikin bangarorin tekun duniya baki dayansa, tunda asalinsu daya ne.

Ta bangaren arewacinsa, Tekun Atlantika yana makwabtaka ne da tekun Aktic (Arctic Ocean). Ta bangaren kudu maso yamma kuma, yayi makwabtaka ne da babban tekun duniya, wato Tekun Pacific.  A bangaren kudu maso gabas kuma, akwai Tekun Maliya (Indian Ocean).  A bangaren kudu tsantsa kuma, Tekun Atlantika na makwabtaka ne da Tekun Kudancin duniya, wato Southern Ocean.

Idan aka dunkule Tekun Atlantika gaba dayansa kamar yadda yake a taswirar duniya, Kambun duniya (Equator) ya raba shi zuwa bangarori biyu ne.  Bangaren farko shi ne bangaren Arewaci, wanda ake kira da suna: “North Atlantic Ocean.”  Sai bangare na biyu mai suna: “South Atlantic Ocean.”  Bayan wadannan bangarori guda biyu, masana sun kara cewa akwai bangaren tsakiya da suka kira: “Central Atlantic Ocean.”  Wannan shi ne bigiren dake tsakanin nahiyar Kudancin Amurka (South/Latin America) da nahiyar Afirka.  Suka ce nau’in dabi’ar ruwa dake bigiren tsakiya ya sha bamban da wanda ke Arewacin Amurka da Turai (America & Europe).

A jumlace dai, Tekun Atlantika na jingine ne a kirjin nahiyar Arewaci da Kudancin Amurka, ta bangaren yamma kenan.  A nan ne ya hade da Tekun Aktik dake makurar arewaci, ta hanyar kananan kogunan dake harabarsa, irin su: Kogin Denmak, da Kogin Greenland, da Kogin Norway, sai kuma Kogin Barents.

A bangaren gabashin duniya kuma Tekun Atlantika na fuskantar nahiyar Turai ne, inda ya hade da Kogin Dutsen Taarik (Jabalu Taariq, ko Gibraltar), wanda shi ne mahadin kogin (Strait) da ya hada alaka tsakanin Tekun Atlantika da babban Kogin Meditaraniyan (Mediteranian Sea).

- Adv -

Girma da Fadi

Idan ka cire kananan koguna dake kwararo masa ruwa, fadin Tekun Atlantika ya kai murabba’in kilomita (Square Kilometers) miliyan tamanin da biyu da dubu dari shida (82,600,000 sqkm).  Yawan ruwan dake dauke a cikinsa kuma ya kai mizanin miliyan dari uku da ashirin da uku da dubu dari shida (323,600,000 cubic meters) a ma’aunin cubic.  Idan ka hade da yawan ruwan dake kananan kogunan dake harabarsa kuma, yawansu ya kai miliyan dari uku da hamsin da hudu da dubu dari bakwai (354,700,000 cubic meters) a ma’aunin cubic.

Tekun Atlantika ne tekun da yafi kowane teku samun ruwa masu shigo masa daga wasu koguna dake haraba ko makwabtaka dashi.  Domin nahiyoyin duniya da yake kusa dasu suna samansa ne.  Wannan yasa duk wani kogi dake makale dasu, ruwansa ke kwararowa zuwa cikinsa kai tsaye.  Shahararrun kogunan da ruwansu ke kwararowa zuwa Tekun Atlantika kai tsaye sun hada da: Kogin tsibirin St. Lawrence, da Kogin Mississipi, da Kogin Orinoco, da Kogin Amazon dake kasar Burazil, da Kogin Rio de la Plata shi ma a Burazil, sai Kogin Congo, da Kogin Naija dake kasarmu Najeriya, da Kogin Loire, da Kogin Rhine, sai kuma Kogin Elbe.  Dukkan wadannan koguna ruwansu na kwarara ne cikin Tekun Atlantika kai tsaye.  A duniya babu tekun dake samun ruwa ta wannan hanya irin Tekun Atlantika.

Zurfi

A bangaren zurfi kuma, Tekun Atlantika yana da zurfi irin nashi, duk da cewa bai kai Tekun Pacific ba.  Mahalli ko bigiren dake da matsakaicin zurfi a cikinsa ya kai zurfin mita dubu uku da dari tara da shirin da shida (3,926 meters).  Bigire mafi zurfi a Tekun Atlantika shi ne mai zurfin mita dubu takwas da dari uku da tamanin (8,380 meters), wanda yayi daidai da taku dubu ashirin da bakwai da dari hudu da casa’in kenan (27,490 feets).  Wannan bigire da yafi zurfi a Tekun Atlantika shi ake kira: “Milwaukee Deep,” kuma yana daidai Tsibirin Puerto Rico ne, can wajen Kudancin Amurka kenan.

Dandano da Dabi’ar Ruwa

Abu ne sananne cewa ruwan teku ya sha bamban da sauran nau’ukan ruwa wajen dandano.  A yayin da ruwan sama da na kogi da na rafi da gulbi suke da gardi wajen dandano, ruwan teku yana da zartsi ne, wato dandanon gishiri kenan.  Binciken malaman kimiyya ya tabbatar da cewa Tekun Atlantika shi ne teku mafi zartsi a duniya.  Ma’ana, darajar dandanon gishiri dake cikin ruwansa ya fi na sauran tekunan duniya sosai.  An kuma kiyasta cewa darajar zartsin dake cikin ruwansa ya fi na sauran da daraja 3.3 zuwa 3.7.

Manyan dalilan da suka sa ruwan Tekun Atlantika yafi sauran wajen dandano da zartsi, a cewar masana, sun hada da: yawan tururin iska dake haurawa zuwa sararin samaniya daga kan tekun.  Dalili na biyu shi ne yawaitan ruwan dake shigowa cikinsa daga wasu kananan koguna dake makwabtaka dashi, kamar yadda bayani ya gabata a baya.  Dalili na uku shi ne, kankarar dake narkewa daga jikin tsaunukan kankara dake cikin tekun.  Wadannan tsaunukan kankara su ake kira “Glaciers.”

A daya bangaren kuma, bigiren da ruwansa yafi karancin zartsi a tekun gaba daya shi ne bangaren Arewacinsa, wato: “North Atlantic.”  Masana suka ce babban dalilin karancin zartsinsa shi ne yawaitan ruwan sama da ake samu a bangaren, wanda ke kwarara cikin tekun.

Tsaunukan Karkashin Atlantika

A kasan Tekun Atlantika, bayan ruwa da kifaye da sauran halittun da Allah ya taskance su don amfanin dan Adam, akwai tsaunuka da ramuka ko gwalalo wadanda Allah ya samar.  Malaman kimiyyar teku sun binciko dukkan wadannan siffofi da abubuwa dake karkashin Tekun Atlantika, tare da ruwaito su ga masu sha’awan karatu ko koyon ilimin dake ta’allake da wannan mahalli mai mahimmanci a rayuwar dan adam a duniya.

Tsaunukan dake karkashin Tekun Atlantika nau’uka uku ne.  Akwai masu tsawo, da matsakaita, da kuma kanana.  Wadannan tsaunuka da malaman kimiyyar teku ke kira da suna: “Ocean Ridges,” sun faro ne daga can kuryar arewacin tekun, daidai tsibirin Iceland, suka gangaro tsawon digiri 50 zuwa kudanci, iya fadin mil 860 (kilomita 1,590).  Daidai inda wannan tsauni yake, a iya bigiren da yafi kowanne bisa zuwa sama, zurfin tekun bai shige mita 2,700 ba (kilomita 2.7 kenan).    A wasu wurare inda tsaunin yayi tsawo sosai, akan hangi tozonsa a saman tekun.  Wannan ke tabbatar da cewa, yadda muke da tsaunuka a tudun kasa da muke rayuwa a kai, haka ake da tsaunuka a ciki ko karkashin tekun duniya.

Daga bigiren tsakiyar tekun atlantika kuma akwai tsauni na musamman da masana ke kira da suna: “Mid-Atlantic Ridge.”  Wannan shi ne tsaunin da ya raba Tekun Atlantika gida biyu daga karkashinsa.  Abin da hakan ke nufi shi ne, tekun ya fi zurfi ne daga bangaren arewaci (North Atlantic) da bangaren kudanci (South Atlantic).  Yayin da tsakiyansa yake da tudu, saboda samuwar wannan tsauni da ya raba tekun gida biyu a karkashinsa.

A bangaren ramuka ko gwalalo kuma, Tekun Atlantika a makare yake da ramuka masu zurfi a karkashinsa.  Ramuka ne da suka faro daga karkashin tekun (Ocean Floor) zuwa can kasa, duk da cewa ba masu fadi bane.  Shahararru daga cikin wadannan ramuka ko gwalalo dake karkashin Tekun Atlantika sun hada da: “Puerto Ricon Trench,” wanda zurfinsa ya kai mita 8,605 (kilomita 8.6 kenan).  Wannan wawakeken rami yana daidai tsibirin Puerto Rico ne.  Sai rami na biyu mai suna: “Laurentian Abyss,” wanda ke gabar tekun a daidai gabashin kasar Kanada, wato arewa-maso-yamma kenan da tekun.  Rami ko gwalalo na uku shi ne: “South Sandwich Trench” da aka kiyasta zurfinsa ya kai mita 8,428 (kilomita 8.4 kenan).  Sai rami shahararre na hudu mai suna: “Romanche Trench” dake kusa da kambun duniya (Equator).  Shi kuma zurfinsa ya kai mita 7,454 (kilomita 7.4 kenan).  Wadannan, a takaice, su ne manyan ramuka ko gwalalon dake karkashin Tekun Atlantika.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.