Tsaga a Jikin Wata: Mu’jiza ko Yawan Shekaru? (1)

Sanadiyyar samuwar wani hoto dake dauke da wata, wanda a jikinsa wata alama ta bayyana mai kama da tsaga, jama’a sunyi ta yaya batu cewa ai wannan tsaga dake jikin hoton wannan wata, asalin tsagar da Allah ke ishara gare ta ne a Al-Kur’ani, wanda ya faru a zamanin Manzon Allah (SAW). Hakan ba abin mamaki bane idan ya tabbata. Sai dai kasancewar duniyar Intanet akwai kwamacala da yawa, yasa na ga dacewar gudanar da bincike don kokarin tabbatar da hakikanin wannan hoto. Shin da gaske asalin hoton wata ne, ko dai za na shi kawai aka yi da manhajar kwamfuta? A wannan mako kasidarmu za ta fara da mukaddima ne kan abin da ya shafi shi kanshi wata; girmansa, da kusancinsa da duniyarmu, da yanayin mahallinsa, da dai sauran bayanai.

592

Mabudin Kunnuwa

Kamar sauran wurare da yanayin zamantakewa na dan Adam, yaduwar jita-jita wata al’ada ce ko dabi’a wacce ke samuwa a duk inda wannan tsarin zamantakewa take.  Tsakanin birni da birni, da kauye da wani kauyen, da kasa da wata kasar, da nahiya da wata nahiyar, duk ba ka rasa yaduwar jita-jita a tsakaniHaka abin yake a duniyar Intanet. Daga cikin dadaddun jita-jitar da ke yawo da yaduwa a duniyar Intanet akwai hoton Wata, mai dauke da tsaga a samansa, wanda ake ta yadawa da kuma sanar da cewa wannan tsaga ko shata ko shaci da ke saman Wata ya samo asali ne tun lokacin da kafiran Makka suka bukaci Manzon Allah (SAW) yasa Wata ya rabe gida biyu, muddin abin da yake ikirari na cewa shi Annabi ne, gaskiya ne.  Wannan hoto mai dauke da Wata da alamar tsagar da ke jikinsa ya shahara sosai a Intanet.  A kalla a iya cewa an samu shekaru kusan goma wannan hoto na yawo a Intanet.  Sanadiyyar wannan shahara ne ma aka samu yaduwar kasidu da sharhi dabam-daban masu tabbatarwa ko kore ingancin wannan hoto.  Har wa yau, wasu na ikirarin cewa an samo wannan hoto ne daga cikin taskar Hukumar Binciken Sararin Samaniya na kasar Amurka, wato NASA, cikin jerin hotunan da masu ziyarar duniyar Wata a kumbon Apollo 11 suka dauko a lokacin ziyararsu, shekaru sama da arba’in da suka gabata.

 

 

Kamar yadda mai karatu zai gani a hoton da na dauko mana daga Intanet, akwai tsaga a saman Wata tabbas, to amma meye alakarsa da wannan mu’jiza ta Manzon Allah a Makka?  Ina alakar wannan hoto da hukumar NASA?  Shin da gaske ne masu binciken Sararin Samaniya a Kumbon Apollo 11 ne suka dauko wannan hoto?  In har da gaske su ne suka dauko wannan hoto a ziyarar da suka kai, tambaya ta gaba ita ce: ganin cewa tsagewar da Wata yayi mu’jiza ce, ba tsagewa ce irin ta al’ada ba, shin ana iya samun alamar tsagar a jiki har yanzu?  Shin meye tasirin mu’jiza a jikin duk wani abin da mu’jizar ta auku?  Wa ya musulunta sanadiyyar wannan al’amari, kuma me ya kai shi  ga hakan?  Kuma meye bambanci tsakanin “Bayanin Tsarin Kimiyya”, da “Mu’jizar Kimiyya”, da kuma “Mu’jizar Annabawa”?  Wadannan, da ma wasu tambayoyin da ke tafe ne nayi bincike na musamman don kosar da mu kan abin da ya shafi wannan lamari na tsagewar Wata da hoton da ke ta yawo a Intanet – mai kokarin hada alaka a tsakaninsu.  Amma kafin mu shiga bayani kan dukkan wadannan, ga takaitaccen bayani nan kan shi kanshi Watan, da tsarin rayuwarsa.

- Adv -

Halittar Wata:  Daga Ina Haka?

Bayani kan daga ina Wata ya samo asali bai kamata ya dame mu ba, musamman ganin cewa a jerin kasidun da muka gabatar a shekarar da ta gabata, masu taken: “Kimiyyar Kur’ani da ta Zamani: A Ina Aka Hadu?”, mun yi wannan bayani.  Abin da ke da muhimmanci mu sani shi ne, shi Wata, ko Moon a turance, shi ne Tauraron Asali (Natural Satellite) da wannan duniya tamu ta mallaka, kuma yake gewaye ta, tare da halittar rana.  Malaman Sararin Samaniya sun yi hasashe cewa a kalla halittar Wata tayi shekaru biliyan hudu ko sama da haka, tun samuwarta.  Wata kan kare gewaye wannan duniya tamu ne cikin kwanaki ashirin da biyar da rabin rana (25.5days), amma idan aka hada da gibin kwanakin da yake kashewa a halin shawaginsa a falakin rana, sai yayi kwanaki ashirin da tara da rabin kwana (29.5days) yake gama gewaye daya.

Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, wannan duniya tamu ba ta da wani Tauraro na Asali (Natural Satellite) da ya wuce Wata, kuma idan aka kwatanta shi da girman duniyar, kusan shi ne Tauraron Asali da yafi girma a dukkan Taurarin Asali da ke gewaye da sauran duniyoyin da ke makwabtaka damu.  Shi Wata ba shi da hasken da yake kyallarowa na kansa, sai dai ya lakato haske daga rana a yayin da take nata shawagin, idan ta juya mana baya kuma muka shiga dare ko duhu, sai ya hasko mana wannan haske, kamar dai yadda bayanai suka gabata a kasidun baya.  Kamar wannan duniya tamu da sauran duniyoyi ko halittun da ke sama, Wata a cure yake, ko ince a mulmule.  Bangaren da ke fuskanto mu a lokacin da yake shawagi, shi ake kira The Near Side, a turancin Kimiyyar Sararin Samaniya.  Wannan bangare ne ke darsano hasken rana don haskaka duniyarmu, kuma an kiyasta cewa darajar zafin da ke wannan bangare ya wuce digiri dari da talatin da bakwai a ma’aunin zafi na santigireti (wato 1370C).  Dayan bangaren da ke shiga duhu kuma daga baya, shi ake kira The Far Side.  Amma kuma sabanin bangaren farko, wannan bangare bai da zafi sai sanyi mai tsanani.  An kiyasta sanyin wannan bangare na Wata cewa ya kai dari da hamsin da shida a kasa da mizanin zafi (wato -1560C). 

Binciken baya-bayan nan da aka yi ya tabbatar da cewa halittar Wata na dauke ne da duwatsu nau’uka dabam-daban, da sinadaran kimiyya masu inganci irin wadanda ba mu dasu a wannan duniya tamu.  Kari a kan haka, jikin Wata, inji masu wannan bincike, kamar gilashi yake wajen mu’amala da haske; duk ta inda ka cillo haske, zai dauka, ya kuma cilla hasken zuwa inda yake fuskanta.  Kamar dai yadda gilashi ke yi idan ka cilla masa haske.  Wannan tasa idan rana ta cillo haskenta, sai Wata ya dauka, ya kuma cillo hasken zuwa wannan duniya tamu, kasancewar shi ne tauraron mu.  Allah Buwayi gagara misali!   Ba nan aka tsaya ba, babu iska balle guguwa a duniyar Wata.  Wannan tasa duk inda ka taka a saman Wata, gurabun sawunka zasu ci gaba da kasancewa a wurin, tsawon zamani.  Har zuwa yau akwai gurabun takun wadanda suka ziyarci duniyar Wata tun shekarar 1969 a Kumbon Apollo 11. 

A karshe, akwai buraguzan taurarin da rayuwarsu ta kare (wato Meteorite) masu shawagi a saman Sararin Samaniya, wadanda kuma ke shigowa wannan duniya tamu lokaci-lokaci.  Ire-iren wadannan buraguzai ne ke afkawa cikin Wata a lokuta dabam-daban, iya gwargwadon girmansu.  Don haka Malaman Kimiyyar Sararin Samaniya suka ce galibin ramuka da tsagan da ke jikin Wata sun samo asali ne sanadiyyar illolin da wadannan buraguzai masu shawagi a can sama ke yi a saman Wata.  Wannan shi ne dan abin da zai samu na bayanai kan yanayin da Wata ke rayuwa a ciki.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.