Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya: Wa Ke Samar Da Tunani? (5)

Ga kashi na biyar kan binciken da muke yi wajen kokarin fahimtar bangaren dake samar da tunani, tsakanin kwakwalwar dan adam da kuma zuciyarsa. A sha karatu lafiya.

738

Mahangar Musulunci Kan Asalin Tunani

A yau cikin yardar Allah ga mu dauke da bayani kan mahangar Musulunci dangane da abin da ya shafi tunani; shin, daga zuci yake samuwa ko daga kwakwalwa?  A mukaddimar da muka gabatar kan nau’ukan ra’ayoyi dangane da haka, mun fahimci cewa, ta la’akari da ayoyin Kur’ani da wasu hadisai na Manzon Allah (tsira da aimincin Allah su kara tabbata a gare shi), tunani na samuwa ne daga zuci, sabanin abin da malaman kimiyya suke tabbatarwa a yanzu.  Amfanin wannan kasida ta yau shi ne tabbatar da hakan ta hanyar kawo nassoshin Kur’ani masu Magana kan hakan, da na hadisai.  Domin su ne bayanan da shakku ko kokwanto ba ya shiga cikinsu, saboda tabbacin da ke tattare da asalinsu.  Kuma tunda mai zancen shi ne ya halicci dan adam wanda muke Magana kan tsarin halittarsa, ashe kuwa babu wanda zai fahimtar damu gaskiyar abin da ya dangance shi sai Mahaliccinsa.

Bayan haka, za mu ji mahangar Malaman musulunci kan ma’anonin da suke baiwa wadannan ayoyi ko hadisai dangane da abin da muke nema na ma’ana a tare dasu.

Kalmar “Zuciya” a Nassin Kur’ani

Daga cikin gabobi ko sassan jikin dan adam, babu bangaren da Allah ya ambace shi karara, da sunaye daban-daban irin zuciyar dan adam.  Wannan a fili yake ga duk makarancin Kur’ani, masani. Shahararriyar kalma ita ce wacce a asali take nufin Kalmar zuciya karara, a harshen Larabci.  Wannan kalma ita ce: Al-Qalbu.  Allah ya kawo ta a sigar tilo, wato Al-Qalbu, ya kuma kawo ta a sigar jam’i, wato Al-Quloob.  Wannan ita ce Kalmar da tafi shahara cikin kalmomin da aka yi amfani da su wajen ambaton zuciyar dan adam; musulmi ne ko kafiri, Annabi ne ko wani gama-garin mutum.

Kalma ta biyu da Allah yayi amfani da ita don nufin zuciya ita ce kalmar: Al-Fu’aad.  Ita ma ta zo a sigar tilo, wato Al-Fu’aad, sannan ta zo a sigar jam’i, wato Al-Af’idah.  Wannan kalma ita ma ta dan shahara a cikin Kur’ani. Sai kalma ta uku, wato kalmar As-Sadr.  Kamar sauran kalmomin da suka gabace ta, ta zo a sigar tilo da jam’i ita ma.  Wato ko dai ta zo a As-Sadr, ko kuma ka ga tazo da suna As-Sudoor, wato jam’in Sadr kenan.  Asalin ma’anar Sadr na nufin “kirji” ne a harshen Larabci.  Amma saboda alakar da ke tsakanin kirji da zuciya, dangane da abin da Allah ke son tabbatar mana don mu fahimta a aya, shi yasa duk masu tafsiri ke hada alaka tsakaninsa da zuciya, amma sukan fassara kalmar ne da ma’anarta na asali (wato kirji). Domin kirji ne farfajiyar zuciya, kuma ganin cewa duk abin da ke cikin farfajiyar nan yana tasirantuwa da abin da ke ciki, kuma zuciya ce gabar da tafi tasiri cikin gabobin da ke cikin kirji (tun da a wasu ayoyin an ambace ta karara), sai malamai su dauka kai tsaye zuciya ake nufi.  Allah shi ne mafi sanin sirrin da ke cikin ma’anonin kalmominsa.

- Adv -

Wadannan kalmomi, a takaice, su ne ke ishara ga zuciya a cikin Kur’ani.  Sannan sun maimaitu a wurare da dama, wanda hakan ke nuna matukar muhimmancin zuciya ga dan adam wajen fahimta ko rashin fahimtar sakon shiriya da Allah ya aiko Manzonsa da shi.  Kafin mu yi nisa, mu fahimci cewa yawan ambaton abu, a tsarin zance, na nuna lallai akwai wani muhimmanci – na bayyane ko na boye – da wannan abin ya mallaka ko yake yi.

Nau’ukan Zukata da Dabi’unsu

Kafin mu yi bayani kan na’ukan zuciya, yana da kyau mu yi bayani kan dabi’un zuciya.  Da farko dai, zuciya abu ne guda daya, wato dunkulen nama da ke bangaren kirjin dan adam na hagu, wacce ke aikin famfon jini, kamar yadda bayanai suka gabata.  Kuma, kamar yadda Allah ya fada cikin Kur’ani, bai taba halittar wani dan adam da zuciya guda biyu a kijinsa ba.  Wannan sunna ce wacce ya tsara wa kansa, cewa kowane dan adam zuciya daya ake halittarsa da ita.  Daga cikin dabi’un zuci da muka sani a al’adance, akwai ji irin na tausayi, da so, da kauna. Wadannan su ne manyan dabi’un da a al’adance muke danganta su ga zuciya.  Hatta masana fannin kimiyya da wannan suka san zuciya, duk da cewa ko a kimiyyance ba za su iya nuna alamar da ke nuna samuwar soyayya da kauna da suke danganta su gare ta ba (tunda ba abubuwa bane da ake iya ganinsu); sabanin hujjar da suke da ita kan kwakwalwa.

A daya bangagren kuma, Musulunci ya sanar da mu kari a kan wasu halayyar da muka sani dangane da zuciya.  Wadannan sun hada da: imani, da kafirci, da munafunci, da tunani, da fahimta, da rashin fahimta, da karbar gaskiya, da kin gaskiya, da shiriya, da karkata, da sabo, da niyya, da tsarkakuwa, da baci ko dauda, da karamci, da fushi, da rashin damuwa, da tsoro, da damuwa, da bakin ciki, da shakka, da kokwanta, da keta, da tawaye, da nadama, da tabbaci, da rashin tabbaci, da jiji-da-kai, da kishi, da kuma girman kai.  Wadannan su ne yanayi da dabi’un zuciya, kamar yadda nassoshin Kur’ani da hadisai ke nunawa.  Shi yasa suka kasa nau’ukan zukata zuwa kashi biyu; da zuciya lafiyayya ko kubutacciya daga kowane irin cuta, wacce ke dauke da farin ciki, da kwanciyar hankali, da imani, da gaskiya, da mika lamura zuwa ga Allah, da kuma zuciya mara lafiya, wacce ke dauke da cututtuka irinsu kafirci, da bidi’a, da shakka kan sakon Allah, da kokwanto, da girman kai, da zalunci, da yawan sabo, da sauran matsaloli makamantansu.

Wannan rabe-rabe ne da malaman Musulunci suka yi, dangane da bayanan da suka zo cikin ayoyin Kur’ani da hadisan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ingantattu.

Dangane da bayanan da suka gabata, idan muka yi dubi sai mu ga cewa a zahirin lafazi da yanayi, wannan zuciyar da muke dauke da ita a kirjinmu na bukatar karin bayani kan ayyukan da take yi.  Domin abin da muka sani kawai shi ne, tana aikin rarraba jini ne a jikin dan adam, wanda hakan ke taimakawa wajen tabbatar da rayuwarsa.  Wannan ta sa ra’ayoyin malaman musulunci suka sha bamban wajen ma’anar kalmar “Al-Qalbu” ko “Al-Fu’aad” a cikin Kur’ani mai girma.  Shin, akwai wata zuciya ce tattare da asalin zuciyarmu wacce ke gudanar da wadannan ayyuka amma ba a ganinta, ko kuma ita din ce ke dukkan ayyukan, a bisa kudura da ganin damar Ubangiji? Ko kuma dai kawai anyi amfani da kalmar ne don nufin wani abu daban, wato Majaaz kenan?

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.