Tsarin Amfani da Wayar “Blackberry” (1)

Kashi na 16 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

298

Tsarin Amfani da Waya Nau’in Blackberry

Daga cikin wayoyin salula na zamani masu tashe a yau, akwai wayoyi nau’in Blackberry da ake amfani da su.  Wayoyin salula nau’in Blackberry suna kan yaduwa a duniya a halin yanzu.  Kuma duk da cewa wayoyi ne na alfarma, kuma masu tsada da ba kowa bane ke iya mallakarsu, shafin Kimiyya da Kere-kere ya ga dacewar gabatar da ‘yan takaitattun bayanai ga masu karatu don fahimtar yadda tsari da kintsinsu yake.  Har wa yau, na tabbata da yawa cikinmu mun samu labarin cewa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates) ta toshe wasu daga cikin hanyoyin amfani da wannan waya mai matukar tasiri sanadiyyar wasu dalilai.

To me ya kawo haka?  Kuma wani irin tsari ne wannan nau’in wayar salula ke da shi da har zai sa wata kasa ta dauki mataki makamancin wannan?  Duk wadannan na cikin abubuwan da za mu karanta cikin wannan mako da makon da ke tafe in Allah Ya yarda.  Da farko dai, ga bayani nan kan ma’ana da samuwar wannan waya ta Blackberry.

Ma’ana da Asali

Kalmar Blackberry, a turancin Kimiyyar Sadarwa ta Zamani a yau, na ishara ne zuwa ga wani jerin wayoyin salula na musamman nau’in Smartphone, masu dauke da  masarrafar Imel da kamfanin Research in Motion (RIM) na kasar Kanada yake kerawa.  Wannan waya ta Blackberry na dauke ne da masarrafai na musamman da ake amfani da su ta hanyoyi na musamman, kuma a wani irin yanayi da ya sha bamban da sauran hanyoyin sadarwa.  Wasu cikin wadannan masarrafai dai sun hada da masarrafar Imel mai zaman kanta, wato Mobile E-mail, da manhajar kalanda, da masarrafar taskance bayanai, da masarrafar allon rubutu na kamfanin Microsoft – irinsu Microsoft Word, da Excel – da taskar adireshi, da manhajar mu’amala da tsarin sadarwa ta wayar iska, wato Wireless Frequency Radio (Wi-Fi), da masarrafar sauraro da shan kida, da rariyoyin saduwa da Dandalin Facebook, da MySpace, da na Twitter. 

Har wa yau akwai masarrafar gano bigire, wato Geographical Positioning System (GPS), da manyan ka’idojin da ke tafiyar da manhajar Imel: Post Office Protocol (POP) da Internet Message Application Protocol (IMAP), sai kuma manhajar hirar ga-ni-ga-ka, wato Instant Chat Messenger, mai taimakawa wajen gudanar da hira tsakanin mai wayar da duk wanda ke giza-gizan sadarwa ta duniya, irinsu Yahoo Messenger, da Windows Live Messenger, da ICQ, da Google Live Talk da dai sauransu.

Wannan waya ta musamman mai suna Blackberry, kamfanin Research in Motion da ke kasar Kanada ne ya fara kera su cikin shekarar 1999.  Zubin farko da kamfanin ya fara kerawa dai su ne nau’in Blackberry Pearl, kuma shafukansu launin fari da baki ne, babu wasu kaloli daban, wato Monochrome kenan.  Cikin shekarar 2002 ne ya fara kera na zamani masu dauke da manhajoji masu kayatarwa.  Kuma a haka kamfanin yake tafiya har zuwa yau; inda yake ta kera wasu nau’ukan daban masu dauke da abubuwa da dama. A kididdigar da masana kuma masu lura da tsari da tasirin tsarin sadarwa ta wayar salula a duniya suka bayar, bayan wayoyin salula masu dauke da manhajar Symbian OS da kamfanin Nokia ke kerawa, babu wata wayar salula da ta fi samun kasuwa a duniya irin Blackberry.

Manufa

Sabanin sauran wayoyin salula wadanda tun asali an kera su ne don aiwatar da sadarwar murya musamman (Voice Communication), su wayoyin salula nau’in Blackberry an samar ko kera su ne musamman don sawwake ayyukan ofis, da kamfanoni, da kuma mu’amala da fasahar Intanet dare da rana safe da yamma.  Wannan kuwa a fili yake, musamman idan mai karatu yayi la’akari da irin manhajoji da kuma masarrafan da wayar ke dauke da su.

Idan kana dauke da waya nau’in Blackberry, wacce ke hade babu kwange tare da ita, to sadarwa a gare ka ba wata matsala bace.  A kowane lokaci tana jone ne ta giza-gizan sadarwa ta duniya, wato Intanet.  Kana iya karba da aika sakonnin Imel a duk sa’adda ka ga dama.  Kana iya hira da duk wanda kake so a duniya muddin a jone yake da Intanet. Kai a takaice ma dai, kana iya tafiyar da ayyukan kamfaninka ko hukumar da kake wa aiki a duk inda kake. Da wannan nau’in wayar salula, ana gudanar da harkar kasuwanci, da shugabanci, da siyasa, da addini, da duk abin da ya shafi zamantakewa.  Kana zaune a gidanka ne, ko a cikin jirgi kake, ko a cikin mota, ko kwance kake, ko a kasuwa kake, ko a maraya kake, ko kuma a karkara; duk ba ka da matsala.

Bayan haka, wannan waya ce da idan ka caja batirinta, kana iya kwanaki masu tsawo baka bukaci na’urar caji ba.  Domin dukkan manhajojin da ke cikinta ba su cin makamashi fiye da kima, balle har kuzarin batirinka ya gaza nan take.  A halin yanzu wannan waya na sahun kayayyakin sadarwa na tafi-da-gidanka masu canza tsarin rayuwa a duniya, wato Convergent Devices.

- Adv -

Babbar Manhaja

Kamar yadda masu karatu suka sha karantawa a wannan shafi, kowace wayar salula na dauke ne da bangarori guda biyu; da bangaren gangar jiki, da kuma ruhi.  Bangaren ruhi ne muke wa lakabi da “manhaja”.  Domin manhajar ce ke tafiyar da wayar; daga kunnawa har zuwa kashewa – idan babu manhaja a tare da ita, to gwamma a jefar a bola, watakila yara su tsinta su rika wasa da ita.  To, wayoyin salula nau’in Blackberry na dauke ne da babbar manhaja (wato Operating System) mai suna Blackberry OS 6.0.  Wannan shi ne zubin manhajar na zamani. Wannan babbar manhaja tana da kuzari matuka, kuma idan kana da Blackberry tsohuwar yayi wacce ke dauke da babbar manhajar baya, kana iya kara mata kuzari (wato Software Update) ta hanyar zuwa shafin kamfanin ta Intanet daga wayar, ko kuma ka yi amfani da manhajar shigar da masarrafai ta kwamfuta, wato Blackberry Desktop Manager wajen yin hakan.

Bayan babbar manhaja, kowace wayar salula nau’in Blackberry na gudanuwa ne a saman masarrafar tafiyar da ruhin waya nau’in ARM.  Nau’in Blackberry na farko sun yi amfani ne da Intel-80386.  Daga baya kuma sa’adda kamfanin ya tashi kera Blackberry zubin 8000 Series, sai yayi amfani da nau’in ARM XScale 624MHz, in ka kebe zubin Blackberry 8707 wacce aka dora ta a saman nau’in Qualcomm 3250.  Wannan mizani ne na tsarin sadarwa mai taimaka wa injin kwamfuta ko wayar salula sauri da gaugawar karba da aiwatar da umarnin da aka ba ta, kuma shi ake kira Processor a turancin kimiyyar sadarwar kwamfuta.

Tsarin Amfani da Wayar Blackberry

Ana iya amfani da wayar Blackberry ta hanyoyi uku.  Hanyar farko ita ce, ka sayi wayar a kasuwa, ka sanya katin SIM dinka a ciki, sai kawai ka ci gaba da amfani da ita kamar sauran wayoyi.   A wannan tsari, za ka iya yin kira, kuma a kira ka; ka yi tes, kuma a aiko maka.  A takaice dai, za ka rika amfani da tsarin sadarwar kamfanin da ka sanya katinsu.  Amma ba za ka iya amfana da galibin masarrafai da manhajojin da wayar ke dauke da su ba.  Hanya ta biyu kuma kana iya saya, ko kaje daya daga cikin kamfanonin waya da muke da su a Nijeriya ka saya (kowanne cikin kamfanonin waya da muke da su a kasar nan suna sayar da wannan waya), sannan ka bukaci su farkar maka da ita, wato Activation kenan.  Kowace waya nau’in Blackberry na zuwa ne da kalmomin iznin shiga (Pin Cord) guda takwas, kuma da su ake amfani wajen gabatar da abubuwa da dama a wayar.  Kamfanin zai bukaci wadannan kalmomi a gidan yanar sadarwarsa, ko kuma a lokacin da kaje, don su shigar da wayarka cikin babbar manhajar sadarwarsu, kafin ka fara amfana da tsarin Intanet da na Imel da wayar ke dauke da su. Wannan tsari na biyu shi ake kira Blackberry Internet Service (BIS). 

Kamfanonin wayar kasar nan na da wannan tsari, kuma idan ka shiga, a kullum za ka iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar, da manhajar Imel, da kuma hanyar hirar ga-ni-ga-ka.  Duk lokacin da ka samu sako a akwatin Imel dinka, nan take wayar za ta sanar da kai cewa sakon Imel ya shigo; kamar dai yadda wayarka ke sanar da kai idan ka samu sakon tes.  Sai dai kuma, dangane da tsarin biya da ke tsakaninka da kamfanin, duk wata za ka rika biyan kudin hanya, ko dai kafin wata ya kama, ko kuma bayan ya kare.  In kuwa ba haka ba, to ba ka da sabis.

Sai tsari na uku, wanda kamfanoni ne ke amfani da shi, kuma ya kunshi jona wayar da wata manhaja ta musamman mai suna Blackberry Enterprise Server (wato BES).  Wannan manhaja za a sanya ta ne cikin kwamfuta ta musamman a ofishin kamfanin, sannan a hada ta da tauraron dan Adam, wanda zai rika aiwatar da sadarwa ta wayar iska tsakaninsa da dukkan ma’aikacin kamfanin da ke dauke da wayar, da Cibiyar Bayanai (Network Operations Center – NOC) da ke kamfanin Research in Motion a can kasar Kanada, da kuma kamfanin sadarwar da wayoyin ke amfani da katin SIM dinsa. Wannan tsari yana da tsada sosai, amma ba abin da ya fi shi kayatarwa wajen sadarwa.  Shi ma, kamar tsarin da ya gabace shi, dukkan kamfanonin sadarwar wayar salula da ke kasar nan na iya aiwatar da shi.  Bari mu dan kara bayani kan yadda wannan tsari na BES ke gudanuwa.

Mu kaddara Malam Jatau na da kamfani mai dauke da ma’aikata 30, kuma yana son a dukkan lokuta kowane ma’aikaci na bakin aikinsa; a gida yake, ko ofis, a gari yake, ko a halin tafiya. Sai ya je kamfanin MTN misali (kamfanin Zain da Etisalat da Glo ku yi hakuri, misali nake bayarwa) ya bukaci wannan tsari.  Kamfanin MTN zai baiwa kowane ma’aikaci wayar Blackberry ne guda daya, mai dauke da katin SIM din kamfanin, wanda kuma aka jona shi da babbar cibiyar sadarwar kamfanin. Sannan sai ya je inda ofishin kamfanin Malam Jatau yake, don sanya wannan manhaja ta Blackberry Enterprise Server a Uwar Garken (Network Server) da ke ofishin.  Sannan ya jona dukkan na’urorin da za su hada alaka a tsakanin babbar cibiyar sadarwarsa ta waya, da wayyoin salular da ya baiwa wadancan ma’aikata, da kuma babbar cibiyar taskance bayanai ta kamfanin Research in Motion da ke can kasar Kanada.  Da zarar yayi haka, an gama komai.

Da wannan tsari, kowanne cikin ma’aikatan nan zai iya aiko sakon Imel cikin gaugawa zuwa ofis, don sanar da ofis halin da yake ciki kan aikin da aka tura shi.  Haka za a iya aika masa da sakon Imel ta gaugawa.  Haka za a iya hira da shi a tsarin hirar ga-ni-ga-ka, wato Intstant Messenger.  Idan kamfanin ya bayar da lambar wayarsa ne ga masu hulda da kamfanin, to duk sa’adda suka aiko sakon tes, ko na Imel, kai tsaye zai wuce zuwa wayarsa, inda wayar za ta sanar da shi cewa sako ya iso.  Idan yana bukatar karantawa, ba ya bukatar sai ya bude wayar; akwai alamar da aka tanada masa a jikin wayar wacce zai matsa, sai kawai sakon ya budo.

Dukkan sakonnin bayanai – irinsu tes, da Imel, da rubutattun sakonnin hirar ga-ni-ga-ka – suna bin hanyoyi uku ne ko hudu, kafin su isa inda aka aike su, a wannan tsari na BES.  Idan aka aika wa wani ma’aikaci sakon Imel misali, sakon za ta zarce ne kai tsaye zuwa cikin wannan babbar manhaja ta BES da ke kamfanin, wacce a dakace take tana jiran sakonni masu shigowa.  Da zarar ta kalli sakon da ya shigo, sai ta cilla wa wancan babbar cibiyar bayanai na kamfanin Research in Motion da ke kasar Kanada.

Wancan cibiya da ke kasar Kanada kuma sai ta cilla wa cibiyar sadarwar kamfanin MTN, wacce mai’aikacin ke dauke da katin SIM din kamfaninta.  Da zarar sakon ya iso kamfanin MTN, sai ita kuma ta aika wa ma’aikacin cikin wayarsa.  Duk wannan zai faru ne cikin kankanin lokaci, sanadiyyar tasirin kayayyaki da hanyoyin sadarwa ta wayar iska.  Sakon na shigowa wayar za ta sanar da shi nan take. Wannan shi ne yadda ake gudanar da sadarwa a tsakanin manhajar BES da kuma wayar Blackberry.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.