Tsarin Amfani da Wayar “Blackberry” (2)

Kashi na 17 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

311

Zubin Wayoyin Blackberry

Akwai wayoyin Blackberry da dama da aka kera su a yanayi da kintsi daban-daban.  Kashin farko su ne wadanda aka kera cikin shekarar 1999, wadanda kuma galibinsu  duk ba su da wasu launukan da suka wuce fari da baki (wato monochrome, ko kuma black and white).  Daga shekarar 2006 zuwa 2008 sai kamfanin ya samar da zubin da yayi wa lakabi da Blackberry Pearls.  Kafin shekarar 2008 ta kare, sai kamfanin ya samar da wasu zubin masu suna Blackberry Curve, kuma irinsu yayi ta kerawa har sai da shekarar 2009 ta kare.  A karshen shekarar kuma sai ya kirkiri zubin Blackberry Storm, wadanda yayi ta kerawa har cikin shekarar 2010.

Daga farkon shekarar 2010 kuma zuwa tsakiyar shekarar, kamfanin Research in Motion ya sake kera wasu nau’uka da sake sanya musu sunan Blackberry pearls, da Blackberry Curve.  Dukkan wadannan zube-zube na nau’in Blackberry suna dauke ne da adadin 7000, da 8000, da kuma 9000 series, kamar yadda ake kiransu a jumlace.  Wayar Blackberry ta baya-bayan nan da kamfanin ya kera ita ce nau’in Blackberry 9300. 

Wayoyin Salula Masu Kama da Blackberry

Akwai wasu cikin wayoyin salula na zamani da aka kera su dauke da masarrafar Imel ta musamman da wayar Blackberry ke dauke da ita, wato Blackberry Email Client.  Wannan ke sa su sifatu da wata dabi’a ko yanayi irin na Blackberry, to amma fa, kama da wane ba ta wane, ko kadan.  Zan so mai karatu ya samu sunayensu, domin idan mun kasa mallakar wayar Blackberry, to mu san cewa akwai wasu nau’uka da za mu iya mallaka don huce fushin rashinta.  Tabbas Blackberry waya ce abin alfahari da morewa, to amma Allah bai yi yatsun hannayenmu iri daya, balle zanen da ke tafukan hannunmu su dace.

Wayoyin salula masu dauke da masarrafar Imel irin na Blackberry dai su ne: AT&T Tilt, da HTC Advantage X7500, da HTC TyTN, da Motorola MPx220, da Nokia 6810, da 6820, da 9300, da 9300i, da kuma 9500.  Cikin jerin wayoyin har wa yau akwai dukkan ayarin wayoyin Nokia zubin E-series (ban da E71 da E66), sai kuma Qtek 9100, da Qtek 9000, da Samsung E719, da Siemens SK65, da SonyEricsson P910, da P99, da M600i, da kuma P1.  Wadannan, a halin yanzu, su ne nau’ukan wayoyin salula masu dauke da masarrafar Imel na wayar Blackberry, wato Blackberry Email Client.  Ba mu san abin da gobe zai haifar ba.

Tasirin Amfani da Blackberry a Duniya

- Adv -

Ko shakka babu amfani da wayar salula nau’in Blackberry yana tasiri sosai wajen aiwatar da sadarwa a yanayi kayatacce kuma mai gamsarwa.  Musamman ganin cewa kamfanoni da hukumomi da daidaikun mutane sun rajja’a wajen amfani da wannan waya.  Dalilan hakan dai ba nesa suke ba. Da farko, bayan yawaitan hanyoyi da manhajoji ko masarrafan sadarwa da wayar ke dauke da su, akwai kuma ingancin tsaro wajen sadarwa, wanda shi ne abin da galibin kamfanoni ke bukata.

A tsarin aikawa da sakonni ta Blackberry, da zarar ka rubuta sako ka aika, nan take za a narkar da sakon don kariya, har sai ya isa inda aka aike shi.  Wannan ta sa wasu kasashe a Gabas ta Tsakiya suka fara damuwa da wannan tsari na boyewa tare da narkar da bayanai ta yadda babu na’ura mai iya hangowa balle ta karance su yadda za a fahimci sakon da ke cikinsu.  Daga sakon tes, zuwa Imel, har rubutattun sakonnin hira da na murya, duk narkar da su ake yi har sai sun isa inda aka aike su.

Wani abin da ya kara wa wannan tsari wuyan sha’awi ga hukumomi masu son tace bayanai na murya ko rubutattu da ake aikawa a tsakanin kayayyakin sadarwa kuma shi ne, dukkan sakonnin da ake aikawa sai sun dire a Uwar Garken kamfanin da ya kera wayar a can kasar Kanada, sannan su isa muhallin da ake jiran isansu.  Shi yasa a ranar 1 ga Augusta kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates) ta toshe kafar amfani da tsarin Intanet da Imel da rubutattun hira ta hanyar wayar Blackberry, saboda dalilai na tsaro.  A kasar hukuma ta saba tace ire-iren wadannan bayanai daga wayoyin salular da ake amfani da su, don tsaron lafiyar jama’a da ma baki da ke shigi-da-fici a kasar a kullum.

To amma saboda tsananin tsaro da wannan waya ta Blackberry ta sifatu da shi, sun kasa samun isa ga ire-iren wadannan bayanai da mutane ke aikawa ta wannan waya.  Don haka suka toshe dukkan kafar Intanet da duk wani mai Blackberry zai iya bi ya aika da sako.  A halin yanzu idan kana Dubai, sai dai ka kira, ko ka yi tes, amma batun Imel da Intanet kam sai dai ka hakura.  Hukuma tace muddin kamfanin bai yi wani hobbasa ba wajen ganin ya warware wannan matsala kafin 11 ga watan Oktoba, to za ta toshe hanyar amfani da wayar ma gaba daya.  A halin yanzu akwai wayar salula nau’in Blackberry guda 500,000 da ake amfani da su a kasar.

A kasar Saudiyya ma hukuma ta koka da wannan tsari na mu’amala da wayar Blackberry.  Don haka ita ma, daidai lokacin da ake wancan dambarwa a Hadaddiyar Daular Larabawa, ta yi barazanar cewa za ta toshe kafar sadarwar Intanet ga duk mai wannan waya, muddin kamfanin Research in Motion bai yi wani abu ba wajen ganin hukuma ta samu kai wa ga ire-iren bayanan da take so ko ake aikawa.  Ai nan take sai kamfanin ya fara shirye-shiryen ganin ya amsa wannan kira.  Domin akwai wayoyin Blackberry wajen 700,000 da ake amfani da su a kasar.

Ya zuwa yanzu, kamfanin ya fara tattaunawa da hukumar Saudiyya, inda yayi tayin sanya wata Uwar Garke (Network Server) da dukkan sakonnin da masu wayar ke aikawa za su rika bi, gwamnati na tace su, kafin su zarce zuwa ga wadanda aka aika musu su, a kasar suke ko a wajen kasar. Domin kasar Saudiyya da ma galibin kasashen Larabawa duk suna tace tsarin sadarwa da ake gudanarwa ta hanyoyin kayayyakin sadarwa irinsu kwamfuta da wayoyin salula da sauransu.

Bayan kasar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, kasar Indonesiya, da kasar Bahrain, da kasar Indiya, da kasar Aljeriya da kuma kasar Lebanon, duk sun fara tayar da kura kan wannan tsari na rashin iya tace bayanan da wannan waya ta Blackberry ke aikawa, kuma akwai hasashen cewa su ma suna iya cew sai an musu irin abin da ake son yi wa kasar Saudiyya, in kuwa bah aka ba, to duk wani mai wayar Blackberry ya jefar da ita a bola.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.