Tsarin Amfani da Wayar Salula (4)

Kashi na 29 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

314

Mu’amala da Fasahar Bluetooth

Daga cikin nau’ukan hanyoyin sadar da bayanai ta wayar salula masu matukar tasiri, akwai fasahar sadarwa ta Bluetooth.  Kusan duk mai amfani da wayar salula a Najeriya yanzu ya san fasahar Bluetooth, ko da a baki ne.  Kuma duk da cewa muna yawan amfani da wannan fasaha wajen aika sakonni musamman lambobin waya da sauti da kuma bidiyo, kadan daga cikinmu ne suka san asalin wannan fasaha da tsarin mu’amala da ita. A shekarun baya mun gabatar da kasidu guda biyu kan fasahar Bluetooth, a yau ma ga mu dauke da takaitattun bayanai kan fasahar, da tsarin amfani ita.

A kimiyyance dai, idan aka ce “Bluetooth”, musamman ma a wannan zamani namu, ana nufin wani tsari ne ko fasahar sadarwa da ke kunshe cikin kayayyakin sadarwa na zamani irin su wayar salula da sauran na’urorin sauraren wakoki da sarrafa bayanai (kamar iPod, da iPad), wanda ake iya aikawa ko karban jakunkunan bayanai da suka shafi haruffa da sauti da murya (irin na wakoki da karatuttuka da laccoci) ko hotuna; masu motsi (Video) ko daskararru, a tsakanin wadannan kayayyakin sadarwa.  Wannan ita ce ma’anar “Bluetooth” a fayyace.  Sadarwa a tsarin Bluetooth na yiwuwa ne ta hanyar neman wayar salular wanda kake son aika masa, a iya tazaran da bai wuce taku talatin ba (30ft), ko kuma nisan mita goma (10 meters).  A iya wannan tazara, idan ka kunna fasahar Bluetooth din ka, to duk wanda nasa ke kunne a iya kadadar wannan tazara ko zango, za ka same shi da zarar ka nemo, har kuma ka iya aika masa da sako.

Wannan fasahar sadarwa ta samo asali ne shekaru kusan 13 da suka gabata, lokacin da wasu kamfanonin kayayyakin fasahar sadarwa guda biyar suka kafa wata kungiya na masu sha’awar ci gaban yadawa da kuma sawwake hanyar sadarwa a tsakanin kayayyakin sadarwa, mai suna Special Interest Group, ko SIG a takaice.  Sun yi haka ne cikin shekarar 1998.  Kuma a karshen shekarar 1999 ne suka cin ma matsaya kan wannan fasahar sadarwa, inda suka zabi sunan wani sarki da yayi zamani a karni na goma a nahiyar Turai mai suna Harold Bluetooth, suka ba wannan sabuwar hanyar sadarwa da suka kirkira.  To me ye dalilin zaban sunan wannan sarki?

Shi dai Sarki Harold Bluetooth, wani basarake ne da yayi rawan gani a tsakanin kasashen Turai wajen iya sasanta kasashe lokacin yaki.  Rawan ganinsa na karshe shi ne wanda ya taka wajen sasanta kasar Norway da Sweden bayan sun dauki tsawon shekaru suna gwabza yaki a tsakaninsu.  Ta la’akari da tsarin hada alaka wajen karba da mika bayanai a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa, wanda kuma shi ne aikin wannan sabuwar fasaha da kungiyar ta kirkira, sai ta zabi kiran wannan sabuwar fasahar sadarwa da sunan wannan sarki.

Babbar ka’idar da ke lura da wannan sadarwa, a kimiyyance ita ce ka’ida ta 802.15.1, wacce Cibiyar Injiniyoyin Lantarki ta kasar Amurka, wato IEEE (Institute of Electrical and Electronics Engineers) ta kirkira cikin shekarar 1994.  Wannan Cibiya ita ke da alhakin tsarawa da kuma kirkiran ka’idojin sadarwa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa na tafi-da-gidan ka (Mobile Devices) masu amfani da tsarin sadarwar wayar-iska, wato Wireless Communication, a duk duniya. Fasahar sadarwa ta Bluetooth ta shahara sosai a duniya, kuma babban dalili shi ne kasancewarta a jikin wayoyin salula.

Kamar yadda bayani ya gabata a sama, wannan fasahar sadarwa an kirkiro ta ne cikin shekarar 1998, aka kuma lakkaba mata sunan wannan sarki a karshen shekarar 1999. Daga nan aka fara kiran wannan kungiya ta kamfanonin sadarwa da sunan Bluetooth Special Interest Group (Bluetooth SIG), wato kungiyar masu kebantacciyar sha’awar bunkasa fasahar Bluetooth.  Mambobinta na asali guda biyar ne, amma kafin karshen 1999, sun kai 400.  A farkon shekarar 2000 sai aka fitar da nau’in farko na wannan fasahar sadarwa, wato Bluetooth v1.0, wanda aka fara shigarwa cikin wayoyin salula a shekarar 2001.  Cikin wannan shekara ne kuma aka shigar da fasahar cikin beran kwamfuta, wato Computer Mouse, da kwamfutar tafi-da-gidanka, wato Laptop, da hanyar shigar da bayanai na tsarin Universal Serial Bus (ko USB Port).  Wannan shekara ta 2001 bata karkare ba sai da aka kirkiri rediyon kunne, wato Headset mai dauke da wannan fasaha ta Bluetooth.

- Adv -

Ana shiga shekarar 2002, sai ga na’urar buga bayanai ta kwamfuta, wato Computer Printer, mai dauke da fasahar Bluetooth, da kuma na’urar daukan hoto ta zamani, wato Digital Camera, ita ma dauke da wannan na’ura.  A wannan shekara ne har wa yau, aka kaddamar da wannan kungiya ta Bluetooth SIG.  Da aka shiga shekarar 2003, ai sai zamani ya ci gaba da bin fasahar Bluetooth, sau-da-kafa. Sai ga na’urar sauraran wake ta zamani, wato MP3 Player, ita ma dauke da wannan fasaha ta Bluetooth.  A wannan shekarar ne aka fitar da wani sabon nau’in wannan fasaha, wato Bluetooth v1.2.  A karshen shekara, sai aka lura cewa a duk mako, akan fitar da kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da wannan fasaha a kalla miliyan daya.  Wannan ya nuna tsananin tasirin wannan fasaha da karbuwan da ta samu.

Da aka shigo sabuwar shekarar 2004, sai kungiyar Bluetooth SIG ta fitar da sabon nau’i mai taken Bluetooth v2.0, wanda ingancinsa wajen sadarwa ya dara nau’ukan baya.  A wannan shekara ne aka tabbatar da cewa akwai a kalla kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da wannan fasaha ta Bluetooth sama da miliyan 250, kuma a duk mako a kalla akan fitar da sababbin kayayyakin fasahar sadarwa dauke da Bluetooth, sama da miliyan uku.  Kafin shekarar ta kare kuma, aka kirkiri rediyon kunne irin na zamani, wato Stereo Headphones, su ma dauke da wannan fasaha ta sadarwa. Da shekarar 2005 ta kunno kai sai aka samu kari wajen yawan kayayyakin fasahar sadarwa da ake kerawa da fitarwa a duk mako, daga miliyan uku a shekarar 2004, zuwa miliyan biyar.

A wannan shekara ne yawan kamfanonin sadarwa da ke kungiyar Bluetooth SIG ya cika dubu hudu, daga dari hudu da ake dasu a karshen shekarar 1999.  Har wa yau, cikin wannan shekara ne aka kaddamar da manyan cibiyoyin wannan kungiya ta Bluetooth SIG a manyan birane/kasashe hudu; da Washington, da Malmo, da Sweden, da kuma Hong Kong.  Kafin shekarar ta yi wafati, sai ga kirkirarren gilashin ido, wato Sunglass, shi ma dauke da wannan fasaha ta Bluetooth.  Babban Magana, wai dan sanda ya ga gawar soja!

Da aka shigo shekarar 2006, ai sai ga agogon hannu, shi ma dauke da wannan fasahar sadarwa.  A shekarar ne har wa yau aka tabbatar da cewa akwai kayayyakin fasahar sadarwa a kalla biliyan daya da  ke dauke da wannan fasaha ta Bluetooth, kuma a kalla duk mako ana kerawa da kuma fitar da kayayyakin fasahar sadarwa miliyan goma, masu dauke da wannan fasaha.  Wannan ke dada nuna mana irin karbuwa da kuma habbaka da wannan fasahar sadarwa ke samu kuma take yi a duniya.  A karshe dai, ana shiga shekarar 2007, sai aka kirkiro akwatin talabijin mai dauke da wannan fasaha.  A shekaran ne mambobin wannan kungiya ta Bluetooth SIG suka cika dubu tara, daga dubu hudu da aka samu a shekarar 2005. An kuma tabbatar da cewa a duk mako akan samu a kalla kayayyakin fasahar sadarwa miliyan 800 da ake kerawa ko fitarwa kasuwa, masu dauke da wannan fasaha ta Bluetooth.  Kusan kashi saba’in na wadannan kayayyakin sadarwa, wayoyin salula (Cell phones) ne da kuma na’urar sauraron wakoki irin na kunne, wato Headset.

Cikin wannan shekara ne dai har wa yau, aka fitar da wani sabon nau’i, wanda ya kere nau’ukan baya wajen ingancin sadar da bayanai. Wannan nau’i shi ne Bluetooth V2.1, kuma tsari da kuma kimtsin da aka yi masa na dauke ne cikin wani kundi mai shafuka 1,400 da ‘yan kai.  Kuma zuwa karshen shekarar 2007 ne kungiyar ta kaddamar da mujallarta mai suna SIGnature Magazine, wanda ke fitowa a duk bayan watanni uku.  Ta kuma yi wannan sanarwa ne a babban taronta na shekara-shekara da take yi, wanda aka yi a birnin Vienna, babban birnin kasar Austria.

Akwai ka’idoji masu dama da suka shafi tsarin sadarwa ta Bluetooth, amma guda hudu kawai za mu kawo, don su ne masu siffata mana mafi karancin tsarin da ake bukata kafin hada alaka a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da Bluetooth.  Da farko dai, wannan fasahar sadarwa na amfani ne da tsarin aikawa da sakonni ta siginar rediyo, wato “Radio Frequency Waves” (RFW), wanda a ilimin fasahar aikawa da sakonni ta zamani ake wa lakabi da “Spread Spectrum.” Wannan tsari na “Spread Spectrum” shi ne tsarin da ke aikawa da sakonni ta hanyar nemo siginar rediyon mai alaka da abokin huldansa, daga mafi karancin zango, sai ya yalwata siginar zuwa zango mafi fadi don sawwake hanyar sadarwan.  Wannan tsari na dauke da manyan ka’idoji guda hudu da ke sawwake wannan sadarwa; akwai  “Baseband Protocol” (BP), wato ka’idar da ke haddasa samuwar siginar rediyo (Radio Frequency Waves) don tabbatar da yanayin sadarwa a lokacin da mai son sadarwa ke bukata.  Hakan kuma na faruwa ne daga lokacin da ka kunna na’urar Bluetooth da ke jikin wayar salularka, don nemo abokin hulda da ke da wannan tsari a wayarsa.

Sai ka’ida ta biyu, wato “Link Manager Protocol” (LMP), wadda ke yin aikinta da zarar “Baseband Protocol” ta gama nata aikin.  Shi Link Manager Protocol aikinsa shi ne haifar da sadarwa a tsakanin wayar salula da wata wayar mai dauke da Bluetooth, don tabbatar da tsarin sadarwan.  Wannan ka’ida ce har wa yau ke tabbatar da tsaro ga jakar bayanai da ake son aikawa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwan biyu.  Daga nan kuma sai ka’ida ta gaba, wato “Logical Link Control & Adaptation Protocol” (L2CAP), wacce ke kacalcala bayanan da ake son aikawa daga wayar da ake son aikawa da su, zuwa irin yanayin da suka dace a aika dasu.  Idan masu karatu basu mance ba, wannan aiki shi kwamfuta ke yi a zangon Presentation Layer, kamar yadda bayani ya gabata a kasidar Tsarin Aikawa da Sakonni a Tsakanin Kwamfutoci (2).  Za a kacalcala bayanan ne, don sawwake tsarin aikawa dasu.  Da zarar sun isa masaukinsu a daya bangaren, akwai ka’idar da za ta gyatta su zuwa yanayinsu na asali.  Har wa yau, wannan ka’ida ce ke tabbatar da samun yanayin aikawa da sako mai inganci.

Sai kuma ka’ida ta karshe, wato “Service Discovery Protocol” (SDP), wacce ke zakulo maka dukkan wata wayar salula da ke dauke da fasahar Bluetooth da zarar ka nemo, ta kuma nuna maka sunan da mai wayar ya bata ko kamfanin da ya kirkiri fasahar ya bata.  Wannan ka’ida ce ke hada alakar idan ka zabi wacce kake son aika mata.  Misali idan akwai wayoyin salula guda biyar masu kunne da Bluetooth a yayin da kake neman abokin huldanka, za ka gansu duka, da sunayen su, sai ka zabi wacce kake son hulda da ita.  Idan ka zaba, wannan ka’ida ce ke yi maka barbaran wacce kake nema, kai tsaye.  Wadannan, a takaice, su ne shahararrun ka’idojin aikawa da kuma karban sakonni ta hanyar sadarwa ta Bluetooth, a kimiyyance.  A yanzu ga yadda yanayin ke kasancewa, a zahiri.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.