Waiwaye Kan Darussan Baya (3)

Idan mai karatu bai mance ba, makonni kusan ashirin da suka wuce ne muka zauna don yin Waiwaye Adon Tafiya kashi na biyu.  A yau kuma cikin yardar Allah gashi mun sake dawowa don maimaita irin wannan zama.  Kamar yadda muka sha fada, amfanin wannan zamfa shi ne don yin tsokaci, tare da kallon baya, da halin da ake ciki, da kuma inda za a dosa nan gaba.  A yau ma kamar sauran lokutan baya, mun kasa  wannan kasida zuwa kashi hudu da kuma kammalawa.   A bangaren farko za mu yi bita kan kasidun baya.  Sai kuma bayani kan mahangar da wadannan kasidu suka ginu a kai.  Daga nan sai muyi tsokaci kan wasikun masu karatu.  Ba wai nassin wasikun za mu kawo ba, don kusan duk na amsa su ko.  Sai abu na karshe, wato bayani kan inda muka dosa a zango na gaba.  Sai a biyo mu!

120

Tuna Baya Shi ne Roko

————————————————-

Kasidun Baya

Kamar yadda na sanar a mukaddima, wannan zango ya kunshi makaloli kusan ashirin ne, wadanda aka buga su, daya na bin daya, a wannan shafi na wannan jarida mai albarka.  Kasidar farko ita ce wacce muka aiko kan Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake, wato Cyber Café kenan a turance, inda muka fadi asalin wannan kalma da tarihin yaduwar wannan tsari na kasuwanci da ke tattare da yaduwar fasahar sadarwa.  Sai kuma Nau’ukan Hanyar Sadarwa da ke Intanet, wanda muka kacalcala zuwa kashi hudu. A kashin farko mun kawo mukaddima ne kan dalilan da suka haddasa yaduwar sauran fasahan sadarwa a Intanet.  A kasida ta biyu kuma muka kawo bayanai kan yaduwar fasahar rediyo.

Sai bayani kan talabijin da jarida suka biyo baya a sauran kasidu na uku da na hudu.  Bayan mun karkare da wannan fanni, sai muka shiga bayani kan Tasirin Fasahar Intanet ga Kwakwalwar Dan Adam.  Wannan fanni mun kasa shi kashi biyu ne; a kasidar farko muka yi bayani kan dalilan da ke haddasa samuwar tasiri, mai kyau ne ko akasinsa, a kwakwalwar dan Adam a yayin da yake mu’amala da wannan fasaha.  Kasida ta biyu kuma ta biyo da bayani kan abin da wannan tasiri ke haifarwa, da kuma hanyoyin waraka.  Muna fita daga wannan bigire kuma sai muka tsunduma wani sashe mai muhimmanci, wato Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet.  Shi ma silsila ne na kasidu guda uku.  A kashin farko muka yi bayani kan ma’ana da kuma muhimmancin ka’ida a rayuwa; a aikace ne ko a ilmance. Mun kuma kawo misalai kan haka.  A kasida ta biyu kuma jero ka’idoji guda goma na farko, da dukkan bayanai ko kaidinsu.  Sai muka gabatar da ragowan sha dayan a kasidar da ta biyo baya.  Wadannan ka’idoji goma sha daya da muka kawo, mun yi kanda-garki cewa ba iyakansu ba kenan.  Kowa na iya kirkiran ka’ida a yayin da yake mu’amala da wannan fasaha, kuma kowace ka’ida da kaidinta.

Daga nan sai mai karatu ya fara samun bayanai kan Tsarin Sadarwa a Tsakanin Kwamfutoci, wato Computer Networking.  Wannan fanni shi ma ya samu karkasuwa ne saboda muhimmancin da ke tattare da yin bayani cikin sauki don samun gwargwadon fahimta kan tsarin sadarwar.  A kasidar farko muka kawo ma’ana da nau’ukan alakar da ke tsakanin kwamfuta da ‘yar uwanta wajen sadarwa.  Mun nuna cewa samun cikakkiyar fahimta kan wannan alaka zai yi wahala, don haka muka gabatar da ka’idar Black Box, don rage mana wahalar samun cikakkiyar fahimta.  A kasida ta biyu mai karatu ya samu bayani kan ka’idojin sadarwa a tsakanin kwamfutoci, wato Computer Protocols kenan.  Sai kuma matakan sadarwa, inda muka kawo tsarin OSI, ko kace Open Standard Interconnect Model a turancin kwamfuta kenan.

Bayan wannan sai kasidar Manhaja da Ka’idar Sadarwa ta Imel ta biyo baya.  A kasidar ne muka samu bayanai kan ma’anar Email Client da kuma Email Protocol, wato ka’idojin da kowane sako ke bi kafin ya isa zuwa inda aka aike shi.  Har wa yau, mun kawo bayani kan Mail Server, wato uwar garken da ke dauke da manhajar Imel kenan.  A karshe kuma muka karkare da bayani kan nau’ukan ka’idojin da sakonni ke bi; irinsu POP3, IMAP, SMTP, HTTP da kuma TCP. Da muka fita daga wannan hurumi na Imel, sai muka tsallaka zuwa kasidar Sadarwa ta Wayar Iska, wato Wireless Communication. 

Wannan fanni ya samu karkasuwa shi ma zuwa kashi-kashi.  Mun fara da koro bayani kan bayyana da kuma yaduwar nau’in fasahar sadarwa ta wayar iska, inda muka dauki GSM a matsayin misali.  Mun kawo tarihin bayyana da yaduwa da kuma tasirin wannan fasaha ta sadarwa ta GSM  a wannan kasa tamu Nijeriya.  Mun karkare wannan kashi ne da ka’idar Killer Application, kashin bayan yaduwar wannan hanya da ma sauran nau’ukan fasahan sadarwa a duniya.  Sai muka ci gaba da koro bayani, inda mai karatu ya san irin hanya da kuma yanayin da ake bukata kafin sadarwa ta yiwu tsakanin mutane biyu masu rike da wayoyin salula.  A karshe kuma muka ci gaba da bayani kan na’urorin da ke sawwake wannan saduwa, wanda kowace kamfanin sadarwa (Service Provider) ke dasu a wurare da dama.  Wadannan, a takaice, su ne kasidun da suka gabata cikin wannan zango.  Saura da me?

Yanayi da Mahangar Kasidun Baya

- Adv -

Manufar kawo dukkan wadannan kasidu a wannan zango shi ne don samun fahimta kan ilimin fasaha gaba daya; daga abin da ya shafi ginawa ko kerawa da kuma ka’idojin sadarwa gaba daya.  Sai kuma abin da ya shafi tunani da tasirin mu’amala da mai mu’amalan ke yi dasu.  Wannan na da muhimmanci, domin idan ka san haddin amfanin da ka za ka iya yi da abu, ba za ka wuce haddinka ba.  Har way au, na lura galibin mutane suna sarrafa wadannan kayayyaki ne na fasaha ba tare da la’akarin tasirin kayayyakin ga lafiyar su ba, musamman ma a kasashe masu tasowa.  Don haka na hade shahararrun kayayyakin fasahan da muka yawaita amfai da su; Intanet, Imel, Kwamfuta da kuma Wayar Salula.  A yanzu na tabbata mun san wani abu daga cikin asalinsu, da na’ukansu da kuma tasirunsu ga tunani da kwakwalwa da ma lafiyar dan Adam ta kowane bangare na rayuwa.

Wasikun Masu Karatu

A wannan zango mun samu sakonnin masu karatu kamar sauran zangunan da suka gabata, sai dai basu yawaita ba.  Dalilin hakan kuwa a bayyane yake;  don galibin kasidun, in ma ba duka ba, sun ta’allaka ne ga asali da kuma nu’ukan hanyoyin sadarwar.  A takaice dai ilmummuka ne aka sanar da mai karatu, wadanda yana bukatar su don sanin halin da wani abu yake ciki.  Abin day a shafi aikatawa a ciki basu da yawa. Sabanin zango na biyu da muka samu kasidu kan yadda ake bude Mudawwanar Intanet (Blog) da gina gidan yanar sadarwa da Imel da sauransu.  Kamar yadda aka saba, mun samu sakonni ta hanyoyi uku; sakonnin Imel da na wayar salula, wato Text Messages.  Sai kuma masu bugo waya don gaisawa da nuna gamsuwa da abin da ake karantawa ko gani.  Kamar yadda na sanar a mukaddima, ba wai nassin wasikun za mu kawo ba, sai dai tsokaci, kamar yadda muka yi tsokaci kan kasidun baya.

Dangane da sakonnin text, mun sakon daga Malam Aminu TYT, daga Kano nake tunani.   Sai Malam Auwalu A. Kano, shi ma Bakano ne.  Har wa yau, Malam Auwal Garba Usman (Abu Asma’u), shi ma ya rubuto sako daga Kano.  Cikin wadanda suka rubuto akwai Malam Salihi Malumfashi, sai kuma Malam Kabiru Saleh.  Daidai lokacin da nake kwankwasa kwamfuta don tsara wannan kasida, sai ga sakon Malama Asma’u daga Katsina birnin Dikko.  Duk muna godiya da wadannan sakonni naku.  Allah Ya bar zumunci, amin.  Sai sakonnin Imel, akwai sakon Malam Auwal Azare, wanda ya rubuto yana neman shawara kan Mudawwanar da ya bude wanda ke http://alkalami.blogspot.com.  Akwai Malam Abubakar Rano day a rubuto don neman shawara kan irin kwamfutar da zai saya.  Na aika masa da jawabi tuni.

Daga nan sai ga Malam Rilwan Yusufu Kano da ke son a taimaka masa da bayani kan yadda zai shigar da hotuna cikin Mudawwanar sa.  Shi ma na aika masa da gamsasshen jawabi kan haka.  Sai kuma Malam AbdurRahman M. Abdu da ke neman shawara kan yadda zai bude shafin sad a ke Gumel.com.  Shi ma na aika masa da jawabi.  Wani bawan Allah da na kasa tuna sunansa ya rubuto shi ma, bai ambaci sunansa ba, sai adireshin Imel dinsa: nayankatsare2@yahoo.com.   Shi nashi bukatar kan shiga Intanet ne a wayar salula, kuma na aika masa da rariyar da zai samu cikakken bayani a Mudawwanar mu da ke dauke da dukkan kasidun da muke bugawa (http://fasahar-intanet.blogspot.com).  Sai kuma Malam Umar Suleiman, shi ma ya turo nashi sakon.  Mutum na karshe shi ne wanda ya rubuto yake son a aiko masa da hoton na’uran cajar Fulani, wacce na siffata ta cikin kasidar GSM.  Babban Magana, wai dan Sanda ya ga gawar soja.  Labari ne wani aboki nay a bani, kuma na yarda da abin day a gaya mani don zai iya yiwuwa, shi yasa ma na nakalto mana labarin.  Amma ba ganin hoton cajar nayi ba.  Malam Abdullahi da ke Life Camp, Abuja, ai mana afuwa kan haka.  Duk muna godiya da sakonninku.

A bangaren masu bugo waya kuma bazan iya tuna sunayen duk wadanda suka bugo ba, illa mutum daya, wato Malam Dalhatu H. Bello, jami’I a gidan rediyon Bauchi.  Ya kuma bugo ne don nuna godiya da gamsuwa da kuma neman alfarma kan lokaci idan za su samu, don yin hira dani kan harkan fasahar sadarwa gaba daya.  Wannan, a cewarsa, za su rika sanyawa ne cikin shirin su na Kimiyya da Fasaha da suka bullo dashi ba da dadewa ba.  Wadannan su ne sakonnin da muka samu daga masu karatu, kuma kamar yadda na bayyana a farko, na aika ma kusan dukkan su jawabai kan abin da suke nema.  To bayan duk wadannan kasidu da muka samu a wannan zango, ina muka dosa daga nan?

Zangon Da Ke Tafe

Ina son mai karatu ya dauki wannan shafi ko kasidu da yake samu a wannan jarida mai albarka a matsayin wata makaranta ce da yake ciki a matsayinsa na dalibi ko mai lura da abin da mai karantarwa ke karantarwa, don tunatarwa a lokacin da bukatar hakan ta taso.  Idan ya kasa dukkan biyun, to kada ya kasa zama dan kallo.  In ba haka ba, sai a yi ba shi.  A matsayin aji, wannan shafi zai ci gaba da kwararo kasidu a zangon gaba kan gwanancewa ko kwarewa a wanni fanni cikin fanning ilimin fasahar sadarwa.  Idan mai karatu bai fahimci wannan lugga ba, ina nufin kasidun gaba za su z one kan abin yi a duniyar Intanet.  Za mu kawo fannonin fasaha daban-daban wadanda mai karatu zai iya kwantar da hankalinsa don koya, da iyawa kafin kwarewa a kan su.  Wannan zai taimaka masa gaya wajen amfanar da kansa da lokacinsa da ma dukiyar sa, a yayin da yake mu’amala da wannan fasaha.  Don haka sai a biyo sau da kafa, don samun bayanai kan wadannan hanyoyi na fasaha da za mu kawo.

Kammalawa

Daga karshe, ina mika sakon gaisuwata ga dukkan wadanda suka aiko sakonni ko bugo waya ga wannan shafi ko marubucin shafin, musamman ma wadanda na ambaci sunayensu a sama.  Sannan, gaisuwa ta musamman ga Farfesa Abdallah Uba Adamu da ke Jami’ar Bayero da ke Kano, Malam Magaji Galadima, Dakta Yusuf Adamu, Malam Adamun Adamawa (Dallatun Bebejin Intanet), Shehu Chaji, Muntaka AbdulHadi, Habeeba Haroon, da dai dukkan wani wanda bai ji sunansa ba.   Allah Ya sada mu da dukkan alherinsa, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.