Yadda Aka Fara Hako Danyen Mai

Daya daga cikin masu karatu ya bukaci a sanar dashi yadda ake hako danyen mai daga karkashin kasa ko teku. A wannan mako mun shiga dakin bincike don tabbatar da hakan. A sha karatu lafiya.

286

Mabudin Kunnuwa

A wannan mako cikin yardar Allah za mu tabo wani fanni mai muhimmanci ga rayuwarmu baki daya, musamman kan abin da ya shafi safara, da sarrafa abubuwa, da kuma tafiyar da rayuwa gaba daya.  Wannan fanni kuwa, kamar yadda mai karatu zai gani daga taken kasidar wannan mako, shi ne fannin yadda ake hako danyen mai, wato Crude Oil, ko kuma “Gurbataccen Mai”, kamar yadda wasu ke kiranshi.  Za mu san wani abu kan haka, da yadda ake tace shi, da kuma yadda bayan an tace, ake fitar da sinadaran da rayuwarmu ke gudanuwa da su a yau, wajen tafiye-tafiye, da wanke-wanke, da tande-tande, da kuma samun abin sanyawa a aljihu.  Amma kafin nan, ga yadda wannan kasida ta samo asali nan:

“Assalaamu Alaikum, ni dai a kullum ina sha’awar sanin yadda aka fara sanin danyen mai ne (Crude Oil), da yadda aka gano cewa yana da amfani a duniya, da inda aka fara tonowa, da wadanda suka fara tono shi, da shekarar da aka fara tonowa, da kuma amfanin da aka fara yi da shi.  Na gode.”

Danyen Mai: Ma’ana da Asali

Danyen Mai, ko Crude Oil a harshen Turanci, shi ne garwayayyen ruwan sinadaran da ke makare a karkashin kasa ko duwatsu, wanda ya samo asali daga attakar matattun dabbobin ruwa da na kan tudu da suka rube sanadiyyar tsananin zafi da daskarewa, tun shekaru aru-aru.  Daga daskararren jikin wadannan halittu ne wadannan sinadarai ke canza yanayi da kama, sai su narke sanadiyyar tsananin zafin da ke karkashin kasa da kuma tsawon zamani.  Bayan sun canza yanayi, wannan sabon mai da ya samu daga jikinsu kan kunshi sinadaran kimiyya nau’uka uku.  Nau’in sinadarin kimiyya na farko da ke ciki shi ne sinadarin Faraffin mai dauke da sinadarin hidarokabon.  Nau’i na biyu kuma shi ne sinadarin Naften, shi ma mai dauke da sinadarin hidarokabon a cikinsa.  Sai nau’i na karshe wanda hadaka ne na tagwayen sinadarai – tsakanin sinadarin Aroma da Asfalt.  Wadannan sinadarai da ke samuwa a jikin kowane danyen mai da ake hakowa, su ne suka kawo samuwar rabe-raben nau’ukan danyen mai zuwa kashi uku.

- Adv -

Nau’in danyen mai na farko shi ne nau’in da ke dauke da galibin sinadarin Faraffin mai garwaye da hidarokabon.  Wannan nau’i shi ake kira Paraffinic Crude a Turancin Kimiyyar Man Fetur na zamani. Sai nau’i na biyu da ke dauke da galibin sinadarin Naften mai garwaye da hidarokabon shi ma.  Wannan nau’i shi ake kira Naphthenic Crude.  Kashi na karshe shi ne wanda ake samunsa cakude da tagwayen sinadaran Aroma da Asfalt sama da kashi arba’in (40%).  A turancin Kimiyyar Man Fetur a yau ana kiran irin wannan nau’i da suna Aromatic & Asphaltic Crude.  Bayan wadannan rabe-rabe kuma, a yanzu masana kan kasa danyen mai zuwa kashi biyu, dangane da yanayin da aka debo shi.  Idan yana da kauri, sanadiyyar bunkasar sinadaran da ke cikinsa sama da kashi arba’in da biyar, sai a kira shi “Daskararren Danyen Mai”, ko Heavy Crude, a Turance.  Idan kuma sinadaran da ke dauke cikinsa ba su da armashi ta yadda suka sa ya zama tsala ko tsalalo, sai a kira shi “Narkakken Danyen Mai”, ko kuma Light Crude a turance.

Kamar yadda mai tambaya ke son sani, shi danyen mai a farkon zamani babu wanda ya san shi, balle ya san daga inda ya samo asali.  A takaice dai a iya cewa shi ne ya fara bayyana kansa.  Yadda lamarin ya kasance kuwa shi ne, wannan attakar matattun dabbobi da ya narke zuwa wannan sinadari na danyen mai cikin tsawon shekaru, a can karkashin kasa yake, a makare.  Saboda tsananin zafin da ke can karkashin kasa, da wanda ke samuwa a tsakanin duwatsu, sai ya rika tilasta wa wannan daskararren ruwa na danyen mai rabuwa zuwa kashi biyu.  Bangaren da ke tsakanin duwatsu sai ya gangara zuwa can kasa, ya ci gaba da taruwa har ya zama wata rijiya ta musamman.  Wannan shi ake kira Oil Reserves, wato rijiyar danyen mai na karkashin kasa. Kuma shi ne nau’in mai da ake iya hakowa a yau, ta hanyoyi daban-daban.  Kasancewar wannan lamari ya samo asali ne daga daular Girka, wato Greece ta da, shi yasa a wancan lokaci suke kiran wannan nau’in danyen mai da suna “Petroleum”, kuma abin da wannan kalma ke nufi shi ne, “Man Dutse”; wato man da aka samo shi a tsakanin duwatsun karkashin kasa.  Asalin Kalmar “Petro”, a harshen Girkanci shi ne “Dutse”.  Kalmar “Leum” kuma yana nufin “Mai” ne.  Don haka suke kiranshi “Petroleum”, wato “Man Dutse”.

Sauran man da ke saman dutsen kuma sai tsananin zafin da ke cikin kasa ya tilasta musu haurowa, tunda ba za su iya komawa kasa ba saboda samuwar duwatsu a kasansu.  A haka za su ci gaba da haurowa har sai sun riski kasar da muke takawa, su ci gaba da malala kamar yadda idaniyar ruwa ke yi a samansa.  Wannan nau’i da ke malala a saman kasa da kansa, shi masana ke kira Surface Oil.  Kuma a tarihin alakar dan adam da danyen man fetur, shi ne abin da ya fara nuna samuwar mai a karkashin kasa. Sanin hakikanin lokacin da wannan nau’in mai ya fara samuwa a tarihin duniya ba abu bane mai yiwuwa a rubutacciyar tarihi.  Saboda wadanda suka gano shi, ba su da tabbacin cewa su ne na farko, balle su yi alfahari da hakan.  Ko da sun san hakan, ba lallai bane ya zama a lokacin akwai hanyar rubutu kamar yadda muke da ita a yanzu. Idan ma akwai, to babu tabbacin an taskance sunan wanda ya gano wannan lamari.  Da an taskance sunansa kuwa, to lallai da an sani.

Amfanin Danyen Mai a Zamanin Da

Kamar yadda bayanai suka gabata, an gano danyen mai ne sanadiyyar tunbatsa da yayi zuwa saman kasar da muke takawa, saboda masifaffen zafin da ya koro wani bangarensa daga can karkashin kasa, ko tsakanin duwatsu.  Amma bangaren da ya gangara kasan dutsen shi yake zama rijiyar mai, kamar yadda muka sani a yau, kuma shi ne ake hakowa a sauran kasashen da suka gano wannan arziki.  Dangane da haka, wadanda suka fara gano wannan bangaren mai da ke malala mai suna Surface Oil, ko kadan ba su zaci wani arziki bane na a-zo-a-gani.  Don haka a zamanin baya babu abin da suke yi da shi sai zuba wa fitilunsu don ganin haske, ko cuccura shi don yin ciko a jikin jiragen ruwa (wato Caulking kenan a turance), da shafa shi a jikin karafa ko wasu abubuwa masu tsauri don mayar da su masu taushi, da yin rigunan shiga ruwa da  su – don an gano cewa suna da tasiri wajen hana ruwa shiga cikinsu, don mai ne.

A karshe kuma an yi amfani da su ne wajen yin magunguna ko hada magunguna da su.  Dukkan wadannan nau’ukan amfani da aka yi da wannan danyen mai a zamanin baya, babu wani bincike na musamman da mutane suka gudanar kafin hakan, sai dai gwaji kawai. Da zarar sun ga ya musu abin da suke so, sai su ci gaba da amfani da shi a haka.  Masana sun nuna cewa dukkan wadannan al’amura sun fara samo asali ne daga Karni na goma sha hudu miladiyya, wato 14th Century – wajen shekaru dari takwas kenan yanzu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.