Yadda Shafin “WikiLeaks” Ya Canza Tsarin Samar da Bayanai a Intanet (2)

Kashi na biyu cikin nazarin da muke yi kan shafin WikiLeaks. A sha karatu lafiya.

108

Hankado Bayanan Sirri

Kamar yadda mai karatu ya karanta a baya, wannan shafi na WikiLeaks ya shahara ne wajen hankado bayanan sirri da suka shafi wasu gwamnatoci ko kamfanoni da ke badakala da kudin jama’a, a kowace kasa ce kuwa.  Dangane da haka ya hankado bayanai masu dama da za su iya mummunan tasiri a siyasar duniya, wanda kuma hakan ne ya kara masa shahara a duniyar hakika da ta Intanet.  Bayanan sirrin da wannan shafi ya fara hankadowa, wanda kuma yayi tasiri a siyasar duniya shi ne kan batun kashe-kashe da jami’an tsaro suka yi ta yi a kasar Kenya tun bayan zaben shugaban kasa da aka yi na biyu.  Wadannan bayanan sirri da shafin ya hankado ya dumama iskar siyasar duniya, inda har a karshe Kungiyar Amnesty International ta bashi kyauta ta musamman a fagen fafutikar neman ‘yancin dan adam a shekarar da ta gabata.

Bayan haka, shafin ne ya fara buga nassin Jakar Sadarwar Imel din Gwabnar jihar Alaska ta kasar Amurka, wato Palin.  Kuma kowa ya amince cewa lallai da gaske jakar Imel dinta ne wasu ‘yan Dandatsar kasar Amurka suka hankado daidai lokacin da ake kokarin gudanar da zaben shugaban kasar Amurka, inda take takarar mataimakiyar shugaban kasa.  Labarin wannan lamari na fara yaduwa, sai wannan shafi na WikiLeaks ya buga nassin sakonnin da wadannan mutane suka hankado, cikin shafinsa; kowa ya gani.

Bayan wadannan, shafin WikiLeaks ya sake hankado bayanan sirrin kasar Amurka da suka shafi Yakin Afghanistan, kamar yadda bayanai  suka gabata a baya, ya hankado wani faifan bidiyo da ke nuna yadda sojin Amurka suka karkashe mutane a kasar Iraki, tare da dimbin bayanan sirri har wa yau kan Yakin Irakin ma gaba daya.  Shahararren bayanin sirri na karshe da wannan shafi na WikiLeaks ya sake hankadowa sun shafi sakonnin diflomasiyya ne tsakanin kasar Amurka da sauran kasashen da take huldar diflomasiyya da su, wato Diplomatic Cables ko kuma Cablegate, kamar yadda shafin ya ayyana su.  Wannan lamari na karshe ne ya fi tasiri da kuma tayar wa gwamnatin kasar Amurka hankali fiye da kowanne, saboda hakan tonon asiri ne kan tsarin huldodin da suka shafe ta da sauran kawayenta. Bayanan na da yawa, domin har gobe kara hankado shafin yake yi.  Nassin sakonnin da ke dauke cikin wannan kundi na diflomasiyyar kasar Amurka ya kai kusan miliyan daya – ciki har da wasu kalaman siyasa da suka shafi kasa da hukumar Najeriya mai ci a yanzu, da kuma kamfanin hakon mai na Shell.  Wannan lamari ya bai yi wa kasar Amurka dadi ba, duk da cewa wasu na ganin kamar akwai hadin baki tsakaninta da wannan shafi, don cin ma wata manufa ta siyasa.  Hakika babu kamshin gaskiya cikin wannan zargi ko kadan.  Wannan zance ne na siyasa wanda ba za mu tattauna shi ba a nan.  A halin yanzu ga bayani kan yadda suke hankado wadannan bayanai, tare da yada su.

Tsarin Bincike Wajen Hankado Bayanai

Da farko dai tukum, zai dace mai karatu ya san cewa wadanda suka mallaki wannan shafi na WikiLeaks dukkansu kwararru ne kan harkar kwamfuta, ba wai ‘yan jarida bane kadai, kamar yadda galibin masu shafuka irin wannan suke.  A takaice ma dai, akwai tabbataccen bayani kan cewa ‘Yan Dandatsa ne, wato Hackers, masu amfani da kwarewarsu wajen hankado bayanai a ko ina suke.  Wannan ba zai hana samuwar wasu kwararru ‘yan uwansu ko wadanda suke basu hadin kai ta karkashin kasa ba.  Hakan ma shi ya fi sauki, musamman ta la’akari da dabi’un wadannan mutane wajen zumuncin musanyar bayanai kyauta, ta hanyar da su kadai ke iya fahimtar tsarinsu.  Wannan ne ma yasa lokacin da aka kama Assange, aka gurfanar da shi a gaban kuliya a kasar Ingila, har wasu kamfanonin karbar tallafi ta Intanet suka rufe taskarsa da yake amfani da su wajen karban tallafi, nan take sai magoya bayansa – ‘Yan Dandatsa – suka fara kai ma shafukan Intanet din wadannan kamfanoni farmaki, inda suka rufe su,  suka hana mutane mu’amala da su.  Kai, hatta shafin Intanet din wasu hukumomin kasar Suwidin ma, duk an kai musu hari.  Abokin biri, in ji Hausawa, suka ce kare.

Kamfanin da ke dauke da kwamfutocin da wannan shafi ke dauke a ciki yana kasar Suwidin ne, sunansa PRQ, kuma kamfani ne da yayi rajista a layin tsarin kasuwancin da ba ya bukatar sanin asali da tsarin wadanda yake mu’amala da su, balle har ya adana wasu bayanai da suka shafi abokan huldarsa.  Yana da kwamfutoci bila adadin a warwatse a duniya – musamman Turai.  Bayan haka, kasar Suwidin ce kadai ke da dokokin da basu yarda a kama binciken yadda wani kamfanin yada labarai ya samo bayanansa ba balle har a tuhume shi kan abin da ya yada.  Wannan ya baiwa su Julian Assange damar kafa wannan shafi cikin sauki a kasar, tare da girke shi cikin wasu kwamfutoci da babu mai iya kaiwa garesu duk kwarewarsa wajen dandatsanci. Bayan haka, sun samar da ma’adana na musamman masu dauke da dukkan shafukan da ke asalin shafin da mutane ke mu’amala da shi.  Sun yi hakan ne don “ajiya” – gida biyu maganin gobara.  Idan aka rufe shafin ta hanyar dandatsanci, nan take sai su bude wani shafin daban.  Wannan tsari shi ake kira Server Back-up ko kuma Server Prototyping, a fannin Kimiyyar Sadarwa ta zamani.

- Adv -

Gidan yanar sadarwar wannan shafi na WikiLeaks na dauke ne da zaratan masarrafan kwamfuta da ake takama da su a fannin tsaro da sato bayanai a ko ina ne.  Ire-iren wadannan   masarrafai ko manhajar kwamfuta dai sun hada da: MediaWiki, da Freenet, da Tor, da kuma PGQ.  Da wadannan masarrafai ko manhajoji ne suke gudanar da harkokinsu.  Masarrafai ne masu matukar tasiri wajen yada bayanai, da nemo su, da kariya ga bayanai, da kuma tsarin shiga da mu’amala da su.  Duk sa’adda aka kai musu hari a shafin da suke gudanar da al’amura, sai su koma wani shafin nan take.  Daga ko ina suke suna iya zuba bayanai a shafin, kuma suna iya sarrafawa tare da tsara yadda suke so su kasance a shafin.  A haka suka zama gagarabadau; ta yadda duk suka so suke nemo bayanai.

Idan wani ya turo musu bayanai, akwai kwamiti da suka kafa wanda ke yin nazari kan wanda ya turo bayanan, da kasar da ya fito, da alakarsa da bayanan da ya turo, da kuma sana’a ko abin da yake yi.  Bayan haka, suna da kwararru a harkar gina manhajar kwamfuta, wato Programmers, masu lura da tsarin bayanan, ko yanayin da aka turo, ko kuma irin masarrafar da aka yi amfani da ita wajen turo su. Akwai kwararru a fannin harsunan duniya, masu yin nazari kan harshe ko yaren da aka turo bayanan cikinsu.  Sannan ka’ida ta karshe ita ce, ya zama bayanan ba wasu sanannun bayanai bane wadanda kowa ya saba da su.  Domin suna neman bayanan sirri ne, masu tasiri a fannin siyasa ko diflomasiyya, saboda kimtsattsiyar manufarsu na kafa wannan shafi.  Idan bayanin da aka turo musu ya cika wadannan ka’idoji, kuma ya tsallake siradin masu nazari, sai su buga shi a shafinsu, ko waye ya shafa, babu ruwansu.

Tasirin Shafin WikiLeaks a Fannin Sadarwar Zamani

Tasirin wannan shafi na WikiLeaks a bayyane yake, musamman ma a siyasar duniya. To amma tunda damuwarmu a wannan shafi shi ne fahimtar tasirinsa a harkar Kimiyya da Fasahar Sadarwa ta zamani, ba za mu tabo wancan janibi na siyasa ba.  A wannan fanni na kimiyyar sadarwar zamani shi ma, tasirin wannan shafi da ayyukansa a Intanet a fili suke.  Janibin farko da za mu duba, kamar yadda muka yi alkawari, shi ne bangaren da ya shafi tsarin yada labarai da nemo su, musamman labarai ko bayanan da ba ko ina ake iya samunsu ba, sai da wata kwarewa ta musamman.  Wannan fanni, wanda a turancin yada labaran ake kira Investigative Journalism, hanya ce da ta shafi gudanar da bincike na musamman, na kwakwaf, ta hanyar karkashin kasa – ta hanyar da ta dace da wacce bata dace ba.  Wannan a tsari da Kalmar aikin jarida kenan.

Amma a tsarin yada labarai ta Intanet, wannan kalma ta fi fadi da gamewa.  Domin ta hada da yin amfani da hanyar dandatsanci, wato Hacking ko Cracking, don “sato” bayanan sirri, kamar yadda masu wannan shafi ke yi ko bi. Duk da cewa an dade ana hankado bayanai ta wannan hanya da tsari a Intanet, amma a ba irin wannan sifa ba.  Domin bayyanar shafin WikiLeaks ne ya fara haska hanya a wannan fage, inda ya samu karbuwa a idon da yawa cikin mutanen da ke mu’amala da wannan fasaha ta Intanet.  Kai hatta daga shugabannin wasu kasashe ma ya samu karbuwa.  Domin lokacin da wannan shafi ya fara hankado bayanan sirri kan diflomasiyyar kasar Amurka, shugaban kasar Benuzuwela, Hugo Chavez, ya jinjina musu sosai.  Bayan haka, hatta wasu kafafen yada labarai masu kima a duniya, irinsu tashar tauraron dan adam ta Aljazeera, wato Aljazeera English sun yi na’am da wannan tsari.  Hakan a fili yake, inda har wanann shafi kan baiwa tashar daman shiga ko isa zuwa ga bayanan da ya fara hankadowa a karon farko, irin damar da ba a baiwa tashoshi irinsu CNN ko BBC ba a misali.

Bayan haka, a yanzu haka akwai wani sabon shafi da wasu suka bude mai suna OpenLeaks, wanda shi ma kusan tsarinsa daya ne da shafin WikiLeaks.  Abin da ya bambanta su kawai shi ne, shafin OpenLeaks yana baiwa masu ziyara daman turo tushen jakar bayanai ne a shafin, ta yadda idan masu karatu suka bukaci budowa ko sauko da bayanan, wannan shafi nasu zai je cikin kwamfutar da ke dauke da wadannan bayanai, a ko ina take a duniya, don budo su.  Amma shafin WikiLeaks, duk da cewa shi ma da haka ya fara, amma a karshe sai ya rufe kofa; sai masu shafin kadai suke zuba bayanai don amfanin masu ziyara, shi kadai yake kidi da rawansa.  Bayyanar wannan sabon shafi mai gudanar da aiki makamancin na WikiLeaks, shi ke nuna mana cewa lallai ga dukkan alamu, nan gaba za a ci gaba da samun ire-iren wadannan hanyoyin yada labarai da bayanai na sirri a duniyar Intanet.

Bangare na biyu kuma shi ne, tasirin wannan tsarin samar da bayanai zai canza yadda mutane ke neman bayanai a Intanet.  A yayin da a bayan mutane na mu’amala ne kadai da bayanan da mai gidan yanar sadarwa ya ga daman zubawa da aikawa kadai, a yanzu masu ziyara na iya karanta abin da ya shafi bayanan sirri dangane da kasashensu.  Wannan, duk da cewa ba abu bane zai iya haifar da mai ido a galibin kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa, da kasashen Asiya irin su kasar Sin da sauransu, zai dada wayar da idanun masu mu’amala da Intanet, tare da samar da wani sabon salon hanyar samun bayanai kai tsaye daga shafuka na musamman.  Bayan haka, akwai tabbacin cewa mutane za su aminta da ire-iren bayanan da suke samu, cewa lallai gaskiya ne, musamman idan sun shafi wasu al’amura da bayaninsu ya zama boyayye ga jama’a a duniya ko kasashen da abin ya shafa.  Duk wanda ya bibiyi dambarwar da aka ta yi tsakanin jami’an gwamnatin Amurka da masu wannan shafi na WikiLeaks bayan sun bayar da sanarwar cewa za su fitar da bayanan da suka fitar daga baya, zai fahimci cewa lallai bayanai ne gaskiya, abubuwan sun faru, kuma an boye su ne ga jama’a don wasu manufofi na siyasa – masu kyau ko munana.

Wannan, a karshe, shi ke nuna mana cewa rayuwa a duniyar Intanet, kusan ta game da irin rayuwar da muke yi a zahiri.  Duk da cewa aikin dandatsanci laifi ne a dokokin mu’amala da Intanet, amma kuma, a dokokin kasashen Yamma – musamman kasar Amurka – sato bayanai ta hanyar dandatsanci, wadanda suka shafi yadda ake gudanar da mulki, da siyasa, da kuma al’amuran jama’a, da kuma yada su ga jama’ar da abin ya shafa, ba laifi bane ko kadan.  In kuwa haka ne, tsarin samar da bayanai a Intanet zai canza nesa ba kusa ba, saboda masu neman bayanai na sirri za su karu, hakan kuma shi zai haddasa samuwar shafuka irinsu WikiLeaks a Intanet.  A dai juri zuwa rafi…!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.