Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1)

Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya.

1,194

Tambaya

Abban Sadik, an ce masana Kimiyya na zamani sun tabbatar da wasu daga cikin Kimiyyar Al-Kur’ani mai girma.  Wadanne ne daga ciki?”  –  Khaleel Nasir Kuriya, Kiru, Kano (GZG274): 07069191677


Gabatarwa

Malam Khaleel Nasir muna godiya kwarai da wannan tambaya mai matukar muhimmanci, kuma Allah saka da alheri.  Amsa wannan tambaya gaba dayanta na bukatar bincike na tsawon zamani mai dauke da hujjoji daga Kur’ani da kuma manyan littafan zamani.  Domin harka ce da ta kumshi ilimi.  Amma za mu yi iya kokarinmu, daga wannan mako zuwa makonni masu zuwa, don ganin mun tabo kadan cikin ire-iren nau’ukan binciken da masana kimiyyar zamani suka yi kuma suka tabbatar, wadanda suka dace da abin da Allah ya fada, shekaru dubu daya da dari hudu da talatin da suka wuce.  Wasunsu sun tabbatar da abin da Kur’ani ya fada kai tsaye, tare da sallamawa.  Wasun su kuma sun kauce cikin lafazinsu.  Abin da suka nuna kawai shi ne, wannan bincike da suka yi da kuma dacewarsa da abin da ke cikin Kur’ani abu ne mai dauke da mamaki, kuma bai kamata a ce mutum ne ya fadi maganar ba.  Sai dai kafin mu fara kawo ire-iren wadannan bincike da ra’ayoyi, zai dace mai karatu ya fahimci wasu abubuwa masu muhimmanci kan tsarin Al-Kur’ani wajen tabbatar da gaskiyar abu, da kuma tsarin malaman Kimiyya wajen tabbatar da nasu binciken.

Tsarin Kur’ani Wajen Tabbatar da Ilimi

Ga duk wanda ya saba karanta Kur’ani mai girma, ya kuma fahimci sakon da yake kokarin isarwa ga mai karatunsa, zai ga cewa littafi ne mai neman shiryar da mai karatu ta hanyoyi masu sauki, wadanda mai karatun zai iya bi don ya shiryu.  Littafi ne mai dauke da dimbin ilimi wanda Allah kadai ya san yawansu.  Littafi ne mai dauke da usulubi mai dadi wajen karatu da karantarwa.  Manyan hanyoyin da Kur’ani ke amfani dasu wajen tabbatar da dalilan Kimiyya sun kunshi hanyar gani, ko kallo, da nazari ko tunani, da kuma tabawa.  Sauran hanyoyin sun hada da hakawa, ko tonawa (don ganin yadda abu yake), da haurawa, da gangarawa, musamman kan abin da ya shafi sararin samaniya da sauran duniyoyin da ke makwabtaka da tamu.  Ga duk wanda ya bi wadannan hanyoyi, zai iya fahimtar sirrin da ke cikin halittan sama da kasa da taurari da wata da rana da karkashin kasa da hazo da ruwan sama da iska da sanyi da zafi da tsarin halittan dabbobi da na dan Adam, da dai sauran abubuwan da Allah Ya watsa a wannan duniya tamu.

- Adv -

Duk wani abin da malamin kimiyya zai karanta ko yi nazari a kai, Kur’ani ya tabo bayani a kanshi, ya kuma kalubalance shi da ya duba ya gani, ko yayi tunani a kai, ko kuma ya hango ya gani, da dai sauran hanyoyin kalubale.  In ya ga dama kada ya fara yin imani sai ya tabbatar da gaskiyar abin da aka sanar dashi.  Amma kuma da zarar ya fahimci gaskiya, to fa hujja ta tabbata a gareshi ko a kanshi.  Wannan ya sha banban da tuhumar da sauran masu akidu ke yi wa Musulmai, cewa: muslims are too dogmatic.  Ma’ana, musulmi mutane ne masu yawan yarda da abu kawai ba tare da sun san hakikaninsa ba.  Wannan kalma suna fadinta ne a babin zargi ba yabo ba, ga dukkan musulmi.  Suna ganin musulunci bai baiwa mutane damar kalubalantar abin da ya fada a Kur’ani ba.  Masu wannan kalami sun jahilci addinin gaba daya.  Da sun karanta Kur’ani sosai, da basu fadi haka ba.  Ga misali nan guda daya, inda Allah ke cewa:

“Lalla ne, a cikin halittan sammai da kasa, da sabawar dare da yini da jirage wadanda suke gudana a cikin teku (dauke) da amfanin mutane, da abin da Allah Ya saukar daga sama na ruwa, sai ya rayar da kasa da shi bayan mutuwarta, kuma ya watsa cikinta daga dukkan dabbobi, da kuma juyawar iskoki da girgije horarre a tsakanin sama da kasa; hakika akwai ayoyi ga mutane masu hankalta.” (Bakara: 164)

Wannan aya, kamar yadda malaman tafsirin Kur’ani suka tabbatar, ta kumshi dukkan nau’ukan ilimin kimiyya da dan Adam ke alfahari dashi a yau.  Daga ilimin Fiziya (Physics), zuwa ilimin sinadaran da ke tsakanin sama da kasa (Chemistry), zuwa ilimin kasa (Geography), da ilimin halittu (Biology), da na tsirrai (Botany), da na teku (Oceaonology), da ilimin tsarin sadarwa (Communication), da na sararin samaniya (Atronomy), da tattalin arzikin kasa, da sauran nau’ukan ilimin da sai mai bincike ya bincika zai gano su.  Abin sha’awa shi ne, da Allah Ya gama sanar da mai karatun wannan aya tsarin halittan da yayi a ciki, sai yace “…hakika akwai ayoyi ga mutane masu hankalta.”  Wannan kuwa ke nuna cewa in har ka hankalta, to za ka ga abin da Allah ke ikirarin ya sanya ko halitta.  A takaice dai wannan na nufin duk abin da Allah ya fada abubuwa ne da ake iya ganinsu da ido, ko iya hankaltar tsarinsu da irin abin da ke cikinsu na mamaki da al’ajabi.

Duk da dimbin ilmin da ke cikin wannan littafi mai girma, mai karatu zai yi mamakin jin cewa Al-Kur’ani ba littafin kimiyya bane, balle na ilimin kasa.  Ba littafin koyar da sadarwa bane kadai..a a, littafin shiriya ne.  Duk abin da ka gani a ciki wanda ya shafi wani ilimi, riban kafa ne kawai. Amma asali Allah Ya kawo shi ne don dan Adam ya fita daga kangin bauta wa wani halitta makamancinsa, zuwa ga bauta wa wanda ya halicce shi kadai, shi ne Allah.  Wannan tasa tsarin littafin yake a sura-sura, ba wai babi-babi mai Magana a kan wani nau’in ilimi ba.  Sabanin sauran littafan kimiyya, inda marubucinsu ke shirya littafin zuwa babi-babi kan abin da yake son karantarwa.  Don haka Kur’ani littafin addini ne da shiriya.  Duk abin da ka samu a cikin wanda ke karantar da kai wani ilimi na neman abin duniya ko amfanin rayuwa, to riba ne da Allah ya sanya a ciki.  Idan ka kara imani da abin da ke ciki, sai ka fi amfana da ribar fiye da kowa.  Wannan tasa sauran masu binciken Kimiyya masu lekawa cikin Kur’ani suna dauko abin da ya dace da iliminsu suna sauya masa tsari don neman suna a duniya, ribarsu kadan ne in ka kwatanta da na wanda yayi imani da littafin.  Wannan, a takaice, shi ne tsarin da Kur’ani ke bi wajen kiran mai bincike yayi bincike cikin abin da aka fada cikin littafin, don gano gaskiyar abin da aka sanar dashi a ciki.

A nasu bangaren, malaman kimiyyar zamani na bin hanyar bincike ne na kwakwaf, don tabbatar da abin da ake ikirari a kai.  Hanyoyin bincikensu na nan da yawa, kamar yadda muka sani.  Suna amfani da na’ura a dakin bincike, da na’urar hangen nesa, da wanda suke kafawa a wajen da suke binciken.  Har wa yau suna amfani da tsarin dauko abin da suke son bincike don yin nazari a kansa, kai tsaye.  Bayan haka, suna da ka’idoji da suke amfani da su (wato Scientific Methodology) wajen tantance abin da samu na sakamako a yayin da suke binciken.  Sannan su basu yarda da duk abin da ba a ji ko gani ko iya taba shi ba.  Duk abin da ake kira hankalta ko ji ko taba shi kadai suke la’akari da shi.  Sannan a galibin lokuta sukan samu sakamako na wucin-gadi, wanda suke amfani dashi don ci gaba da wani binciken.  Bayan haka, saboda kasancewarsu ‘yan Adam ne masu tawaya, ba dukkan lokuta ko bincike suke gano abin da yake daidai ko gaskiyar abin da suke nema ba.  Wannan tasa kafin su binciken sai sun tsara wasu nau’ukan hasashe (wato Hypothesis) da zasu musu jagora wajen samun irin sakamakon da suke bukata.  Wannan, a takaice, shi ne tsarin da malaman kimiyya ke bi wajen gudanar da bincikensu a kimiyance.  Addini da al’ada basu tasiri wajen bincikensu ko kadan.  “Zahiri”, shi ne abin da suka sani.  Allah mana jagora!


Sanarwa!

Ina sanar da masu karatu, musamman wadanda ke birnin Katsina da Zariya, cewa ina nan tafe cikin mako mai zuwa in Allah Ya yarda.  Zan fara zuwa Katsina ne, wajen dawowa in tsaya a garin Zariya.  Tafiya ce ta kashin kaina, kuma ina sa ran kaiwa masu karatu da ke wadannan wurare ziyara in da hali.  Don haka ga wadanda suke Katsina ko Zariya, sa iya aiko min da lambar wayarsu, don in tuntube su a yayin da na isa.  Sai na ji daga gareku.  –  Baban Sadik

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    ALHAMDULILLAH!!!

    A HALIN YANZU INA CIKIN ZARIA ANAN NAKE YIN KARATU.

    SAI DAI NA KUSA KAMMALAWA.

    ZAN SO ACE ALLAH YA NUNA MIN RANAR DA ZAMU HADU A ZAHIRI BA A ONLINE KAWAI BA, AMMA KUMA NAGA AN WALLAFA WANNAN MAKALA SAMA DA SHEKARA 1 .

    INAYI MAKA FATAN ALKHAIRI.

    INSHA ALLAH IDAN DA RAI DA RABO WATA RANA ZAMU HADU.

Leave A Reply

Your email address will not be published.