Asali da Samuwar Wayar Salula a Duniya

Kashi na biyu cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

607

Asali da Samuwar Wayar Salula

Wayar salula ta samo asali ne shekaru kusan dari da suka gabata, daga kasashe guda shida, musamman.  Wadannan kasashe dai su ne: Kasar Amurka, da Ingila (ko kace Burtaniya), da Jamus, da Rasha (ko Rusasshiyar Daular Sobiet), da Suwidin, da kuma kasar Finland.  Idan ka cire kasar Amurka, duk sauran kasashen na nahiyar Turai ne.  Kuma sabanin yadda muke ganin wayar salula irin ta yau, wannan fasaha ta samo asali ne daga kananan rediyon sadarwa masu amfani da tsarin hanyar sadarwa biyu (Two-way Radio), wadanda ake sanyawa a cikin motocin haya, ko motocin daukan marasa lafiya, ko motocin ‘yan sanda.  A wancan lokaci ana kiransu Radio Rigs, kuma basu amfani da babbar tashar sadarwa na tarho ta kasa, saboda rashin lambar waya da suke fama da shi.

Ire-iren wadannan wayoyi ko rediyon sadarwa suna amfani ne da hanyoyi biyu kadai, don sadarwa, kuma dole ne ya zama wanda zai kira ka yana da irinta; daga kai sai shi kadai.  Kamar yadda bayani ya gabata, suna makale ne a cikin mota.  Sai a mota ake iya amfani dasu.  Daga baya aka kera wadanda ake iya rikewa a hannu, amma kuma baka iya amfani dasu sai ka jona su da wutar mota, ta hanyar makalutun kunna sigari da ke cikin mota, wato Cigarette Lighter Plug.  Dole sai ta haka, domin basu da batir, kuma basu da siginar rediyo da ke jone da tashar sadarwa. Wadannan nau’ukan kuma su aka kira Bag Phones a wancan lokaci.  Domin kana iya sanya su a cikin jaka kayi yawo dasu, sai dai kuma basu da bambanci da wadanda ke cikin mota.  Wannan fasaha a kasar Amurka aka kirkireta, kuma hakan ya faro ne tun shekarar 1911.

Cikin shekarar 1926 sai wannan fasaha ta yadu zuwa kasar Jamus, inda aka kayatar da ita, aka sanya mata suna Radio Telephony.  Tsarinsu duk iri daya ne; ana amfani da su ne a manyan jiragen kasa da ke daukan mutane daga birnin Berlin zuwa birnin Hamburg, duk a kasar Jamus.  Har wa yau an yi amfani dasu a jiragen sama, inda matuka jirgi ke amfani dasu don sadarwa tsakaninsu da ma’aikatan tashar jirgi.  Sannan a karshe kasar Jamus ta sanya su a cikin manyan tankunan yakinta da tayi amfani da su a lokacin yakin duniya na biyu.

Ana shiga shekarar 1940 sai kamfanin Motorola da ke kasar Amurka ya canza wa wannan fasaha tsari, inda ya bullo da wayoyin hannu masu matukar girma da nauyi.  Domin kowane daya zai kai kaurin damtsen hannun matashi a yau, kuma suna dauke ne da batir.  Wadannan su ne wayoyin da ya sanya musu suna Walkie Talkie, kuma ya kera wa Hukumar Sojin Amurka ne. Da aka haura zuwa 1946 sai aka samu wasu injiniyoyi ‘yan kasar Rasha guda biyu; da D.G. Shapiro da kuma Zaharchenko, wadanda suka yi wani bincike kan tsarin sadarwa, har suka yi gwaji a mota.

Wannan tsari ya kumshi tsarin sadarwa ta wayar salula mai cin kilomita 20, kuma sabanin binciken da wasu suka yi a baya, wannan tsari na su Zaharchenko na iya hada alaka tsakanin wadannan wayoyin salula na wancan lokaci da kuma tashar sadarwa da ke kasar.  Wannan, a iya bincike na, shi ne yunkurin da aka fara yi don hada alaka tsakanin wayoyi da kuma tashar sadarwa a tsarin amfani da wayar salula irin ta zamani.  Shapiro da Zaharchenko sun yi kokari ta wannan bangare.

- Adv -

Da aka shiga shekarar 1947 sai aka samu wasu injiniyoyi daga kamfanin binciken kimiyya na Bell Labs da ke kasar Amurka, masu suna Douglas H. Ring, da kuma Rae Young, suka gudanar da wani bincike na musamman su ma kan sadarwa a tsarin sadarwar rediyo tsibi-tsibi.  Sun gabatar da wannan bincike ne don amfanin wayar salula da ke makale cikin motoci.  To amma saboda rashin samuwar fasahar wayar salular da za ta dace da wannan tsari da suka bullo dashi, sai ba a dabbaka ba.  Haka wannan bincike mai maiko ya shiga kundin tarihi, ya kama bacci.

Ana cikin haka, sai ga kamfanin Ericsson (ko Sony Ericsson) a shekarar 1956 da wata sabuwar fasaha mai suna Mobile Telephone system A, ko MTA a gajarce.  Ta bullo da wannan sabuwar waya ce a kasar Suwidin.  Sai dai, kamar nau’in Walkie Talkie, su ma suna da dan karen nauyi.  Kowanne daga cikinsu ya kai nauyin kilogram arba’in (40kg).  Amma daga baya sai kamfanin ya dada kayatar dashi, inda ya mayar dashi mai nauyin kilogiram tara (9kg).  Hakan ya faru ne a shekarar 1965.  Ya zuwa shekarar 1983, kamfanin ya samu kwastomomi har dari shida, wadanda suka saya, kuma suke amfani da wannan nau’in waya.  Abin dai bai dore ba, domin cikin shekarar aka dakatar da sayar da wannan waya nau’in MTA. 

Daga nan kuma sai guguwar bincike ta sake komawa kasar Rasha, cikin shekarar 1957, lokacin da wani matashi injiniya mai suna Injiniya Leonid Kupriyonovich ya kirkiri wata sabuwar wayar salula da ya sa mata suna ta amfani da haruffan sunayensa, wato LK-1.  Daga baya aka sake wa wayar suna zuwa “Radiophone”.  Wannan nau’in waya dai waya ce ta salula, mai dauke da kunnuwan sadarwa (Antenna), kuma kai tsaye take amfani da tashar sadarwar kasar Rasha.  Nauyinta duk bai shige Kilogiram uku ba (3kg), tana kama tashar sadarwa a tazarar kilomita ashirin zuwa talatin (20 – 30km), kuma kasancewarta mai amfani da batir, kana iya yin kira har na tsawon sa’o’i ashirin zuwa talatin shi ma, batirin bai dauke ba.  Wannan ci gaba ne sosai, idan muka yi la’akari da yanayin binciken da aka yi a baya. A shekarar 1958 sai wannan matashi ya kara kayatar da wannan waya tasa, inda nauyinta ya gangaro zuwa giram dari biyar kacal (500gm).

Har zuwa zamanin da injiniya Leonid ya gudanar da bincike ya kuma samar da wayarsa ta LK-1, ana amfani wayoyin salula ne a wuri guda.  Inda kake, nan kadai zaka iya kira.  Duk kuwa da cewa wayoyin na yin hakan ne ta hanyar jonuwa da tashar sadarwa ta kasashen da suke ciki.  Amma tsarin sadarwar a waje daya kawai take.  Da zarar ka fice daga unguwa ko garinku, to shikenan.  Baka iya buga waya ko amsa kira.  Sai cikin shekarar 1970, lokacin da wani kwararren injiniya mai suna Amos Joel Jnr da ke aiki a Cibiyar Bincike ta Bell Labs a kasar Amurka ya bullo da wani “tsarin sadar da yanayin sadarwa daga zango zuwa zango” da ya sanya wa suna “Call Handoff”.  Wannan tsari ne ke bayar da damar yin kira ko amsa kira ta amfani da gamammiyar tsarin sadarwa tsakanin zangunan sadarwa.

Misali, kana iya kiran wani alhalin kana tuki ko tafiya a kasa, daga unguwa ko garinku inda tashar sadarwarku take, har ka fice zuwa wata tashar ba tare da sadarwar ta yanke ba.  Wannan sabon tsari ya taimaka gaya, inda a karshe aka samu kamfanin sadarwar tarho mai suna AT&T da ke kasar Amurka ta ci gaba da amfani dashi, har ta samar da tsarin sadarwa mai suna Advance Mobile Phone Service (AMPS) a tsarin sadarwa nau’in Analog.  Hakan ya faru ne a shekarar 1971.

Daga nan kuma Hukumar Kasar Finland ita ma ta samar da nata tsarin mai suna ART, duk a shekarar.  Wannan dai a karshe, shi ya ci gaba da haifar da samuwar kamfanonin sadarwar wayar salula a duniya, tare da kayatar da tsarin sadarwa mai inganci, daga wani zamani zuwa wani, har zuwa wannan zamani da muke ciki.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA says

    Masha Allah

Leave A Reply

Your email address will not be published.