Binciken Malaman Kimiyya Kan Tsibirin Bamuda (3)

Wannan shi ne kashi na uku kuma na karshe, cikin jerin binciken da muka faro makonni biyu da suka gabata kan tsibirin Bamuda. Da fatan masu karatu sun samu fa’ida kan haka. A sha karatu lafiya.

852

Ra’ayoyin Malamai Kan Tsibirin Bamuda

Bayan nazari kan rubuce-rubucen da maruba ko masana suka yi kan wannan kusurwa na shedan da a Turance ake kira The Devil’s Triangle, ra’ayoyi nau’uka uku ne suka fito fili kan haka. Wadannan ra’ayoyi, idan mai karatu yayi nazari kan su, zai ga cewa kusan kowanne daga cikinsu ya danganci abin da ke faruwa a wajen.  To amma, ganin cewa kowannensu ya rike ra’ayinsa ne a matsayin shi ne daidai, wannan tasa muka fitar da ra’ayi gamamme da ya kumshi dukkan sauran ra’ayoyin nan guda uku, don bai wa mai karatu wata sabuwar mahanga kan wannan lamari.  A halin yanzu ga wadannan ra’ayoyi nan da muka taco, kan musabbaban da ke haddasa wadannan al’amura masu ban mamaki a Kusurwar Bamuda, ko The Bermuda Triangle.

‘Yan Al’ada da Gargajiya

Sanannen ra’ayi wanda a kanshi ne aka fara rubuce-rubuce kan wannan Tsibiri, shi ne wanda ya ke ta’allaka dalilan da ke sa jirage na bacewa ga wasu ra’ayoyi na gargajiya da al’adu.  Masu wannan ra’ayi suka ce babban abin da ke haddasa bacewan jirage bayan sulmuyarsu a cikin ruwa, ko ma a rasa inda suka shiga daga sararin samaniya ba tare da samun wata alama da ke nuna abin da ya kawo hakan ba, shi ne dayan abubuwa hudu.  Abu na farko suka ce akwai wasu halittu da ke shigowa wannan duniya daga wasu duniyoyin da ke makwabtaka da wannan duniyar da muke ciki.  Wadannan halittu da a Turance ake kira Aliens, inji masu wannan ra’ayi, su ne ke yin tasiri wajen haddasa wadannan hadarurruka masu ban al’ajabi.  Suka ce su ne masu sace jiragen suna kai su duniyarsu.  Su ne ke sulmuyar da jiragen ruwa can cikin karkashin teku, su hana masu bincike ganin buraguzansu.  Wadannan halittu, inji masu wannan ra’ayi, tabbatattu ne ba tatsuniya ba.  Domin akwai labarai da ke nuna samuwarsu a wasu sasannin Amurka, shekaru masu yawa da suka wuce.

Abu na biyu da ke haddasa hakan, a cewar masu wannan ra’ayin, su ne jinsin aljanu, ko kuma rauhanai, kamar yadda aka fi saninsu a kasar Hausa.  Suka ce bayan wadannan halittu na Aliens, su ma jinsin aljanu na da hannu wajen haddasa ire-iren hadarurrukan da labarinsu ya sha kan duniya. Sai abu na uku, wanda ya kunshi wasu halittu ko abubuwa masu ban mamaki da dan Adam ba ya iya hankalta balle ya fahimci yadda tasirinsu yake.  Suka ce wasu irin halittu ne ko abubuwa da ke yawo a sararin samaniya, lokaci-lokaci, kuma akwai tabbacin suna yin tasiri wajen haddasa hadarurrukan jiragen sama a lokuta da dama.  Wadannan halittu ko abubuwa, wadanda a Turance ake kira Unidentified Flying Objects (UFO), su ne dalilai na uku da a cewar masu wannan ra’ayi, ke haddasa wadannan hadarurruka masu ban al’ajabi.  Sai abu na hudu, wanda shi ne na karshe.

Wannan abu kuwa, shi ake kira Paranormal.  A ka’idar ilimin kimiyya, malamai sukan kira shi: Suspension of the Laws of Physics.  Wannan yanayi wani irin tsari ne da ke nuna faruwar abubuwa, a fili, amma kuma babu wata alama ta kusa ko ta nesa da ke iya zama musabbabi kan faruwar abin.  Idan aka samu wannan yanayi, a kan kira shi Paranormal  –  ma’ana duk wani yanayin da ke haddasa abubuwa su faru, a fili ana gani, amma a kasa gane dalilin faruwarsu bayan kaddamar da binciken kimiyya a kansu, haka suke kiran yanayin.  A takaice dai sun sallama wa “dabi’a” kenan, kamar yadda sauran malaman kimiyya ke cewa.  Wannan ke nuna lamarin ya sha karfinsu.  To amma tunda ba yarda galibinsu suka yi da Allah ba, sai su kauce, su bashi wannan suna.  To, wannan dalili na hudu, a cewar masu wannan ra’ayi, yana cikin dalilan da ke haddasa hadarurruka a wannan kusurwa ta shedanu.  Kuma ma, su suka bai wa wannan mahalli wannan suna, kamar yadda bayanai suka gabata a baya.

Wadannan su ne kashi na farko cikin ra’ayoyi hudu da marubuta suke ganin suna da hannu wajen faruwar abubuwa a kusurwar shedanu.  Sai nau’in ra’ayi na gaba.

Malaman Kimiyya

Kafin mu yi nisa, yana da kyau mu san cewa a ka’idar bincike na kimiyya, musamman ma ta zamani, ba a yarda da duk wani abin da ke haddasa faruwar abubuwa, wanda kuma ba a jinshi ko ganinshi ko iya taba shi ba.  Kuma ba a yarda da cewa ga wani abu na faruwa amma an rasa dalilin faruwarsa ba.  Wannan, a cewarsu, bazai taba yiwuwa ba.  Da wannan, masu binciken Kimiyya kan ire-iren hadarurrukan da ke faruwa a wannan bigire na kusurwar shedan, suka ki yarda da ra’ayin malaman farko, masu ta’allaka dalilin faruwar ga jinsin aljanu ko wasu halittu masu shigowa wannan duniya tamu daga wasu duniyoyin, ko kuma wadansu halittu da ke shawagi a sararin samaniya (Unidentified Flying Objects – UFO)  ko ka’idar Paranormal ba.  Wannan, a cewarsu, duk hauragiya ce da rashin kan gado.

A nasu mahangar, malaman kimiyyar zamani suka ce akwai a kalla dalilai guda biyar masu haddasa wadannan matsaloli.  Dalilan farko da na biyu su ne: yawan jiragen sama da na ruwa masu zirga-zirga tsakanin dirkokin wannan kusurwa.  Da kuma mummunar yanayin hazo ko iska ko ruwan sama, watau Terrible Weather Condition da ke samuwa a wannan wuri.   Wadannan na cikin abin da ke haddasa samuwar hadarurruka da yawan maimaituwansu lokaci-lokaci.  Da aka tambayesu kan abin da ke haddasa bacewar jiragen kuma fa?  Mun yarda yawan zirga-zirga da kuma samuwar mummunar yanayi na haddasa hadari, amma me yasa idan aka yi hadarin, sai kuma a rasa buraguzan jirgi?  Sai suka ce dalilai na uku da na hudu da kuma na biyar ne ke haddasa bacewar wadannan jirage ko buraguzansu, har a wayi gari ba a ganinsu idan hakan ta faru.  Ga bayani kan haka filla-filla, dalla-dalla, sanka-sanka.

Dalili na uku suka ce shi ne wani irin sinadarin kumfa da ke samuwa a saman manyan tekunan duniya, irin su tekun Atilantika da sauransu.  Wannan sinadari mai dauke da yanayin kumfa da a Turancin Kimiyya ake kira Methane Hydrates, kumfa ne da ke samuwa a saman teku, mai dauke da iska a cikinsa, wanda kuma samuwarsa a saman tekun ke yin tasiri wajen rage nauyin ruwan da ke tekun.  Wannan nauyi na ruwan teku da ake kira Water density, karfinsa ne ke iya daukan jirgin ruwa da abin da ke dauke a kansa, don yin shawagi daga gaba zuwa gaba.  Idan karfinsa ya ragu sanadiyyar samuwar wannan kumfa mai dauke da sinadaran Methane Hydrates, sai nauyin ruwan ya ragu, ta hanyar komawa kasa da yake yi, don baiwa kumfar damar mamaye ilahirin bigirensa.  Da zarar jirgin ruwa ya doso wuri irin wannan, inji wadannan malamai na kimiyya, sai ya fada cikin wannan kumfa, inda kuma babu iya mizanin nauyin ruwan da yake bukata don wuce wannan wuri.  Nan take sai kumfar yayi kasa, tare da jirgin, sauran ruwan tekun kuma ya maye saman jirgin, har a kasa samun buraguzansa.  Wannan hujja kan jiragen ruwa kenan.  Amma ta yaya aka yi hakan ke shafan jiragen sama?  Nan ma suna da ta cewa.

Tasirin wannan sinadari na Methane Hydrates a kan jirgin sama kuma shi ne, idan ya taso a saman teku, ya mamaye iya bigiren da zai iya mamayewa, bayan nauyin ruwan tekun da yake ragewa, har wa yau, suka ce yana yin tasiri wajen rage nauyin iskar da ke sararin samaniyar tekun ma, watau Air Density kenan a Turancin kimiyya.  Idan kuma aka samu raguwar iskar da ke sararin samaniya, wacce ke tasiri wajen karfin dagawa da saukan da jirgi ke yi, to nan take jirgi na iya rasa daidaituwarsa a sama, har ya rikito kasa.  Kuma tunda a saman teku ne, da zarar ya fado cikin ruwan, nan take wannan kumfa ta Methane Hydrates na iya sulmuyar dashi karkashin tekun, ba tare da bata lokaci ba.

- Adv -

Hujja ta hudu da ke haddasa faruwan hadarurruka a wannan kusurwa ta shedanu a cewar Malaman Kimiyya, ita ce mahaukaciyar guguwa mai dauke da iska da ruwan sama, irin wacce kasashen Amurka da Karibiyan ke fama da ita a duk shekara, watau Hurricane, a harshen Turanci.  Tasirin wannan mahaukaciyar guguwa yana samun jiragen ruwa ne kadai, banda jiragen sama.  Suka ce mahaukaciyar guguwa na iya kife jirgin ruwa, tare da sulmuyar dashi nan take, a kasa ganin dukkan sassansa.  Da aka tambaye su hujja, sai suka ce akwai jirgin ruwan kasar Faransa tafkeke, mai suna Francisco de Bobadilla, wanda mahaukaciyar guguwa ce ta kifar tare da sulmuyar dashi nan take, ko gawarsa ba a gani ba!  Wannan lamari ya faru ne cikin shekarar 1502, kuma har zuwa yau ba a samu buraguzan jirgin ba.   Malaman Kimiyya suka ce in har haka zai kasance ga wannan babban jirgi, to hakan na iya kasancewa ga galibin kananan jiragen ruwan da suka ta bacewa a wannan Tsibiri da ke kusurwar shedanu.

Sai hujja ta karshe, wacce ke da dangantaka da abin da suke kira Magnetic Poles, a Turancin kimiyyar karkashin kasa.  Malaman Kimiyya suka ce bincike ya nuna cewa wannan duniya tamu, daga sararin samaniya zuwa can karkashin kasa, akwai wasu sinadaran maganadisu (Magnetic Waves), da ke manne da dirkokin duniya, watau Earth Poles a bangaren gabas da bangaren yamma.  Wannan sinadarin maganadisu yana yin tasiri ne wajen janyo duk wani abu mai nauyi da ke saman iska a wannan jihohi na duniya.  Wannan ya hada da jirgin sama da kuma na ruwa.  Da suka kaddamar da bincike, sai ya tabbata cewa wannan mahalli na kusurwar shedanu da ke tsakanin tsibirin Bamuda da sauran jihohi, yana zaune ne daidai inda wadannan dirkokin duniya a bangaren yamma suke.  Wannan, a cewar Malaman, bazai rasa tasiri ba wajen haddasa hadarin jiragen sama da na ruwa.  Suka ce tunda wuri ne mai yawan zirga-zirgan abin hawa, haka na iya kasancewa.  Wadannan, a takaice, su ne ra’ayoyin Malaman Kimiyya kan dalilan da ke haddasa wadannan hadarurruka masu ban mamaki da ake gani amma aka kasa fahimta.  Sai nau’in ra’ayi na uku.

Ra’ayin ‘Yan Zahiri

Masu nau’in wannan ra’ayi na kira su  “’Yan Zahiri” ne domin sun sha bamban nesa ba kusa ba, da masu sauran ra’ayoyin da suka gabata.  Shugaban masu wannan ra’ayi shi ne Farfesa Lawrence Kusche da ke Jami’ar Arizona a kasar Amurka.  Malamin Jami’a ne mai sha’awar binciken kwakwaf.  Kuma kamar yadda bayanai suka gabata a baya, shi ya fara zuwa da sabon tsarin bincike kan dalilan da ke haddasa wadannan hadarurruka.  A cewar Kusche, duk abubuwan da ake ta fada shirme ne.  Babu wani abu sabo da ya raba irin hadarin da ake samu a wannan wuri da wanda ake samu a sauran wuraren da ke wasu nahiyoyin duniya.  Ya yi wannan tsokaci ne cikin littafinsa mai suna The Bermuda Triangle Mystery: Solved, wanda ya rubuta cikin shekarar 1975.

Farfesa Kusche yace dukkan cece-kucen da ake ta yi kan wannan kusurwa na shedanu shirme ne.  Babu wani abu sabo da ya cancanci a tsaya ana mamaki kansa.  Da farko yace idan aka kwatanta yawan jiragen sama da na ruwa da ake ikirarin sun bace a tsibirin Bamuda, da wadanda suka bace a wasu wuraren, musamman bakin gaban tekun kasar Jafan, sai a ga ma ba wani yawa bane dasu.  Na biyu kuma yace, idan aka sake la’akari da irin yanayin zirga-zirgan da jiragen sama da na ruwa ke yi a yankin, har wa yau, za a ga ba wani abin mamaki don an samu yawan hadarurrukan da ake ta kukan suna faruwa lokaci-lokaci.  Abu na uku, Farfesa Kusche yace akwai karin gishiri cikin labaran da ake bayarwa ma.  A cewarsa, wasu hadarurrukan basu faru ba kamar yadda ake ta ikirari; akwai karin gishiri don labarin yayi dadi.  Na hudu, yace akwai karancin bincike yayin da wani hadari ya faru.  Yace sau tari idan wani jirgi yayi hadari, aka rasa inda buraguzansa suke, nan take ‘yan jaridu da masu bincike zasu yi ta ihun sanar da duniya cewa ga abin mamakin da ya sake faruwa.  Amma bayan tsawon lokaci, ko da an gano buraguzan, basu sani balle su juya akalar labarin da suka bayar a farko.

Abu na biyar, Farfesa Kusche yace wasu labaran da ake bayarwa na hadarin wasu jirage musamman na sama, karya ne, basu faru ba.  Misali, akwai labarin da ya yadu a littattafai da bakunan masu labarai kan wani jirgi da aka ce ya fadi a farfajiyar tsibirin Daytona, watau Daytona Beach, cikin shekarar 1937.  Yace bincike ya tabbatar da cewa wannan labari karya ne, hadarin bai faru ba.  A karshe dai yace duk labaran da ake ta bayarwa kan wannan tsibiri, ko dai karairayi ne, ko kuma an yi karin gishiri a kan labarun gaskiya, ko kuma rashin fahimta ce kawai da son kambama abin da bai cancanci kambamawa ba.  Dankari!  Wani zancen sai malaman jami’a.

A Ina Gaskiyar Take?

Bayan koro bayanai kan dukkan wadannan nau’ukan ra’ayoyi da marubuta suka tafi a kai na dalilan da ke haddasa wadannan hadarurruka a tsibirin Bamuda, mai karatu zai so sanin wanne ne gaskiya daga cikinsu?  To kafin mu yi nisa, kuma kamar yadda duk wani musulmi ya sani ne, sanin hakikanin abin da ke faruwa a wurin, da ma sauran wurare, sai Allah.  Abin da zai iya taimaka wa mai karatu fahimtar burbushi ko kamshin gaskiya dangane da wannan wuri, shi ne yin la’akari da yanayin labaran.  A iya bincike na, zan iya cewa dukkan ra’ayoyin da suka gabata na da wani kamshin gaskiya kan dalilin da ke haddasa hadarurrukan, komai kankantarsa kuwa.  A ra’ayin farko, wanda shi ne abin da yafi shahara, ma iya cewa ba mamaki idan aka samu wasu halittu masu yin tasiri wajen faruwar haka.  Da ikon Allah komai na iya faruwa.  Kuma a bayyane yake cewa duk abin da ya faru, yana iya samun dalilan fili da na boye.  Don haka ma iya daukan ra’ayin farko a matsayin wasu cikin dalilan da suke na boye ne, da ke haddasa hakan, ba tare da yarda da cewa hakikanin wadannan halittu ne ke haddasa su ba, a hakikatan.  Domin sanin wannan kam sai Mai duka.

Idan muka koma kan ra’ayin malaman kimiyya, ba abin da hakan zai nuna mana illa dalilan bayyane.  Babu tantama cewa za a iya samun dukkan dalilan da malaman kimiyya suka kawo a matsayin hujja, amma na bayyane.  Domin su basu yarda da duk abin da ba a ganinsa ba, ko jinsa, ko kuma taba shi.  Amma a ka’ida ta rayuwa kuwa, idan sun yi dogon nazari, zasu samu da dama cikin abubuwan da ke haddasa faruwar abubuwa ba a ganinsu.  Misali idan muka dauki “hankali”, sai mu ga wani abu ne wanda ba a ganinshi, sai dai kuma yana cikin abin da ke tafiyar da dan adam gaba daya.  To a nan, ma iya daukan hujjojin malaman kimiyya a matsayin bayyanannun dalilan da ke haddasawa.

A bangaren karshe kuma, dole ne mu yarda cewa akwai karin gishiri cikin galibin labaran da ake bayarwa.  Ba wai Farfesa Kusche kadai ba, galibin marubutan su ma sun yarda akwai wannan.  Wasu labaran ma basu faru ba, kamar dai yadda bayanai suka gabata.  To amma kuma baza mu dauki bangaren ra’ayin Kusche ba da ke cewa: “Babu wani abu sabo da ke faruwa a wajen.”   Samuwar hakan ne ma ya haddasa shaharar wannan bigire na duniya a kan sauran bigirori inda makamantan hakan ke faruwa.  In ba haka ba, akwai wurare da dama da ire-iren wadannan abubuwa ke faruwa, amma basu shahara ba a duniya.  Don haka, akwai abubuwan mamaki masu faruwa, sai dai sun sha bamban da yadda ake ruwaito su.  Wannan kuma dabi’ar dan adam ce wajen ruwaito labara; da wahala ya bayar dashi yadda yake a hakikaninsa, musamman idan abu ne mai yawan maimaituwa cikin yanayin da a zahiri ya sha karfin tunaninsa. Dan adam ya gaji kambama abu, idan ya birge shi, ko ya firgitar dashi fiye da duk wani mai firgitarwa.

Har wa yau kuma babu wani tabbataccen dalili – na boye ko na fili – da aka gano cewa shi ne ke haddasa wadannan hadarurruka.  Abu na karshe da ya kamata mu sani kuma shi ne, don an kasa samun wani dalili kwaya daya ko sama da daya da ke haddasa hakan, ba shi ke nuna cewa babu ba.  A a, watakila yanayin binciken da ake gunadarwa ne ya kasa gano hakan.  Ko dai saboda wata hikima ta Ubangiji, boyayya, ko kuma lokaci ne bai yi ba.

A dai ci gaba da zuwa rafi…!

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Nazir says

    Allah dae ya kara maka ilimi baban sadiq.

Leave A Reply

Your email address will not be published.