Dandatsanci: Wani Sabon Salon Yaki Tsakanin Kasashen Duniya (3)

Kashi na uku cikin jerin kasidun dake nazari kan sabon salon yakin kutse a tsakanin kasashe. A sha karatu lafiya.

165

Tabbaci…

Bayan tsawon lokacin da kowace kasa daga cikin kasashen Turai da Amurka ke dauka wajen aiwatar da aikin Dandatsanci ta hanyar kwararrun ‘yan Dandatsa da ake ji dasu a warwatse a sauran kasashe, tuhuma bai ragu ba kan cewa lallai kasashen Rasha da Sin ne ke cin karensu ba babbaka a wannan sabuwar filin dake Giza-gizan sadarwa ta duniya.

Cikin wani hira na musamman da jaridar Global Post ta yi da shi, Darakta Dan McWorther, shugaban kamfanin Mandiant dake kasar Amurka, ya nuna cewa lallai ko shakka babu babban harin dandantsanci da aka kai wa manyan kamfanonin kasuwanci da muhimman hukumomin kasar Amurka a watan Maris na wannan shekara ya samo asali ne daga kasar Sin.  A matsayinsa na kwararre a fannin tabbatar da lafiya da bayanai da hanyar sadarwa (Information Security Expert), McWorther ya nuna cewa, wani babban abin bakin ciki ma shi ne, duk ‘yan Dandatsan da ke kai wa kasar Amurka hari ta hanyar sadarwar kwamfuta da ma sauran kasashen Yamma, gwamnatin kasar Sin ce ke tallafa musu; ita ce ke basu mafaka, ita ce ke basu kayan aiki, hatta da inda za su zauna a yayin da suke aikinsu.  Yace ba wannan kadai ba, akwai sashe na musamman da hukumar sojin kasar Sin ta bude mai suna: Unit 61398.  Wannan sashe na musamman, inji Darakta McWorther, shi ne ke lura da yadda hukumar sojin kasar ke horar da zaratan samarin jami’a da na sakandare masu hazaka a fannin kwamfuta, tare da shirya gasa don neman fitattu wadanda hukuma za ta rika amfani dasu wajen samar da bayanai ko aiwatar da duk wani aiki na musamman da a ganin gwamnati ci gaban kasa ne.

Wannan kungiya da Unit 61398 ya samar shi ne APT1, kuma shi ne ke lura da ayyukan dandatsanci wadanda suka shafi satar bayanan sirri, da hakkin mallaka kan harkar fasahar kere-kere, da sace masarrafan sirri na kwamfuta, da duk wasu bayanai da kamfanonin kasar Sin ka iya amfani dasu wajen habbaka kasuwanci da ci gaban tattalin arzikin kasa.  Wadannan bayanai na tuhumce-tuhumce na cikin wani kundi na musamman da kamfanin Mandiant ya fitar watanni uku da suka gabata mai shafuka 171, wanda sakamakon wani bincike ne na kwakwaf da kamfanin yayi kan wannan kungiya, ciki har da hotunan sheda, da lakubban wasu daga cikin wadanda ke aiwatar da wannan al’amari a madadin hukumar kasar Sin.  Bayan wannan kungiya ta APT1, a cewar Darakta McWorther, akwai wasu makamantanta sama da ashirin da ke aiki a karkashin kasa dare da rana safe da yamma.  Kuma suna warwatse ne a wasu kasashe, bayan wadanda ke zaune a kasar Sin.  An kuma kiyasta cewa sun kai wa shafukan yanar sadarwa sama da 141 hari cikin watan Maris da ya gabata.  Hukumar kasar Sin dai ta karyata dukkan wadannan zarge-zarge, tare da nuna cewa ba ta ma san ana yi ba, wai kunu a makwabta.  Tace har yanzu bata samu wani bayani daga wata kasa ko kungiya a hukumance, da ke zargin cewa ita ce ke aiwatar da wadannan abubuwa ta karkashin kasa ba.

A nata bangaren kuma, kasar Rasha Kura ce sha-zargi.  Ba kasashen Amurka da Ingila kadai ba, hatta kasar Isra’ila na zargin kasar Rasha da taimaka wa kasashen Larabawa da kwararrun ‘yan Dandatsa don daukan fansa a kanta a wasu lokuta.  Sai dai kuma, kamar yadda masu iya magana ne kan ce: Gwano ba ya jin warin kanshi.  Duk da cewa abu ne sananne duk duniya babu wata kasa da ta kai kasar Rasha yawan kwararru kan harkar kwamfuta, musamman a bangaren gina manhaja da masarrafanta, amma tabbatattun bayanai a baya sun nuna cewa lallai kasar Isra’ila na amfani da ‘yan Dandantsan kasar Rasha ita ma, wajen cinma burace-buracenta na siyasa a fagen siyasar duniya.  Wannan ke nuna cewa duk da yawan wadannan kwararru a kasar Rasha, hukuma ba ta da wani iko mai karfi a kansu wajen tirsasawa don a aiwatar da dandantsanci.  Bayan haka, su ‘yan Dandatsa galibinsu ‘yan haya ne; duk mai wuri na iya daukansu, nan take za su zo da wuri, su bude wuri, don biya masa bukatarsa.  Da wannan za mu ga cewa hatta kasar Amurka da Ingila duk suna amfani da wadannan mutane, don cinma wata manufa ta siyasa ko tattalin arziki, a boye.  To, don me za a rika zargin Rasha da Sin kadai?

Wata Sabuwa…

- Adv -

Sanadiyyar cece-kuce da ya zama ruwan dare cikin sauran shekarun da suka gabata kan wannan lamari, kwararru a fannin kwamfuta sun dage wajen neman sanin hakikanin abin da ke faruwa kan wannan lamari.  Domin, a kididdiyar wasu gidajen yanar sadarwa masu bincike kan fannin kariyar bayanai da inganta tsarin sadarwar zamani suka fitar, alkaluman bayanai sun nuna cewa babu abin da aka fi yinsa a kowane dakika na rayuwarmu ta yau a giza-gizan sadarwa ta duniya irin aikin dandatsanci.  A kowane dakika, ko minti, ko sa’a, ko yini, ko dare, ko kwana, ko mako, ko shekara, ana gudanar da aikin dandatsanci babu kakkautawa a duniya.  Ko dai satar tsagwaron bayanai ne, ko satan manhajojin fasahar kere-kere da yadda ake sarrafa su, ko satar bayanan sirrin jama’a a kasahen da suka dogara kai tsaye da hanyar sadarwar zamani wajen gudanar da kasuwanci da siyasa.  Wani masani yace, a takaice dai, akwai ayyukan dandatsanci da ke gudanuwa a giza-gizan sadarwa ta duniya fiye da tunanin mutane.

Daga cikin hankoron kokarin fahimtar wannan matsala akwai wanda hukumar sadarwar tarho na kasar Jamus take yi a halin yanzu, inda ta bude gidan yanar sadarwa mai zaman kansa, dauke da manhajar kwamfuta da ke taimaka wajen sinsino irin hare-haren da ake kaiwa kwamfutoci a duniya ta hanyar dandatsanci.  Wannan hukuma mai suna: SICHERHEITSTACHO ta samar da manhajoji masu inganci wajen jure hare-hare, tare da iya sinsino irin zungurar da ake wa Iyayen Garke (Computer Servers) a ko ina ne a duniya.  Gidan yanar sadarwar na wannan adireshi: www.sicherheitstacho.eu. Kamar yadda mai karatu zai gani idan ya shiga, akwai bangaren da ke dauke da taswiran duniya, tare da dige-gien launukan ja, abin da ke nuna iya kamarin da hare-haren dandatsanci yayi a kasar da aka sa mata alama.  A kasan taswiran kuma akwai jadawali mai dauke da bangarori guda hudu. Bangaren farko na dauke da lokacin kai hari ne.  Daga awa, zuwa minti, har da dakika na lokacin da ake kai harin.  Mai karatu zai ga lokutan kai harin na caccanzawa, abin da ke nuna cewa a lokacin da yake kallo ne ake kai harin nan take, cikin kowane dakika.

A bangren jadawalin na biyu kuma zai Source, wato asalin inda harin ya fito.  A karkashin haka zai ta ganin sunayen kasashen da hare-haren ke faruwa ne.  Sai kuma bangare na uku mai dauke da mahallin da masu kai harin ke darkakewa, wato inda aka rubuta: Attack On.  Sai kuma bangaren karshe mai dauke da irin tsarin da mai kai harin ya bi, da tsarin da gidan yanar sadarwar ke amfani da shi wajen taskance harin da ake kaiwa.  Wannan shi ne bangaren Parameter kenan.  A zahiri wannan shi ne abin da mai ziyara a wannan gidan yanar sadarwa zai gani.  Duk bai shige shafuka biyar ba.  Amma a karkashin kasa, gidan yanar sadarwa ne tafkeke, mai dauke da manhajojin sinsino hare-haren ta’addanci ga kwamfuta a giza-gizan sadarwa ta duniya.

Wannan shafi dai ya fara aiki ne a watan Janairun wannan shekaru, kuma ya zuwa yanzu yana kan taskance bayanai masu muhimmanci kan wannan al’ada na ta’addanci.  Daga rahotannin da ya tara cikin watan Fabrairu, alkaluman bayanai sun tabbatar cewa kasar Rasha ta zo ta farko da yawan hare-hare.  Inda a cikin watan gidan yanar sadarwar ya taskance hare-hare 2,402,722.  Sai kasar Taiwan da tazo na biyu da yawan hare-hare 907,102. Na uku ita ce kasar Jamus da yawan hare-hare 780,425. Kasa ta hudu a yawan hare-hare ita ce kasar Yukrain da yawan hare-hare 566,531.  Kasar Amurka ta shallake kasar Sin, inda tazo na shiga da yawan hare-hare 355,341, ita kuma kasar Sin tazo na goma shabiyu, da yawan hare-hare 168,146.  A watan Maris da ya gabata kuma har wa yau kasar Rasha ce ta sake zama kasa ta farko da yawan hare-hare 2,450,063.  Sai kasar Jamus da yawan hare-hare 1,312,865. A wannan karo kasar Amurka ta zo ta biyar, da yawan hare-hare 450,931, inda kasar Sin ta zo na goma, daga cikin kasashe goma shabiyar da aka fi samun yawan hare-hare a duniya.

Abin da wannan alkaluman bayanai ke nunawa shi ne shahara da kuma watsuwar sannan sana’a ta dandatsanci a duniya, musamman a wannan zamani da harkokin kasuwanci suka fi dogaro da na’urori da hanyoyin sadarwr zamani, irinsu kwamfuta da fasahar Intanet, da wayoyin salula, da sauransu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.