Fasahar Sadarwa ta GPRS

Fasahar GPRS ce ke lura da tsarin aikawa da karban sakonnin hotuna da bidiyo ta siginar rediyon wayar salula. Duk da cewa wannan tsari bai bunkasa a tsakanin kamfanonin sadarwar wayar salula ba, saboda rashin hanyar sadarwa mai inganci, yana da kyau mu san me wannan fasaha take nufi. A sha karatu lafiya.

295

Tsarin sadarwa ta fasahar GPRS (wato General Packet Radio Service) ita ce hanyar da ta kunshi aikawa da kuma karbar sakonnin da ba na sauti ko murya ba, tsakanin wayar salula da wata wayar ‘yar uwarta ko kuma kwamfuta.  Wadannan sakonni da ake iya aikawa ta hanyar GPRS dai sune rubutattun sakonnin tes (SMS) ko Imel ko mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar wayar salula ko kuma tsarin kira ta hanyar bidiyo (video call) da dai sauransu.  Wannan tsari na sadarwa na cikin sabbin tsare-tsaren da wayoyin salular da aka kera cikin zamani na biyu (2nd Generation Phones) suke dauke dasu.  Kuma ita ce hanya ta farko da ta fara bayyana wacce ke sawwake sadarwar da ta shafi rubutattun sakonni da na bidiyo da kuma mu’amala da fasahar Intanet.

Amma kafin nan, tsoffin wayoyin salula na amfani ne da hanya kwaya daya wajen aikawa ko karbar dukkan nau’ukan sakonni.  Idan kana Magana da wani, to ko da an aiko maka rubutacciyar sako, baza ta shigo ba sai ka gama Magana sannan ta iso.  Idan kana son aikawa da rubutacciyar sako kuwa, ta hanyar aikawa da murya za ka aika, kuma da zarar ka fara aikawa, layin zai toshe, babu wanda zai iya samunka, sai lokacin da wayar ta gama aikawa, sannan za a iya samunka.  Wannan ya faru ne saboda wayoyin salula na zamanin farko (1st Generation Phones) na amfani ne da layin sadarwa guda daya tak.  Wannan tsari shi ake kira Circuit Switched Data (CSD).  Karkashin wannan tsari, kamfanin sadarwarka zai caje ka ne iya tsawon lokacin da sakonka ya dauka kafin ya isa, wanda kuma mafi karancin lokaci shi ne dakiku talatin (3o seconds).

To amma da tsarin sadarwa ta wayar iska na GSM ta bayyana, sai aka samu fasahar GPRS, wacce ke amfani da layin aikawa da karbar rubutattun sakonni kai tsaye tsakaninta da wata wayar ko kuma kwamfuta, idan ta Intanet ne.  Hakan kuma na samuwa ne musamman idan wayar na dauke da fasahar Wireless Application Protocol, wato WAP, wacce ka’idar da ke tsara sadarwa a tsakanin kwamfuta da wayar salula, ta hanyar wayar iska.  Karbar sakonnin tes ko Imel ko kuma mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar GPRS shi yafi sauki da kuma sauri wajen mu’amala.   Sai dai kuma wannan tsari ta GPRS na cikin nau’ukan hanyar sadarwa da kamfanin sadarwa ne ke bayar dasu, wato Network Service.  Wannan ke nufin idan wayarka na da WAP, ko kuma tsarin mu’amala da fasahar Intanet, to kana iya amfani da ita kai tsaye wajen shiga Intanet.  Kuma da zarar kayi haka, kamfanin sadarwarka zai caje ka kudin zama a kan layi.

- Adv -

Tsarin sadarwa ta GPRS na amfani ne da wasu hanyoyi masu zaman kansu wajen aikawa da sakonni.  Wannan tsari shi ake kira Multiple Access Method a Turance.  Ta amfani da wannan tsari, wayarka na iya amsar sakonnin Imel ko tes a yayin da kake Magana da wani.  Sai dai kawai ka gansu sun shigo.  Kana iya karbar rubutattun sakonni fiye da daya a lokaci guda.  Hakan ya faru ne saboda tsarin na amfani ne da hanyoyi fiye da daya wajen karba ko aikawa da wadannan sakonni.  Ba ruwansa da layin da kake karbar sakonnin kira na sauti, sam.  Sai dai kuma, mu a nan galibi, kamfanonin sadarwarmu na amfani da ita ne kawai don bayar da damar shiga ko mu’amala da fasahar Intanet.  Kamfanin sadarwa ta Glomobile da MTN duk suna da wannan tsari na GPRS, amma kamar yadda na zayyana a sama, idan ba wayoyin salula na musamman irinsu Black-berry ba, ba a iya amfani da ita sai wajen shiga Intanet kadai.   Amma a sauran kasashe ana amfani da wannan tsari wajen karba da aikawa da sakonnin tes, da sakonnin Imel da kuma yin hira da abokinka ta hanyar gajerun sakonni, wato Instant Chat. 

Dangane da nau’in wayar salula, akwai yanayin sadarwa iri uku ta amfani da fasahar GPRS.  Akwai wayoyin salula masu karfin karbar kira na sauti ko murya da kuma karba ko aikawa da sakonnin tes, duk a lokaci guda.  Ma’ana, kana Magana, sannan kana rubuta sakon tes, idan ka gama rubutawa, ka aika dashi nan take, ba tare da layin da kake Magana da abokinka ya yanke ba.  Wadannan wayoyin salula sune ke martaba na farko, a sahun wayoyin salula masu amfani da fasahar GPRS, wato Class A kenan.  Sai dai kuma basu yadu sosai ba, watakil sai nan gaba.  Sai kuma wadanda ke biye dasu, wato Class B, wadanda idan kana amfani da fasahar GPRS, ta amfani da Intanet ko sakonnin tes, sai kira ya shigo, to wayar zata tsayar da wancan layin da kake karbar sako ko kake mu’amala da Intanet, don baiwa layin da ke karbar kira damar sadar da kai da wanda ke kiranka.   Wadannan sune kusan kashi tamanin cikin dari na ire-iren wayoyin da ake amfani dasu a yanzu.  Sai nau’i na karshe, wato Classs C, wadanda idan kana son amfani da fasahar GPRS, to dole sai ka shiga cikin wayar, ka saita ta da kanka.  Da zarar ka saita ta, to  ba wanda zai iya samunka, sai in ka gama abin da kake, ka sake saita ta zuwa layin karbar kira na sauti ko murya (voice call).

Wannan fasahar sadarwa ta GPRS dai na cikin fasahohin da suka kara wa wayar salula tagomashi da kuma karbuwa a duniya. Domin ta sawwake hanyoyin yadawa da kuma karbar sakonni ba tare da mushkila ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.