Hadarin Amfani da Wayar Salula Yayin Tuki

Mu’amala da wayar salula a halin tukin mota ko babur abu ne mai hadari matuka. A wannan mako za mu dubi abin da masana suka ce kan haka. A sha karatu lafiya.

361

Duk da cewa galibin mutane in ba duka ba, suna sane da hadarin da ke tattare da bugawa ko amsa wayar salula yayin tuka mota ko babur ko hawan keke, har yanzu akwai da dama cikin mutane da basu aiki da wannan doka.  Hakan na faruwa ne sanadiyyar rashin lura da kuma yawan mantuwa.  Wasu na ganin ai ba wani abu bane, domin suna kallon hanya da kyau, kuma ba a shagalce suke ba.  Wasu kuma su ce ai suna amfani da lasifikar kunne, watau  Handsfree Speaker, wanda ke nuna ba sai sun rike wayar da hannunsu ba, sai dai kawai su yi ta Magana.  Ga wasu kuma, sai su sanya wayar a tsarin Speaker Phone, wanda ke sawwake Magana da abokin hira ba tare da sun rike wayar ba; suna jin muryar abokin hulda, tare da bashi amsa cikin  sauki.

Duk da haka, wadannan ba dalilai bane, sam.  Domin a yayin da kake tuki, musamman a kasashe masu tasowa irin su Nijeriya (musamman inda ba kowa ke bin dokar hanya ko tuki ba), dole idan kana tuki ka rika lura da wadanda ke gabanka, da kuma wadanda ke bayanka.  A takaice dai dole ne ka rika lura da tukin da kake yi, da kuma tukin da wasu ke yi a hanyar da kake tafiya.  Dole ka san cewa wanda ke gabanka na iya taka burki kai-tsaye ba tare da saninka ba, sanadiyyar wata dabba ko wani abu da ka iya faruwa nan take.  Haka a yayin da kake son wuce wanda ke gabanka, dole ne ka rika lura da wanda ke bayanka;  ta yiwu a guje yake, yana shirin wuce ka, idan baka lura ba, kana budawa sai ku gwabza.  Idan wannan shi ne tsarin tuki, ina direba ya samu dalilin amfani da wayar salula a yayin da yake tuki?

Domin a lokacin da kake Magana, hankalinka fa bay a kan hanyar, gululun idonka ne ke kallon hanya, ba ganinka ba.  Dukkan hankalinka zai koma ne kan wanda kake Magana dashi, kana mai sawwara irin maganan da kuke yi, a kwakwalwarka.  Hatta tsarin tafiyarka na iya canzawa ba tare da ka sani ba, musamman idan  a babban hanya kake tafiya.

- Adv -

Wani abin lura har wa yau shi ne, galibin hanyoyinmu basu da kyau.  Ramuka sun cika su, sannan ga rashin kwarewan tuki wajen galibin mutane musamman ma cikin cinkoso a manyan biranenmu.  Wannan ya tilasta wa mai tuki ajiye wayarsa cikin aljihu, ko wani wuri dabam inda ba zai fitinu ba idan aka bugo ko kuma ya ga sunan wanda ke bugowa.  Idan kuwa ya zama dole sai ka dauki wayar mai bugowa, kana da damar janyewa daga kan hanya, ka tsaya ka gama maganarka, sannan ka ci gaba da tafiya.  Idan mai tuki yayi haka, shi kanshi zai fi samun natsuwa da gamsuwa.  Amma idan kana cikin tuki kuma kana Magana da wani a waya, to dayan biyu ne; ko ya zama ya dauke maka hankali, ka samu matsala da tukin da kake yi, ko kuma hankalinka ya koma kan tukin, ba tare da wanda kake Magana dashi ya samu tattaruwan hankalinka waje guda ba.

A karshe, wani bincike da wani gungun masana daga Jami’ar Uta ya gabatar, ya nuna cewa da dama cikin masu tuki kan amsa waya a halin tukinsu, wanda bai dace ba.  Da kuma cewa hakan na haddasa hadari musamman a manyan hanyoyi.  Don haka ya kai direba mai tuka wani ko kanka ko kuma dauke da fasinja, ka yi wa kanka adalci ta hanyar daina wannan dabi’a.  Masu wannan bincike sun nuna cewa wannan dabi’a ce mai wahalar kawarwa, amma a hankali ana iya ragewa.

Wannan tasa masu kera wannan fasaha ta wayar salula ke sanya dokar hana buga waya a wurare da kuma halayya dabam-daban.  Daga cikinsu akwai asibiti, da bankuna da wuraren ibada da kuma yayin tuki.  Idan kana son ka koma gida iyalinka su ganka kai ma ka gansu, ka samu biyan bukata a rayuwarka, to lallai ka daina buga waya a yayin da kake tuki.  An san akwai kaddarar Allah, amma idan aka gane illar abu, to dole ne a guje masa.  Don shi ma gujewar na cikin kaddara.  Idan aka ki, har kuma mummunar sakamakon hakan ya shafi mai aikatawa, danganta hakan da kaddara ya zama ganganci.

Allah Ya tsare mu baki daya, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA says

    MASHA ALLAH

Leave A Reply

Your email address will not be published.