Hanyoyin Inganta Al’umma a Kimiyyance (2)

A yau ga kashi na biyu kuma na karshe cikin jerin kasidun da muke gabatarwa kan ciyar da al’umma gaba a fannin kimiyya. A makon jiya mun kawo kashi na daya.

319

Fannoni Masu Muhimmanci

Ga duk wanda ya dubi al’ummar Najeriya gaba dayanta, da al’ummar arewacin kasar nan musamman, ya san lallai muna da matukar bukatuwa zuwa ga wasu fannoni na musamman da suka shafi ilmi, wadanda ko dai samuwarsu ne zai kawo mana ci gaba kai tsaye, ko kuma ta hanyar samuwarsu rayuwa za ta inganta har a karshe a samu ci gaba bayyananne.  Muna da bukatuwa a fannin likitanci a kasar nan.  Muna da bukatuwa zuwa ga kwararrun likitoci a kasar nan.  Kamar yadda Dakta Solomon Anyegwu, shugaban kungiyar Masu Lura da Muhalli na kasa ya sanar da manema labaru a shekarar 2012, cikin mutum miliyan 150 da kasar nan ke dasu a kalla, likitocinmu guda dubu 35 ne!  Wannan ke nuna kowane likita daya zai lura da marasa lafiya dubu 3,800 kenan, da a ce kowa zai kamu da rashin lafiya a lokaci guda.  Wannan ko kusa bai yi ba da ka’idar Majalisar Dinkin Duniya da yace a samu likita guda ya rika lura da mutane 600.

Bayan fannin likitanci, fannin kere-kere ma yana matukar bukatar kwararru na musamman, musamman a arewacin Najeriya, wadanda za su dada inganta mana sana’o’inmu da muka tashi muka ga kakanninmu a kai.  Babban abin bakin ciki shi ne yadda muka wayi gari kowa ya kaurace wa sana’o’in gargajiya da muka gada daga iyaye.  Wadanda suka gada suna yi kuma sun kasa inganta su.   Misali, baa bin mamaki bane har yanzu ka ga makera na amfani da kayayyakin aiki irin na baya.  Hakan ba aibu bane dari bisa dari, amma da za a inganta sana’ar, ta hanyar amfani da kayayyakin zamani, wannan zai dada jawo kwastoma, ya kuma sawwake wa mai sana’ar hanyoyin kere-kerensa.  Sana’o’i irin su kira, da saka, da rini suna da matukar amfani wajen gina al’umma; ko dai wajen samar da sana’a ko inganta rayuwa ta hanyar samar da hanyoyin more rayuwa.

Har wa yau muna da karancin malamai a dukkan wadannan fannoni a makarantunmu, musamman a fannin kere-kere. A wani bincike na musamman da wani malamin jami’a yayi a jihar kogi, yace ba abin mamaki bane ka samu dalibin da ke karanta fannin kere-kere musamman a fannin karafa, amma bai san bambancin da ke tsakanin noti (Nut) da sandar noti (bolt) ba.  Duk da cewa wannan bangare ne da ya shafi hukuma, amma mu kanmu ba mu mayar da hankali wajen karatu. Domin bincike ya nuna cewa duk yadda al’umma ko wani yanayi ko dama ta baci, idan mai nema ya mayar da hankalinsa, ya sa abin a ransa, zai dace.

Duk Kwakwalenmu Iri Daya ne

Cikin shekarun da nayi ina rubutu a wannan shafi na sha samun tambayoyi kan yadda turawa ke samar da na’urori masu aiwatar da abubuwa cikin mamaki da al’ajabi, da cewa: “Shin, wannan ba sihiri ne suke yi ba kuwa?”  Haka ma cikin shirin da Sunnah TV ke shiryawa wanda suke hira da ni kan hanyoyin sadarwa, daga cikin masu tambaya akwai wanda ya yi tambaya makamanciyar haka, sadda na gama bayani kan tsarin sadarwar wayar iska, da fasahar Bluetooth, da Infra-red da dai sauransu.   Suna ganin ba abu bane mai yiwuwa ace ka kira mutum a waya daga garin Kaduna, wanda kake kira kuma yana wata kasa ko wata jiha daban, cikin ‘yan dakiku wayarka ta fara ruri tana kiransa, kuma ace tsakanin sadda ka latsa wayarka ka fara kiransa, zuwa lokacin da kiran ya shiga wayarsa, sai da na’urar sadarwa ta dauki bukatarka zuwa rumbun bayanan kamfanin wayarka, kamfanin wayarka kuma ta cilla wa kamfanin wayarsa.  Daga nan kuma kamfani wayarsa ya nemo jiha ko bigiren da mai waya yake, kafin ta sadar masa.  Shin, wannan ba sihiri bane kuwa?

Amsar da nake baiwa masu tambaya makamancin wannan ita ce, tsari irin wannan, wanda ke samar da na’urorin kere-kere na sadarwa ko na safara, ko na gine-gine, duk ba sihiri bane.  Ilimi ne tsantsa!  A nan ba ina wanke turawa bane cewa ba su yin sihiri, ko kadan.  Suna yi. Ba ma su kadai ba, kowace al’umma tana da irin gargajiyarta, wanda a ciki ba a rasa wani nau’i na surkulle ko sihiri.  Amma a wannan bangare babu wani abu wai shi sihiri.  Ilimi ne kawai tsantsa.  Abin da ke tabbatar mana da hakan kuwa shi ne, akwai da yawa daga cikin bakaken fata da suka koyo wannan nau’in ilimi.  Da akwai wani nau’i na sihiri a ciki da tuni sun sani.  Kuma da sun yada shi ga al’umma, ko dai don a kauce masa, ko kuma don abin da suka koyo kenan.

Wani abin mamaki ma shi ne, galibin wadannan na’urori da ake kerawa musamman a fagen sadarwa, duk za ka samu asalin wadanda ke aiki a kansu ba turawa bane, bakaken fata ne.  Idan ka je kamfanin Apple, da kamfanin Microsoft, da kamfanonin kera motoci irin su Honda, da Toyota, da Ford Motors, duk za ka samu galbi bakaken fata ne.  Cikin shekarar da ta gabata tashar talabijin CNN tayi hira da wani matashi dan Najeriya, haifaffen jihar Sokoto, wanda ke aiki a kamfanin BMW da ke kasar Jamus.  Daidai lokacin kamfanin ya fitar da wata nau’in mota kirar BMW wacce kowa ke yabawa.  Da bincike yayi nisa, sai aka gano ashe wannan matashi mai suna Zailani Aliyu ne ya zana asalin kwarangwal din motar gaba dayanta.  Haka ma sashen Hausa na BBC ya taba hira da wani bawan Allah da ke aiki a wani kamfanin kera motoci da ke kasar Jamus, wanda Injiniya ne, masanin makaman kera motocin zamani. Bahaushe ne dan Najeriya.  Ire-iren wadannan mutane suna da yawa, ba a jin ko duriyarsu, saboda dadewarsu a kasashen waje, musamman sanadiyyar yadda tsarin mulki da shugabanci ya tabarbare a kasarmu.

- Adv -

Mu dawo kan zancenmu na sihiri.  Ba abin da ke taimakawa wajen samuwar ire-iren wadannan na’urori sai tsantsar ilimi, da kuma kwazo da himma dawwamammu.  Wadannan su ne tafarkin tsira.  Shi ilimi muddin ka rike shi da mahimmanci, ka bashi hakkinsa, ka ririta shi ta hanyar dabbaka abin da ka koya, zai samar maka da hanyoyin sauki a rayuwarka, ya zama sanadiyyar inganci da habbaka ga al’ummar da kake rayuwa a cikinta.  Wannan shi ne abin da ke faruwa.  Ba wai cewa Turawa sun fi mu gaskiya bane dari bisa dari, ba wai sun fi mu kwakwalwa bane, ba wai sun fi mu iya sauraron malami bane a cikin aji, ba wai sun fi mu imani bane da Allah, illa sun baiwa ilimi muhimmanci ne, sun ririta shi, sannan suka juya shi ta yadda suke so.  Shi yasa duk da maguzancinsu, idan kaje kasashensu za ka ga bayyanannen ci gaba ta fannin gine-gine, da zane-zane, da kere-kere da kuma ingancin lafiya a rayuwarsu.  Duk wannan ba wani abu bane ya taimaka musu illa rikon ilmi da suka yi da mahimmanci.

Mafita

A karshe zan yi kira ga matasa musamman, domin su ne masu jini a jika, da su riki ilmi da muhimmanci. Wajibi ne ga duk mai son ci gaba a fannin ilmi musamman na kimiyya da kere-kere, ya lazimci abubuwa kamar haka:

Hakuri da Juriya:  Wadannan dabi’u guda biyu suna da mahimmanci wajen ci gaban rayuwa baki dayansa; daga rayuwar addini zuwa fannin mu’amala.  Hujja kan haka kuwa ba sai na kawo mana nassoshin shari’a ba, hatta a al’adance mun san wannan.  Har wa yau duk wanda ka ga ya zama wani a duniya, har ana yi da shi a fannin da ya shahara, idan ya baka labarinsa za ka ga sai ya lazimci hakuri da juriya. To haka karatu yake, musamman fannin da mutum ke son kwarewa a kai, dole sai ya lazimci hakuri da juriya.  Hakuri shi ne danne zuciya wajen daukan abin da al’adance ba za ta iya ba, ko barin abin da a al’adance ba za ta so bari ba.  Shi kuma juriya shi ne tabbata kan hakuri na tsawon lokaci.  Idan hakuri bai samu ba, to, juriya ba ya samuwa.  Sai an jure.

Kyakkyawar Niyya:  Wannan shi ne manufa kan abin da kake son kaiwa gare shi.  Wasu kan dage ne su jure don suna son sunansu ya shahara a duniya.  Wasu kuma don al’umma su amfana da kokarinsu.  Su kuma wasu don su samu abin duniya, ko abin hannu.  Manufarka ce za ta taimaka maka wajen daukan kowace irin dawainiya – na kashe lokaci ne, ko wahala, ko ciyar da dukiya –  don ganin ka cinma burinka.  Amma muddin ba ka da manufa cikin abin da kake yi, zai yi wahala ka iya jure dawainiya da wahalar da ke dauke cikin yin abin ko nemansa, a al’adance.  Amma idan kana da manufa, duk irin wahalar da za ka sha, da zarar kayi niyyar fasawa ko hakura da abin, sai zuciyarka ta tuna maka cewa ga fa dalilin da yasa kake neman wannan abu, nan take sai kaji ka kara samun kaimi.

Hanyoyin Kariya:  Bayan hakuri da juriya da kyakkyawar manufa, idan fannin da kake karantawa ko kokarin nakaltarsa fanni ne mai dauke da hadari ga rayuwa ko lafiyarka, dole ne ka nemi hanyoyin kariya, don rayuwa ta kara inganci.  Kuma ma zai yi wahala ka samu wani fanni na ilimi mai dauke da hadari wajen koyo amma babu hanyoyin kariya ga masu koyonsa ko masu dabbaka shi bayan sun koya.  A takaice dai, kada samuwar hadari cikin fannin karatu ya hana ka koyon wannan fanni, musamman idan kana da sha’awa kansa.  Domin, kamar yadda bayani ya gabata ne a baya, babu wani abu a rayuwa wanda ba ya dauke da hadari a cikinsa, hatta cin abinci, da shan duk wani abin sha, da lasar duk wani abin lasawa, za ka samu akwai hadari a cikinsa.   Abin da kawai za ka duba shi ne maslahar da ke ciki, ma’ana tarin fa’ida da za ka samar wa al’umma bayan ka kware a wannan fanni.

Bukatun Al’umma:  Da yawa daga cikin magabata wadanda suka yi wa al’umma hidima a fagen ilimi sun yi haka ne ta la’akari da abin da al’ummar da suke ciki take da matukar bukatuwa zuwa gare shi.  Wannan ma shi ne babbar makasudi da ake so duk wani mai bincike a fagen ilmi musamman na kimiyya ya rika la’akari da shi a duk sadda yazo gudanar da wani bincike.  Wannan ne zai sa a samu fa’ida cikin abin da aka gabatar, babu maimaici mara fa’ida.  A matsayinka na dalibi mai niyyar shiga jami’a, idan ba ka da wata bukata ta kashin kanka kan fagen da kake son karantawa, to ka dubi meye al’umma ke da bukatuwa zuwa gare.  Wannan zai baka gamsuwa, da kuma ambato na gari a baki jama’a, bayan lada da za ka samu.

Kammalawa

A kowane irin al’amari na rayuwa dole ne a samu kalubale.  Wannan al’adar rayuwa ce.  A matsayinka na dalibin ilmi matashi, wajibi ne ka nemi hanyoyin fuskantar wadannan kalubale, tare da kokarin cin nasara a kansu.  Babu wata al’umma da taba ci gaba ba tare da sadaukar da kai ba.  Shi kuma sadaukar da kai ba abu ne da ke kan hukuma kadai ba, a a, daga kan daidaikun mutane yake farawa, har a wayi gari tsarin ya zama na hukuma.  Domin ba kowa bane hukuma face mutane.  Daga cikin hanyoyin da ke taimakawa mutum ya zama mai sadaukar da kai kuwa akwai hakuri da juriya, da kuma samun manufa ingatacciya wacce a kullum za ta rika tsinkarin matashi don kaiwa ga manufarsa a aikace.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.