Hira da Edward Snowden (3)

Ga kashi na uku na hirar Peter Taylor da Edward Snowden. A sha karatu lafiya.

275

Peter Taylor:  Daga cikin bayanan sirri da ka hankado akwai wani kundi dake dauke da wani tsarin leken asiri mai suna: “Prism,” wanda a karkashinsa bayanai sun nuna irin alakar dake tsakanin Gwamnatin Amurka da sauran kamfanonin sadarwa na sada zumunta dake kasar, irinsu Google, da Facebook, da kuma Yahoo!  Karkashin wannan tsari na “Prism,” hukuma ta tilasta wa wadannan kamfanoni na sadarwa ta hanyar doka, da su rika baiwa hukumar NSA bayanan sirri na jama’a, a duk sadda ta bukata daga gare su.  Babbar manufar wannan tsari na “Prism” shi ne don baiwa hukuma gano ‘yan ta’adda dake wajen kasar Amurka.  Meye karin bayanin da za ka iya yi kan wannan tsari?

Snowden:  Abin da wannan tsari na “Prism” ke nunawa shi ne, hukuma kan je kotu ne a boye, don neman damar aiwatar da kudurinta na tilasta wa wadannan kamfanoni.  Wadannan kotunan jeka-na-yika ne kawai.  Kuma hukumar NSA na gaya musu ne cewa, “Muna neman bayanan wane da wane ne…” amma ba tare da bin ka’idar doka ba.

Peter Taylor:  Babu wanda yasan hakikanin abin dake faruwa ta bayan fage…

Snowden:  Babu wanda yasan abin da ke faruwa, tabbas.

Peter Taylor:  Wasu irin nau’ukan bayanai ne hukumar NSA ke iya tatsa daga wayar salula irin ta zamani?

Snowden:  Sunayen wadanda ka kira, da sakonnin tes da ka aika, da shafukan yanar Intanet da ka shiga, da dukkan lambobin wayar abokanka dake cikin wayar, da wuraren  da ka ziyarta a zahiri, da cibiyar siginar Intanet da kayi amfani dasu (Wireless Access Point) – a gidanka ne ko a ofis.  Don haka, manhajar “Smurf Suite” wani hadakan tsarin tatsar bayanai ne daga wayar salula nau’in iPhone.  Ita kuma “Dreamy Suite” wata cibiya ce mai samar da makamashin lantarki, wanda aikinta shi ne ta kunna wayar salula ko ta kashe, ba tare da saninka ba.

Peter Taylor:  Ko da kuwa na kashe wayar take?

Snowden:  Tabbas!

Peter Taylor:  Sannan akwai wata manhaja mai suna “Nosey Smurf.”   Mece ce “Nosey Smurf” kuma? 

Snowden: “Nosey Smurf” kuma aikinta shi ne tatsar bayanai daga na’urar amsa kirar wayarka, ba tare da saninka ba.  Misali, idan wayarka na cikin aljihunka, ko da a kashe take, hukumar (GCHQ) na iya bude wayar ta zama kamar an kira ka ne ka daga; duk zancen da ake yi a inda kake, suna ji garau.  Domin suna da na’urar da za ta iya kunna wayar ko da kuwa a kashe take.

Peter Taylor:  Ko da wayar tawa a kashe take?

Snowden:  Eh, ko da kuwa a kashe take.  Domin suna da manhajar da za ta iya kunna wayar ba tare da ka sani ba.

Peter Taylor:  Sai manhajar “Tracker Smurf.”  Mece ce manhajar “Tracker Smurf”?

- Adv -

Snowden:  Ita kuma “Tracker Smurf” manhaja ce dake iya gano bigiren da mutum yake, (Geolocation Tool) wanda ta haka (hukumar NSA da GCHQ) za su iya bibiyarka babu kuskure, a duk inda kake.  Ingancinta yafi na’urar gano bigire dake kan wayoyinmu na salula.

Peter Taylor:  Ayyukan wadannan manhajoji ya tsaya ne kan wayar salula nau’in iPhone, ko dai har da sauran wayoyin salula?

Snowden:  Ya hada har da dukkan nau’ukan wayoyin salula.  Abin da ya kamata ka sani shi ne, ita wayar salula fa da kake gani, wata irin na’ura ce da a kullum take like da siginar rediyo na sadarwa, mai dauke da na’urar amsa kira (Microphone) like da ita.  A fannin leken asirin bayanan jama’a, wannan bangare na daga cikin bangarorin da zai yi wahala ka iya kau da kanka daga gare shi, saboda irin daukan hankalin dake tattare dashi wajen inganci.

Peter Taylor:  Daga cikin bayanan da ka hankado har wa yau, akwai wanda ke dauke da bayanai kan yadda hukumar GCHQ ta kasar Burtaniya ke iya tatsar bayanan jama’a ta amfani da wata hanya mai suna: CNE.  Meye karin bayani kan haka?

Snowden:  Wannan shi ake kira: “Computer Network Exploitation,” kuma wani fanni ne daga cikin hanyoyin leken asiri ta amfani da na’urorin sadarwa na zamani.  Tsari ne da yake iya baka damar mallakar bayanai da na’urorin sadarwar da ba naka ba (wadanda ke wata uwa duniya kenan), ta amfani da wasu kalmomin sirri na sadarwa, don tatsar bayanai kan abin da masu na’urar ke aiwatarwa.

Peter Taylor:  Daga cikin bayanan akwai wanda aka yi wa tambari da: “Bayanin Sirri ne na koli,” ya shafi tsarin leken asiri ne ta hanyar kwamfuta.  Kundin hukumar GCHQ ne, kuma daga cikin bayanan, akwai sakin layin dake nuna yadda hukumar ta barko cikin gajeren zangon sadarwa na kamfanin CISCO, ta hanyar na’urar “Router” dinsu dake kasar Pakistan.  Bayanin yaci ga da cewa, hakan ya samar wa hukumar damar kaiwa ga bayanan duk wani mai amfani da Intanet a kasar Pakistan.  Me yasa hukumar tayi haka?

Snowden:  Yadda fasahar Intanet ke aiki shi ne: mutane na musayar bayanai ne a tsakaninsu ta hanyar kwamfuta.  To amma don samar da tsari, akwai kamfanonin sadarwar intanet (Internet Service Providers – ISPs), wadanda ke baiwa jama’a damar mu’amala da Intanet a sawwake.  Abin da su kuma hukumomi ke yi shi ne, sai suyi amfani da tsarin dandatsa su barko cikin gajeren zangon sadarwar wadannan kamfanoni na sadarwa, a boye, don samun damar mallakar bayanan mutanen dake amfani da Intanet, cikin sauki.

Peter Taylor:  Ba tare da sanin su kamfanonin sadarwar ba kenan?

Snowden:  Ba tare da saninsu ba, tabbas.

Peter Taylor:  To, da kamfanin CISCO suka gano haka, me suka yi?

Snowden:  Dole ransu zai baci matuka, domin abin da hukumar ke yi shi ne, suna tarwatsar da amincin da kamfanonin ke dashi ne daga zukatan jama’ar dake kasuwanci dasu.  Sannan mu sani, su wadannan kamfanoni fa wani bangare ne mai matukar mahimmanci wajen ci gaban tattalin arzikin kasarmu.  Tambayar da wadannan kamfanoni na sadarwa ke yi ma ita ce: “Shin, wai wa muke wa aiki ne; kwasotmominmu ko kuma gwamnati?”

Peter Taylor:  Wannan kundi na GCHQ dake nuna yadda hukumar ta barko cikin gajeren zangon sadarwar kamfanin CISCO a Pakistan, shin, hakan bai saba doka bane?  Ko kuma ya halatta?  Domin kundin na dauke da neman izni ne don ci gaba da aiwatar da wannan tsari (na leken asiri).  In kuwa haka ne, to kenan ashe wannan ya halatta kenan.

Snowden:  Wato wani abin mamaki ma shi ne, ba wai abin da hukuma keyi wanda ya saba wa doka bane, a a.  Babban abin tambaya ma shi ne, shin, akwai wani abin da hukuma keyi ne wanda yake halattacce (a wannan fannin)?  Babban hadarin dake tattare da wannan aiki ma shi ne, idan ka barko cikin na’urar “Router” na kamfanin sadarwa, ba wai bayanin mutum daya bane fa kake tatsa; kana tatsar bayanan miliyoyin jama’a ne.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Yahuza Idris says

    Hakika addu’A bazata gushe ba ga wanan taliki, wanda ya saryar da lokacin sa ga al’uma, wanda basu da sanyya ga fannoni da dama na rayiwa. Babu wata kalma da zamuyi amfani da ita domin nuna godiyar mu fatan mu shine Allah ya zama gatanka dama iyalanka ga baki daya, da ana samun Mutane irinsa acikin al’umar Hausa Fulani to da mutanen Kudu basu mana goriba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.