Launin Ruwan Teku

Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muka fara kawowa kan tekunan duniya. A yau mun dubi launin ruwan teku ne. A sha karatu lafiya.

1,193

Wannan shi ne kashi na 2 cikin jerin kasidu masu take: “Tsarin Tekunan Duniya da Abubuwan Da Ke Cikinsu.”


Launin Ruwan Teku

Daga nesa ko daga sama idan ka kalli ruwan teku, za ka tarar launinsa shudi ne, wato “Blue.”  Amma da za ka je bakin tekun ka kamfaci ruwan dake tekun da tafin hannunka, ko ka sa kofi ka debo, za ka tarar launinsa ya koma launin ruwan da ka saba mu’amala dashi a kogi ko ma na famfo, wato: mai daukan idanu, kamar gilashi.  Meye dalilin da ya sa launin ruwan teku ya zama shudi?  Malaman kimiyyar teku sun bayar da dalilai guda uku kan haka.  Na farko, suka ce yanayin launin ruwa asali kamar madubi yake; yana daukan hoton duk abin dake samansa ko yake makwabtaka ko ya gilma inda yake.  Wannan a bayyane yake.  Kuma tunda babu wani shamaki tsakanin teku da sararin samaniya, hakikanin launin sama ne ruwan teku ke daukowa.  Shi yasa da zarar ka kalli ruwan teku daga sama, musamman a saman jirgi, za ka ga launinsa iri daya ne da launin sama, wato shudi (Blue).  Wannan kuma ke nuna cewa, idan aka samu hazo a sama, daidai inda tekun yake, launin ruwan tekun zai dace da launin hazon ne; idan fari ne, ruwan zai zama fari.  Haka ma idan baki be, zai zama baki.

- Adv -

Dalili na biyu, suka ce bayan daukan hoton launin sama da ruwan tekun ke yi sanadiyyar yanayinsa, idan hasken rana ya bayyana, ya kuma ratso cikin ruwan teku, wannan haske kan koma sama ne, tunda yanayin ruwan kamar madubi be.  Kenan, bayan fuskar teku dake daukan hoton sama, hatta ruwan dake cikin tekun (daga tsakiya zuwa can kasa, misali) da zarar ya yi arba da hasken rana, sai ruwan ya cilla wannan haske zuwa sama.  Idan hasken ya isa sama, sai hoton launin sama (shudi) ya bayyana nan take a cikin tekun; ya saje dashi.

Dalili na uku, suka ce a yayin da hasken rana ya ratso zuwa cikin teku, akwai sinadaran dake cikin ruwa masu suna “Molecles” a harshen turancin kimiyya.  Su wadannan sinadarai da zarar hasken rana ya keto daga sama ya ratsa su, nan take suke girgiza.  Wannan girgiza nasu shi ke kashewa ko narkar da launukan haske guda hudu daga cikin shida dake cikin kowane haske.  Launin da wannan girgiza na sinadaran ruwan teku ke batar dasu su ne: Ja (Red), da Lemo (Orange), da Rawaya (Yellow), da Kore (Green).  Sauran launuka guda biyu da suka rage a cikin hasken su kadai muke gani, wato: shudi (Blue) da Jirkitaccen Shudi (Violet).  Wannan ke sa ruwan ya zama launin shudi a idanunmu, kuma, a cewar Malaman Kimiyyar Teku, shi ne dalili mafi karfi daga cikin wadannan dalilai uku dake sa launin ruwan teku ya zama shudi a idon mai gani.

Bayan haka, binciken Malaman kimiyyar teku ya tabbatar da cewa tekunan duniya kan fitar da wani irin haske cikin dare, mai walkiya da daukan idanu, wanda kuma ke mamaye bigire mai fadi na ilahirin tekun.  A shekarar 2005 malaman kimiyyar teku sun yi kokarin daukan hoton irin wannan haske dake bayyana, wanda a wancan lokaci ba a san dalili ba.  Da bincike yayi nisa, sai aka gano cewa a cikin dabbobin dake rayuwa a cikin teku, akwai wadanda ke fitar da haske daga jikinsu saboda wasu dalilai.  Haka Allah ya halicce su.   Wannan haske shi ake kira: “Bioluminescence,” a harshen malaman kimiyyar teku.  Wanann haske, a cewar masu bincike, Allah ya samar wa wadannan dabbobi ne don wasu dalilai na musamman.  Ga wasu, wannan haske kariya ne daga abokan gaba.  Ga wasu, suna amfani da wannan haske ne wajen jawo hankalin abokan jinsi ko hulda.  Ga wasu dabbobin, wannan hanyar sadarwa ce.  Ga wasu dabbobin kuma, wannan haske gargadi ne ga dabbobin dake kokarin cutarwa ko kusantar mai hasken.  Allah buwayi gagara misali!

Daga bayanan da suka gabata a kashi na farko zuwa sakin layin da ya gabata, mai karatu ya fahimci kadan cikin tsari da yanayin teku a jimlace.  Ga bayanai nan kan kowanne daga cikinsu; daya bayan daya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.