Manyan Matsalolin Dandalin Facebook (1)

A kashi na hudu dai, za mu dubi manyan matsalolin wannan dandali ne na Facebook. A sha karatu lafiya.

272

Wannan shi ne kashi na 4 a jerin kasidu masu take: “Dandalin Facebook a Manhangar Binciken Ilimi.”


Matashiya

Idan mai karatu na tare da mu a wannan jerin kasidu da muka taso tun shekarar da ta gabata kan Dandalin Facebook, ya san mun dakata ne a kasidar da ke dauke da bayani kan dalilan yaduwar wannan sabuwar hanyar sadarwa ta zamani a duniya.  Kuma kada a mance, mun yi alkawarin kawo dukkan bayanan da suka shafi wannan shafi ne gaba daya, cikin yardan Allah; iya gwargwadon sani da fahimta.  Wannan ita ce kasida ta shida.  A yau kuma ga mu dauke da bayanai kan Matsalolin da ke tattare da wannan dandali.  Yana da kyau a rayuwarmu mu rika kiyaye wani abu guda daya; cewa duk lokacin da wani abu ya shahara a duniya wajen amfani, muddin abu ne na mu’amala ba wai ibada ba, to duk yadda alherinsa ya yawaita, sai an samu matsaloli sanadiyyar amfana da ake yi da shi.  Ko dai ya zama matsalar daga jikin abin ne, ko kuma daga wajen masu mu’amala da abin.  In kuwa haka ne, to kada mai karatu da ke tinkaho da Dandalin Facebook a wajen abokai ko ‘yan matansa – yana ganin ai shi wani dan birni ne wayayye, mai amfani da wata hanyar sadarwa mai tasiri da a tunaninsa kowa da kowa suka yarda da shahararta – bayan ya ga wannan kasida kuma yaji hankalinsa ya tashi.  Wannan ka’ida ce ta rayuwa.  Don haka sai mu kiyaye.

Kamar yadda muka yi bayani a baya, wannan dandali ya shahara, ya kasaita, ya kuma tumbatsa a duniyar Intanet.  Wanda ya mallaki wannan dandali, wato Mark Zuckerberg, a halin yanzu yana daga cikin matasa masu kudi a duniya.  Wannan ke nuna cewa hatta a bangaren kasuwanci dandalin ya bunkasa.  To amma kuma akwai matsaloli masu dimbin yawa da ke tattare da wannan shafi na dandalin Facebook.  Wadannan matsaloli sun kasu kashi biyu.  Na farko sun samo asali ne daga shafin shi kanshi; yadda aka tsara shi, da yadda ake tafiyar da shi.  Na biyu kuma sun samo asali ne daga yadda masu mu’amala da shafin ke amfani da shi.

Babban abin da ya zaburar da ni wajen kawo wadannan bayanai dai shi ne don mutanenmu Hausawa da suka fara yaduwa da barbazuwa a shafin, ta hanyar mallakar shafukansu na kashin kansu, wadanda kuma galibinsun matasa ne; maza da mata.  Wajibi ne mu fahimci cewa akwai bambancin al’ada da addini a tsakaninmu da mafi yawancin masu amfani da wannan shafi a wasu kasashe, musamman kasashen yammacin duniya. Wannan zai taimaka mana wajen daina kwaikwayon da yawa cikin abubuwan da suke yi marasa kyau a shafin, wadanda kuma muna gani, muna karantawa.  Ire-iren wadannan matsaloli ne ma tasa wasu daga cikin malaman addinin musulunci musamman suke ganin kamar haramun ne musulmi ya rika mu’amala da shafin ko a shafin.  Kuma ba komai ya kawo wannan fatawa mai zafi ba sai don ganin abin da ke faruwa a shafin dandalin Facebook.  Ni dai a iya ‘yar gajeriyar fahimta ta, ya danganci yadda ka yi amfani da shafin.  Idan ya zama ka kiyaye dokokin Ubangiji a matsayinka na musulmi a yayin da kake mu’amala da jama’a a wannan dandanli, to, hakika ka tsira.  Amma idan ka dauki tafarkin ‘yan duniya, masu ganin ai yanzu duniyar ta waye, dole ne a tafi da zamani, to kai ka jiwo, sautun mahaukaciya.  Kada mu tsawaita, a halin yanzu ga wasu daga cikin wadannan matsaloli.  Da fatan za mu kiyaye.  Allah ya mana jagora, amin.


Cin Mutuncin Addini

Wannan ita ce matsala ta farko daga cikin matsalolin da suka fi shahara a dandalin Facebook.  Kuma daga cikin addinan da wannan matsala ta shafa akwai addinin musulunci. Kuma wannan matsala ta cin mutuncin addini ta samo asali ne daga wajen masu amfani da wannan shafi.  Shekaru biyu da suka gabata wata kungiya da ba a san ko su waye ba sun bude wani shafi da ke kira zuwa ga zanen hoton Manzon Allah (SAW), a daidai lokacin da suke gab da bikin farin cikin zagayowar ranar da wani mai zane dan kasar Denmak ya aiwatar da wannan mummunar aiki, kamar yadda suka sanar.  Wannan lamari ya tayar da kura a dandalin gaba daya, inda har musulmai suka bude shafi don nuna damuwarsu kan wannan lamari.  Nan take sauran musulmi da ke dandalin suka fara bore.  Aka kirkiri wata rajista ta musamman don baiwa kowane musulmi sanya hannu kan kira ga shugabannin Dandalin Facebook su rufe wancan shafi da ke kira zuwa aibanta Manzon Allah ta hanyar zana hotonsa.  Cikin awanni ashirin da hudu aka samu musulmi sama da dubu hamsin da takwas da suka rattafa hannunsu kan wannan rajista.  Bayan nan kuma, musulmin kasar Pakistan sun yi zanga-zanga a gaban ginin majalisar dokokin kasar don kira ga majalisar ta fitar da dokar da za ta haramta mu’amala da shafin Facebook a kasar gaba daya. Ganin haka ke da wuya sai hukumar dandalin Facebook ta rufe wancan shafi.

- Adv -

Faruwar wannan lamari ya baiwa da yawa cikin musulmi haushi, inda suka yi ta fita daga dandalin, suka ta rufe shafukansu, kuma suna ta kira ga duk wani musulmi ya fice daga wannan dandali. Duk da cewa hukumar Facebook ta kulle wancan shafi da ke batanci ga Annabi Muhammad (SAW), da yawa cikin musulmi basu sake da ita ba, domin a yarjejeniyar asali da hukumar shafin ta tanada, sun nuna cewa kowa yana da hakkin bayyana ra’ayinsa na siyasa ne ko na addini, muddin ba zai ci mutuncin addinin wani ko al’adarsa ba.  In kuwa haka ne, to bai kamata ma tun asali hukumar ta bar masu wancan shafi na batanci har su kai gaci ba, tunda ra’ayin da suke kokarin bayyanawa ya ci karo da wannan yarjejeniya.  To me yasa ba a hana su ba har sai da musulmi suka nuna damuwarsu, har aka yi kokarin kawar da shafin daga kasar Pakistan, sannan suka rufe?  Wannan, a cewar da yawa cikin musulmin kasar, alama ce da ke nuna cewa lallai hukumar Dandalin Facebook basu dauki addinin musulunci a bakin komai ba.  Wannan matsala ta farko kenan.

Gulma da Hirar Banza

Ba dandalin Facebook kadai ba, duk inda majalisar Intanet take, ana samun yawaitar gulmace-gulmace da karairayi marasa tushe.  To amma wanda ake samu a dandalin Facebook ya fi kowanne yawaita da maimaituwa.  Ba don komai sai don hanyoyin mu’amala da shafin sun yawaita matuka.  Bayan kwamfuta da ake iya amfani da ita wajen shiga dandalin, kana iya amfani da wayar salularka, wacce kake damfare da ita a duk inda kaje, muddin akwai Intanet a ciki.  Wannan ke bayar da damar ganin a kowane lokaci ka fadi wani abu, ko halin da kake ciki, ko inda kaje, ko wani abin da ka gani, ko abin da wani ya fada.  Duk wanda ke ziyartar shafukan Hausawanmu matasa a Facebook zai fahimci abin da nake nufi.  Bayan zumunci, wanda ake yinsa sosai kuma abin alfahari ne a garemu, akwai batanci da ke samuwa, da zage-zage ga wasu daga cikin shugabanninmu wadanda suka shude ko suke kan mulki.  Dukkan wannan, a riyawar masu shafukan da kuma wadanda suka assasa shafin, fadin albarkacin baki ne.

To amma da za a auna wa mutum nauyin kalmomin da yake fada miyagu a kan wasu, da irin hukuncin da ke jiransa a kabari ko a kiyama, da ba haka ba.  Wajibi ne kowane musulmi ya san cewa, kamar yadda za a tambayeshi kalmomin da ya fada da harshensa, da wadanda ya daka ko ya yafuta da hannunsa ba tare da hakki ba, to haka za a titsiye shi ya yi bayanin abin da ya rubuta da hannunsa a filin kiyama.  Wannan matsala ta gulmace-gulmace da hirar banza marasa alfanu su suka fi yawa a shafukan dandalin Facebook.  Tabbas akwai raha da ake yi a tsakanin abokai, ko magoya bayan wasu kungiyoyi na kwallo ko na siyasa.  Wannan raha da ake yi dole ne yana da ma’auni.  Ma’auninsa kuwa shi ne tabbaci ko rashin tabbacin kalmomin da ake fada a yayin da ake rahan.  Ma’ana, gaskiya ko rashin gaskiyar kalmar da aka fada.  Don haka sai a kiyaye.  Sai matsala ta gaba.

Haifar da Tsana da Hassada

Daga cikin matsalolin dandalin Facebook manya akwai haifar da tsana da hassada.  Watakila mai karatu zai yi mamaki, musamman ganin cewa rubuce-rubuce ne kawai ake yi a shafukan. Da farko dai babu abin da ke haifar da yawan tsana a tsakanin masu mu’amala da shafin sai gulmace-gulmace.  Ire-iren wadannan matsaloli kan haddasa yankewar alaka a tsakanin wadanda abin ya shafa, ko da kuwa a zahirin rayuwa suka hadu.  Yawan zage-zage, da gulma, da rade-radi marasa tushe, da kuma fadi-ba-tambayeka ba, duk su ne ke haddasa tsana a tsakanin dandalin.  Babban abin da ke haddasa samuwar hassada kuma shi ne yadda wasu ke sifata rayuwarsu da abin da suke riya cewa sun mallake shi wanda karya ne, ko darajan ilminsu, ko martabarsu a rayuwa, ko wasu mukamai da aka basu a shafi ko dandalin.  Mai karatu zai mamakin jin cewa akwai mukamai na sarautar gargajiya da ake dasu a shafukan Facebook; bangaren dandalin Hausawa nake nufi.  Wadannan mukamai na sarauta don raha ne aka kirkiresu.  Amma shaharar masu mukaman ko ganin yadda suka samu karbuwa a wajen mambobin da ke dandalin, na iya haifar da hassada a zukatan wasu.  Wannan a tabbace yake, domin hatta a Majalisun Tattaunawa na Yahoo! da Hausawa suka mallaka, ana samu wannan matsala.  To, a shafukan Facebook ma akwai ta.  Ba komai ya dada taimakawa ba sai ganin cewa gilli da hassada wasu dabi’u ne da Allah ya rakkaba dan adam a kansu wajen halitta.  Maganinsa na samuwa ne ta hanyar karantar ilmin addini da kuma aiki da shi.  Sai matsala ta gaba.

Gajiya da Damuwa

A duniyar Intanet, babu abin da ya fi haddasa gajiya da damuwa (Stress and Fatige) kamar shafukan abota irinsu Facebook.  Hakan na samuwa ne sanadiyyar dadewan zama ana abu daya, da kallon gilashin kwamfuta ko wayar salula masu dauke da sinadaran hasken da ke cutarwa a hankali a yayin da ake karatu ko rubutu, da kuma tsawaita tunani ko damuwa ko bakin ciki kan abin da ya faru ko yake faruwa a shafi ko dandalin da mutum ya mallaka.  Bayan haka, idan mutum ya kamu da mummunar shakuwa kan Intanet, wato Cyber Addiction, wata matsala mai zaman kanta na iya samuwa.  Matsalar kuwa na iya nuna kanta ne ta hanyar zazzabi a duk lokacin da ba a samu damar shiga dandali ko shafin ba, da kuma tsawaita bakin ciki mara misali da ma’ana kan abin da mai shafin yake kullawa. Kai a takaice ma dai, ana iya kaiwa wani mataki wanda shi kanshi mai shafin ba zai taba samun natsuwa da jama’ar da yake rayuwa da su a gida ko unguwarsu ba, sai ya shiga dandalin Facebook da ke wata duniya tsakanin mafarki da hakika.  Sai matsala ta gaba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.