Manyan Matsalolin Dandalin Facebook (2)

A kashi na biyar, zamu ci gaba da duba manyan matsalolin dandalin Facebook ne. Da fatan masu karatu za su kiyaye, musamman ma masu mu’amala a wannan dandali. Wannan kashi na biyu kan binciken abin da ya shafi matsaloli kenan. A sha karatu lafiya.

201

Wannan shi ne kashi na 5 a jerin kasidu masu take: “Dandalin Facebook a Manhangar Binciken Ilimi.”


Kashe-Kashe da Ta’addanci

Nau’ukan kashe-kashe da ta’addanci mara misaltuwa – wadanda kafafen labarai suka hakaito da wadanda ba a hakaito ba – ruwan dare ne a duniyar Intanet, kuma hakan ya fi shahara ne a kasashen yammacin duniya.  To, watakila mai karatu yace ai mu ba ruwanmu da wannan bakin rayuwa. A a, daga na gaba ake ganin zurfin ruwa.  Idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, maza ka nemi gulbi ko tafki ko kududdufi ka tsoma naka a ciki.  A dandalin Facebook an samu ire-iren wadannan matsaloli, inda masu sace kananan yara ke amfani da adireshin gidajen iyayensu, ko barayi ko kuma wadanda aka tura su don kashe wani, galibi sukan yi amfani ne da shafukan Facebook don sanin fici-da-shigin wanda suke son kamawa ko kashewa ko masa ta’addanci.  Domin dandalin Facebook taska ce inda galibin turawa sukan rubuta duk abin da ya shafi rayuwarsu baki daya.  Sannan ko tuntube suka yi a kan titi, sai sun rubuta.  To, haka ma mutanenmu da ke dandalin.  Sai ka ga mutum ya rubuta cewa, yanzu bacci nake ji, ko yunwa nake ji, ko ba ni da lafiya, ko jiya na je wajen wance ta wulakanta ni, ko na fi sha’awan abin ci ko abin sha nau’i kaza.  Dukkan wadannan bayanai ne na sirri da suka shafi rayuwarka, kuma wani abokin gaba na iya amfani da su wajen cutar da kai, kamar dai yadda muke jin labari a wasu kasashen.  Tabbas babu abin da zai faru da kowane dan adam sai abin da Allah ya kaddara masa, to amma Allah da kansa ya sanar da mu cewa mu kiyaye.  Don haka sai a kiyaye.  Sai matsala ta gaba.

Dodorido

Kalmar dodorido ta shahara a dandalin Hausawa a Intanet.  Kuma abin da kalmar ke nufi shi ne yin amfani da fuska ko sunan wani daban don boye kai.  Ma’ana wani ya bude shafi da sunan wani shahararren mutum, yana nuna cewa shi ne wannan mutumin, alhali ba haka bane. Yana iya nemo hoton mutumin ya lika, ya samo ra’ayoyinsa na siyasa ko na addini, ya kattaba a shafin, yana muzurai wai shi ne wane.  Duk wannan na samuwa ta hanyar dandalin Facebook. In kuwa haka ne, to ya kamata ka san da wa kake mu’amala.  Karairayi da yaudara sifofi ne guda biyu da suka shahara a duniyar Intanet.  Dole ne ka zama mai iya tantancewa; da wani irin mutum kake alaka?  In kuwa ba haka ba, za ka sha mamaki.  Wani abin bakin shi ne, masu irin wadannan dabi’u na boye kai sun fi shahara a shafukan abota irin su Facebook da Twitter.  Don haka sai a kiyaye.  Sai matsala ta gaba.

Batsa da Ashararanci

Yadda batsa da ashararanci suka yadu a duniyar zahiri da muke rayuwa a ciki, to haka suka yadu a duniyar Intanet.  Akwai shafuka na musamman masu sayar da zina ko hotunan batsa.  Amma a dandalin Facebook galibi hanyoyin “hada waya” ne ake da su.  Ma’ana, ta hanyar wannan dandali da yawa cikin masu wannan dabi’a kan hadu, su yi abota, su shirya wurin haduwa, sannan a yi abin da ake son yi.  Kowa da jama’arsa!  Galibin abotan da ake shiryawa ko kullawa a ire-iren wadannan shafuka – ko dai tsakanin maza da mata, ko tsakanan mata da mata, ko kuma tsakanin maza da maza.  Al’amuran sai dai addu’a.  A wajen masu wannan dabi’a, dandalin Facebook wajen neman abokan hulda ne da harka.  Domin a wajen bayanan da suka shafi mutum kana iya sanin manufarsa idan ya rubuta.  Maza yake son abota da su ko mata kadai.  Mace take son yin abota da ita ko maza kadai, duk za ka samu.  Bayan haka, wasu ma kan wuce gona da irin shukawa, su bayyana hakikanin abin da suke nufi ko so. Wasu kalmar baka ce kadai, ba sa nufin abin da suka rubuta, amma wasu kuma da gaske suke yi.  Sai an latsa ake iya bambancewa.  Allah kiyashe mu mummunar latsi.  Sai a kiyaye.  Sai matsala ta gaba.

- Adv -

Yawan Shagaltuwa da Shagaltarwa

Da yawa cikin makarantun da ke kasar Amurka da sauran kasashen yammacin duniya, sukan sanya wa shafin dandalin Facebook takunkumi, ta yadda idan a makarantar kake, ba za ka iya shiga shafin ba.  Ba don komai ba sai don yadda dalibai suka jarabtu da shafin, wajen abota da hirarraki marasa alfanu.  Wanda kuma hakan yana mummunar tasiri kan karatunsu.  Domin ba su samun daman zama su yi nazarin darussan da aka karantar da su.  Haka hukumomi da ma’aikatun da ke wadannan kasashe, har da ma kasashe masu tasowa, sukan sanya wa wannan shafi takunkumi a ma’aikatar, ta hanyar masarrafar garkuwar wuta, wato Firewall.  Domin an lura cewa galibin ma’aikata kan shagaltu da wannan shafi, har kadarin aikin da suke yi ya ragu.  Wannan na cikin abin da ke dada harzuka masu wadannan ma’aikatu, har dai a karshe suka ga ba sarki sai Allah, suka katange ma’aikatansu daga wannan bala’i.

Wadannan dabi’u na shagaltuwa da shagaltarwa a bayyane suke a wannan dandali.  Domin idan ka fara mu’amala ko abota da mutane, gaba daya zuciyarka za ta koma kan dandalin ne kacokam.  Za ka ji in ba shafin kaje ba, kamar baka samu cikakkiyar rayuwa ba. Idan har ka fara jin haka, to ka san cewa lallai wadannan miyagun dabi’u guda biyu sun shige cikin kwaroron jinin jiki da zuciyarka, kamar yadda guban cizon sauro ke kwararowa cikin jiki.  A matsayinka na wanda makaranta ko ma’aikatar da kake aiki basu katangeka daga wannan matsala ba, ka san cewa kana da aiki mai girma.  Domin babu abin da ya fi wahala irin tarbiyyantar da kai.  Don Allah a rika kiyayewa, a san cewa lokaci yana da tsada, kuma da zarar ya wuce fa, ba zai kara dawowa ba.

Matsalolin Gudanarwa

Matsalolin da za mu dakata a kansu su ne matsalolin gudanarwa da wannan dandali ke fama da su.  Da farko dai, akwai rade-radin da ya game duniyar Intanet mai nuna cewa lallai hukumar gudanarwar dandalin Facebook na sayar da bayanan da suka shafi jama’a, wanda suke taskancewa cikin kwamfutocinsu, ga kamfanonin kasuwanci da binciken dabi’un mutane a Intanet.  Wannan, in har gaskiya ne – wanda kuma akwai alamar hakan – ba karamar cin amana bace.  Domin a cikin kundin yarjejeniyar da kowane mamba ke yarda da su kafin a bashi shafi, sun nuna cewa ba za su bayyana bayanansa na sirri ga wani daban ba. Yanzu kuma a samu labarin cewa kamfanin na sayar da wadannan bayanai da suka shafi sirrin rayuwar jama’a ga wasu, ba karamar cin amana bace.

Bayan haka, idan kana mu’amala da shafin Facebook, a duk lokacin da ka shiga matsala, to ba ka da wanda zai warware maka matsalar da ka tsunduma ciki.  Da zarar ka je shafin neman taimako, wato Help Page, babu abin da za ka ci karo da shi sai tsofaffin bayanan da ko kadan ba za su dace da matsalarka ba. Wannan matsala kuwa ta samo asali ne saboda masu gudanar da wannan shafi basu ajiye wani mutum na hakika, wanda zai rika zama yana amsa matsalolin masu shafuka a dandalin ba.  Manhajar kwamfuta ce suka tanada, wacce da zarar ka tura musu bukatar a warware maka wata matsala, sakonka na isa inda take, sai kawai ta cillo maka rariyar likau din da za ta kaika wajen wancan shafi da muka yi bayaninsa a sama.  Wannan ke nuna mana cewa lallai araha ba ta ado.

Sannan a wasu lokuta ba abin mamaki bane ka nemi shiga dandalin ma gaba daya, sai a ce maka: “Yi hakuri, a halin yanzu muna fuskantar wasu ‘yan matsaloli ne…nan da minti daya ka sake kokarin shiga.” Minti daya na karewa idan ka nemi shiga za ka sake samun wannan sako.  Wannan ba karamar matsala bace.  Domin idan ya zama rayuwarka da farin cikinka gaba daya suna cikin shafin Facebook ne, to watarana idan aka yi rashin sa’a kwanakinka suka kare, sai buzunka.  Wajibi ne a kan masu gudanar da wannan dandali su tanadi kwamfutoci masu dimbin yawa da girman mizani, da masarrafai ko manhajoji masu nagarta da tasiri wajen tsare bayanai da iya mika su cikin lokaci. In kuwa ba haka ba, abin da ya samu shafuka irin su MySpace, zai same su. Abin da yaci Doma, ko kadan ba zai bar Awe ba.  Muddin mutane ba su samun daman shiga shafukansu a lokacin da suke so, kamar yadda aka musu alkawari, to, da zarar an samu wani shafi da yafi shi nagarta, kowa zai kaurace masa ne.

Sai matsala ta karshe, wato “goge” shafi daga kwamfutocin kamfanin Facebook. Idan ka gaji da mu’amala da shafinka na Facebook, ba ka da wata hanyar goge shafin gaba daya, sai dai ka “kulle”.  Idan ka je bangaren “Settings” da ke shafinka na Facebook, a can kasa, za ga an rubuta “Deactivate Your Account”.  Kalmar “Deactivate” na nufin ka kulle shafin ne daga amfani da shi, amma dukkan bayananka, da hotunanka, da sauran abubuwanda suka shafeka, suna nan daram-dakam a kwamfutocinsu.  Ma’anar wannan kalma ta sha bamban  da kalmar “Delete”, wanda duk masanin harkar sadarwa ya san gogewa ake nufi.  Wannan kuma ke nuna cewa nan gaba suna iya amfani da su.  Watakila mai karatu ba zai fahimci matsalar da ke tattare da hakan ba, tunda mu a nan bamu cika damuwa da sirrin bayanan da suka shafe mu ba. Amma ga wadanda suke wasu kasashe, ba karamar matsala bace da kuma barazana ga rayuwa ko mutuncinsu.  Duk da yake wasu sun gano wata sabuwar hanyar da ake bi a goge shafin baki daya, amma da sauran rina a kaba.  Musamman ganin cewa masu gudanar da wannan shafi sun ki fitowa fili karara don nuna wa masu mu’amala da shafukansu yadda za su iya goge dukkan abin da suka rubuta ko adana a ciki.  To me yasa suka ki bayyanawa?  Oho!  Allah kadai ya san addu’ar kurma.  Abin da yake wajibi ga mai mu’amala kawai shi ne, ya san irin bayanan da zai rika zubawa a ciki, da irin kalmomin da zai rika amfani da su, don komai na iya faruwa a kowane lokaci.  Allah mana jagora, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.