Mashakatar Lilo a Intanet (Cyber Cafe)

A makon da ya gabata, mun yi zama ne don nazari kan kasidun baya da tasirinsu wajen taimaka ma mai karatu kara saninsa da fahimtarsa kan wannan hanyar fasahar sadarwa da abin da ya shafe ta.  A haka za mu ci gaba da kawo bayanai, muna zama lokaci-lokaci, don yin waiwaye, abin da wani bawan Allah mai suna Malam Bahaushe ya ce “adon tafiya” ne.  A wannan mako, za mu yi bayani ne kan Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake, wato Cyber Café, a turance.  A yanzu za mu dukufa!

256

Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake

Ma’anar Cyber Café shi ne Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake.  Wuri ne da duk mai son shiga Intanet ke zuwa don ya sayi lokaci (sa’a daya ko mintuna talatin ko makamancin haka), don yin lilo da tsallake-tsallake a giza-gizan sadarwa ta duniya.  Bayan Cyber Café, a kan yi amfani da kalmar Internet Café, duk da nufin abu daya.  Wannan kalma ko kalmomi, kamar yadda muka sha sanarwa dangane da sauran kalmomin turancin da su ka danganci fasahar sadarwa, kalmomi ne baki, wadanda mai karatu zai sha wuya idan yace sai ya samu hakikanin ma’anarsu a cikin Kamus (Dictionary) na turanci.  Tabbas akan samu wasu kalmomin, saboda yawan bita da ake ma kundayen kamus na turanci, amma sau tari sai ka nemi wata kalmar  ka rasa, ba ma ta ma’anarta ake ba.

Babban dalili kuwa shi ne, saurin yaduwan kalmomin ya zarce kusancin lokacin da ake daukawa wajen bitan kamus din, nesa ba kusa ba.  A Hausance kuma, kalmar “Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake” kuma, Farfesa Abdallah Uba Adamu da ke Jami’ar Bayero ne (a iya sani na), ya kirkireta.  Don haka mu ke biye da shi a kan wannan turba.  Kuma duk da kiran da ya sha yi, cewa wadannan kalmomi (da wasu daban ba wadannan ba) ya kirkire su ne a bisa fahimtar da yayi na irin sakon da kalmar turancin ke son isarwa. Yana kuma kira ga masana harshen Hausa da ke Jami’o’in Arewacin Nijeriya, kai har ma waje, su yi bitan wadannan kalmomi don tabbatar da daidainsu ko rashin dacewarsu, har yanzu ban ji wani ya yi ko tari ba kan hakan.  Don haka, idan ka ji an ce: “Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake”, to kada ka raba daya biyu: ana nufin Cyber Café ne, idan dan boko ne kai masanin turancin Ingilishi.  Idan kuma dan uwa na ne kai, to ana nufin shago ko wata rumfa da ake zuwa don samun hanyoyin mu’amala da fasahar Intanet.

Tarihin Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake a kasashen duniya, musamman in da wannan fasaha yayi buruzi, tarihi ne dadadde.  A kalla ma iya cewa dadewarsa daya ne, ko kasa da haka kadan, da dadewar fasahar Intanet din ita kanta.  Idan ka je kasashen Turai da Amurka, da kasashen Gabas-ta-Tsakiya musamman, za ka samu shaguna kayatattu, masu cike da kayan alatu da kayan makulashe da kwamfutoci da sauran karikitai, don masu zuwa yin lilo da tsallake-tsallake a giza-gizan sadarwa ta duniya.  Wannan Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake kenan, da tairhin kalma da lokacin bayyanar ta.  To me da me ke cikin wannan mashakata, musamman a kasashenmu na Afirka?

Me Ke Ciki?

Ta la’akari da manufar kafa wannan shago ko mashakata, mai karatu zai iya hasashen me da me zai kasance a ciki.  Galibin abin da ke cikin Mashakatar Tsallake-tsallake sun kasu kashi uku; kashi na farko su ne kwamfutoci, sai kayayyakin lantarki, masu taimakawa wajen sarrafa kwamfutar, irinsu UPS, Stabiliser, Wayoyi dsr.; sai kuma ma’aikata.  A dukkan wani mashakata na lilo da tsallake-tsallake akwai kwamfutoci, wanda a kan su ne mai lilo zai yi duk abin da yake son yi.  Wadannan kwamfutoci ba su da iyaka; ya danganta da girma da kuma karfin mai shago.  A wasu wurare zaka iya samun kwamfutoci sama da ashirin.  A wani wurin kuma ma basu wuce biyar; iya gwargwadon girman shago ne da karfin aljihu.  A galibin biranen Nijeriya, yawan kwamfuta a cikin mashakatar tsallake-tsallake na danganta ne da yanayin wuri; akwai jama’ ko babu, masu sha’awan shiga.  Duk wannan na daga cikin abin da ke tabbatar da yawan ko kiman girman shagon lilo da tsallake-tsallake.

Wadannan kwamfutoci dai ana hada su ne da juna, a bisa tsarin gajeren zangon sadarwa, wato Local Area Network (LAN).  Duk mashakatar da ka je ka samu kwamfutoci sama da daya, ana shiga Intanet ta cikinsu, to a hade suke da guda daya, wacce ake kira uwar garke, wato Server kenan a turance.  Ita wannan Uwar Garke zaka samu tana gefe ne, an ajiye mata wanda ke kula da ita, ko kuma a wasu wurare ka same ta cikin wani daki daban.  Ita ce kwamfutar da ke karban shafukan yanan gizo daga kamfanin da ke sadar da masu shagon (idan ta hanyar wasu suke samu), wato Internet Service Provider (ISP), ko kuma ta hanyar tauraron dan Adam mai suna Earthlink, idan kai tsaye su ke saduwa da giza-gizan sadarwa.  Hakan kuwa na faruwa ne ta dalilin wani kafcecen dish na tauraron dan Adam (Satellite Dish) da ke taimaka masu.  Idan wannan kwamfuta ta zuko, sai ta raba ma dukkan sauraron kwamfutocin da ke cikin mashakatar, kai tsaye, ba wai adana su take a tumbinta ba.  Su kuma sauran kwamfutocin na samun wadannan shafuka ne ta hanyar wayoyin kebul, wanda ke hade da babban mahadar karban bayanai, wato Switch.

Shi Switch wani dan karamin na’ura ne mai kafofin shigar da wayoyi, wanda ta wadannan kafofi yake raba duk abin da ya kwaso daga cikin Uwar Garken.  Shi ya sa da zarar siginar Intanet ta dauke a kwamfutocin mutane, sai ka ji ana ta yi ma Operator (wanda ke lura da Uwar Garken kenan) ihu da surutu, musamman ganin cewa kudinsu na tafiya, kuma babu sigina.  Dayan abubuwa uku ne ke haddasa daukewan sigina; ko dai ya zama hadari ya hadu ganga-ganga (ya Allah ruwa na sauka ne ko ba ya sauka), ko kuma masu lilo a saman Uwar Garken kwamfutar masu sadarwasu, sun yi yawa (ka kwatanta mana ka gani; ko da reshen itaciya ne aka samu masu lilo a hannayensa sun yi yawa, yaya? Dole yayi laushi ko ma ya karyo kasa da kowa da kowa); ko kuma ya zama ainihin wayar da ke sadar maka da sigina daga Uwar Garke ne ya cire.  To bayan kwamfutoci, sai kuma sauran karikitan da ke taimaka musu aiwatar da ayyukansu.  A sama mun ambaci Switch, idan babu shi, to babu Internet, gaba daya ma.  Domin shi ne “dan aike”, mai sadar da kwamfuta da ‘yar uwanta.  Sai kuma Uninterrupted Power Supply (UPS), wanda ke taimaka ma kwamfuta rike wuta na wani dan takadirin lokaci, idan an dauke wuta.  Wasu su kan sanya ma kowace kwamfuta na ta, wasu kuma su sanya babba guda daya, wanda zai dauke dukkan kwamfutocin.  Bayan nan kuma sai wayoyin kebul, amma ba kebul din da kowa ya sani ba ne.  Shi wannan ana kiransa Data Cable.  Waya ce wacce bayanai ko sauti ke iya wucewa ta cikinta, ba wutar lantarki ba kadai.

Sai kuma Stabilizer, wanda duk na tabbata mun san shi, da irin aikin da yake yi.  Banbancinsa da UPS shi ne; shi UPS kan yi sa’a guda ko minti talatin ko goma ko kuma mintuna biyar (ya danganta da girman mizaninsa), yana rike da wuta.  Amma shi Stabilizer, aikinsa shi ne auna iya gwargwadon wutan da ake bukata, amma da zarar an dauke wuta, shi ma ya tafi kenan.  Shi a kan yi amfani da shi ne don TV, ko Rediyo da wasu kayayyakin lantarki da ba kwamfuta ba.  Bayan wadannan, sai kuma kujeru da tebura da ake zama a kai.

- Adv -

Kashi na karshe cikin abin da ake samu cikin mashakatar lilo da tsallake-tsallake, shi ne ma’aikatan da ke tafiyar harkokin kasuwancin da ke ciki.  Su ma kashi-kashi su ke; akwai injiniyoyi masu lura da kwamfuta idan an samu matsalar daukewar sigina ko lalacewar kwamfuta (ba dukkan mashakata ba ne ke da wanann).  Sai kuma masu karban kudade da sayar maka da lokacin lilo.  Suna yin hakan ne ta hanyar bayar da tiketi, wanda ke dauke da lambobi ko bakake.  Idan ka zo kan kwamfuta sai ka shigar da su, don ka samu mashigi.  Wannan tikiti ne zai rika kididdige maka yawan lokacin da ya rage maka.  Hakan na faruwa ne saboda su na amfani ne da wata masarrafa da ke fuskan kwamfuta; idan ba ka da wadannan lambobin da ke dauke a saman tikiti, babu shiga kenan.  Wannan manhaja ana kiransa  Cyber Lock.  Kamar yadda bayani ya gabata ne, cewa wasu mashakatar ba su kai wasu ba.  Don haka, a wasu wuraren ma za ka samu mutum daye ne ke komai (komai da ruwanka kenan).  Wasu ma ba su da Cyber Lock; da agogo ake kididdigan lokacin da ka ci.  Dankari!

Aikace-Aikace

Bayan sanin abubuwan da ke cikin mashakatar lilo da tsallake-tsallake, yana da kyau mai karatu ya san shin wani irin aiki su ke yi ne?  Eh, na san na sanar da mu cewa waje ne na shiga Intanet, na kuma san da dama cikin masu karatu sun san yadda tsarinsa yake to amma ta yaya abin ke kasancewa?  Shi Cyber Café waje ne mai tattare da aikace-aikace da dama.  Duk da cewa shiga Intanet a ke, a wasu wuraren za ka samu abubuwa da dama.  Wasu sun fadada mashakatar zuwa abin da a yanzu mu ke kira Business Center (ko Cibiyar Kasuwanci, a Hausance).  Za a iya buga maka bayanai (Printing); za a iya layance maka ID Card ko wasu takardunka masu muhimmanci (Lamination), ko a daukan maka hoton hutunanka, don ka samu sanya su cikin kwamfuta (Scanning) da dai sauran aikace-aikace.  Har wa yau, a mashakatar lilo da tsallake-tsallake ka na iya kwana ka na lilo a giza-gizan sadarwa (Overnight Browsing).  Bayan nan, kana iya buga waya (Phone Calls), ko ka sayi katin wayar salula (Recharge Card), ko kuma a sawwara maka takardunka (Photocopy).

A wasu manyan mashakatar lilo da tsallake-tsallake da su ka kasaita a manyan birane irin su Kano da Kaduna da Jas, da Uwa Uba Abuja, ana sayar da abin makulashe (cin-cin, lemon kwalba, alawa dsr).  In ka na bukatar gidan yanan sadarwa na kashin kanka, suna iya gina ma ka, ka biya su.  Kai idan ma so kake ka rika shiga Intanet a kwamfutarka da ke gida,  za su iya jona ka hanyarsu, kana biyansu duk wata.  A takaice dai mashakatar lilo da tsallake-tsallake wuri ne mai tara jama’a (na gari da na banza), kuma yaduwarsa na rage yawan marasa aikin yi a gari (musamman birane), kuma ya na daga cikin manyan hanyoyin yaduwar arziki.  A karshe kuma, makaranta ce babba, wacce sanadiyyarta da dama sun iya amfani da fasahar sadarwa irin tarho, kwamfuta da sauransu.

Shawarwari

Bayan duk mun ji wannan, zai dace har wa yau mu lura da wasu abubuwa, musamman ga masu taifyar da irin wadannan wurare, domin akwai bata-gari.  Ba wasu ba ne kuwa illa masu zuwa suna aiwatar da harkokin harkalla na abin da ya shafi kasuwancin karya, da sunan wai su a kasashen waje su ke.  Wadannan, idan mai karatu bai mance ba, su na daga cikin wadanda muka kawo bayanai a kansu cikin kasidarmu mai taken: “Spam”: Don Kawar  Da Bakin Haure! Mayaudara ne da ke tafiyar da sana’ar sata da zamba cikin aminci ta hanyar fasahar Intanet.  Kuma kashi casa’in da biyar cikinsu na amfani ne da mashakatar Lilo da tsallake-tsallake.  Wannan ta sa hukumar Yaki da Zamba Cikin Aminci wato EFCC ta kulla da su.  Ta bi kusan dukkan ire-iren wadannan mashakatar lilo da tsallake-tsallake tai musu rajista, don taimaka musu kame ire-iren masu wannan ta’ada, musamman a birane irinsu Legas da Abuja da Ibadan da Kaduna da Jas da sauran birane.  Duk wanda aka san shi da wannan ta’ada, lallai dole ne a yi hankali da shi.

Har wa yau akwai barayi masu shiga don ganin irin kalolin mutanen da ke shiga, idan ka fita a bi ka a kwace maka kudade.  Su ma galibi a manyan birane ake samun su.  Sai kuma kananan barayi (‘yan tsintau) masu sace ma jama’a wayoyin salularsu.  Dole ne a rika lura da masu shigowa suna yin lilo na Allah-da-Annabi, da masu shigowa don kailula da walagigi.  Kai ma mai zuwa wajen, dole ka rika lura da aljihun ka; duk abin da ka san ka je da shi wajen, ka lura da shi.  Kuma mu daina zuwa don nuna takama da “son cinyewa”; shi ne, mutum yayi shiga irin ta takama da nuna cewa “ni mai kudi ne ko sukuni”.  Galibin masu yin haka za ka samu samari ne irin mu (‘yan talatin da biyar zuwa kasa), kuma duk don ‘yan mata masu zuwa wajen ake yi.  Wannan ke sa wa ka ga mashakatar tsallake-tsallake ta zama kamar wata daba ta samari da ‘yan mata.  Duk sai a rika lura da abin da zai kawo zaman lafiya da samun arikizi, ba abin da zai kawo tir ba.

Kammalawa

Daga karshe, za mu dakata a nan, sai wani mako.  Duk abin da ba a fahimta ba a yi kokarin tambaya.  In Allah Ya yarda za mu taimaka da bayanai iya gwargwadon fahimta.   Kada a mance da Mudawannar Fasahar Intanet da ke: http://fasahar-intanet.blogpsot.com.  Ina mika gaisuwata ga dukkan masu karatu.  Sai wani mako.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.