Rayuwar Tauraron Dan Adam A Cikin Falaki

Idan aka harba tauraron dan adam cikin falaki, wani irin rayuwa yake yi? Me da me yake bukata don gudanar da rayuwarsa? Wadannan su ne mahimman abubuwan da kasidar wannan mako za ta mana darasi a kai. Kashi na hudu kenan cikin jerin kasidun dake mana darasi kan tauraron dan adam.

527

Tsarin Tafiyar da Tauraron dan Adam

Bayan tauraron dan Adam ya samu kansa a cikin falaki, ba abin da zai ta yi sai shawagi don gudanar da aikinsa, sai in matsala ya samu.  Tsarin tafiyar da tauraron dan Adam a cikin falaki yana bukatar abubuwa kamar haka:

Wutar Lantarki

Kowane tauraron dan Adam akan kera shi ne tare da makamashin da zai rika gudanar da rayuwarsa da shi.  Don haka a yayin da kumbun harbawa ya harba tauraron zuwa cikin falaki, da makamashinsa ya tafi.  Hanyar samun makamashin kowane tauraron dan Adam ya kasu kashi biyu ne; akwai makamashi na farko wanda yake a siffar batir ne.  Wannan batir shi ke samar da wutar lantarkin da ke tafiyar da injin roken din da yake dauke da shi.  Galibin amfanin wannan batir cikin dare ne, ko lokacin da babu hasken rana, musamman da yamma.  Amma da zarar rana ta hasko, akwai wasu fika-fikai da aka kera masa; hagu da dama, masu dauke da faya-fayan taskance makamashin hasken rana (solar radiation panels), suna sarrafa injin.  Wannan shi ne hanyar samar da makamashi na biyu.

Da wadannan hanyoyi kowane tauraron dan Adam ke rayuwar da yake yi a sararin samaniya.  Kowane tauraron dan Adam akan kera masa batirinsa ne iya gwargwadon girma da kuma dadewansa yana shawagi a cikin falaki.  Haka ma faya-fayan da ke taskance masa makamashin hasken rana, dole su zama manya masu fadi.  Misali, tauraron dan Adam mai suna The Hubble Space Telescope, mai dauke da na’urar hangen nesa da bayaninsa ya gabata a makon jiya, yana dauke ne da fankacecen faifan taskance hasken rana wanda fadinsa ya kai murabba’in mita 290 (290 sq m), kuma yana taskance hasken rana da kimarsa ya kai watt dubu biyar da dari biyar (5,500 watts).  Wadannan fika-fikai na budewa ne da zarar kumbon harba tauraron ya cilla shi cikin falaki, sai su bude, don fara gudanar da aiyukansu.  Wutar lantarki, wanda ke samuwa ta hanyar makamashin da ke batir ko na hasken rana, shi ne abu na farko kuma mafi muhimmanci da kowane tauraron dan Adam ke bukata.  Sai abu na gaba.

Yanayin Shawagi

A yayin da tauraron dan Adam ya samu kansa cikin falaki, dole yana da jiha ta musamman, ko yanayi na musamman da yake kasancewa cikinsa.  Wannan yanayi shi ake kira Satellite Orientation.  Da zarar ya fara shawagi, yakan bude fuka-fukansa ne suna fuskantar rana (don taskance masa makamashin da yake bukata), sannan ya juya na’urorin daukan bayanansa (Antennas and sensors) zuwa jihar wannan duniya tamu, ko kuma dukkan abin da aka harba shi don yin nazarinsa.  Idan tauraron sadarwa ne (communication satellite), sai ya fuskantar da na’urar daukan bayanansa zuwa wannan duniya; idan na lura da yanayi ne, zai fuskantar da kemararsa ne shi ma zuwa wannan duniya tamu;  amma idan tauraron binciken sararin samaniya ne, zai fuskantar da na’urar hangen nesansa ne zuwa halitta ko duniyar da aka aike shi yin nazarinta.  Har wa yau, kowane tauraron dan Adam na dauke ne da inji na musamman, wanda ke taimaka masa tabbatuwa a jiha ko yanayin da zai taimaka masa yin aikinsa.

- Adv -

Yanayin Muhallin Shawaginsa

Kamar yadda bayanai suka gaba a fakon wannan silsila, taurarin dan Adam na fuskantar kalu-bale iri-iri a yayin da suke shawagi a cikin falakinsu.  Wannan dole ne ya faru, domin da farko dai, an kera su ne da wasu maddodi (karafa ko gilasai) wadanda ba za su iya jure wa muhallin da aka jefa su ciki ba har abada.  Sannan, idan ma suna iya jurewa, na dan wani lokaci ne; dole wata rana na zuwa da zasu kode, har su rasa ingancin da zai basu damar jure wa muhallin da suke cikinsa.  Idan aka cilla tauraron dan Adam cikin falaki, kalu-bale na farko da zai fara karo dashi shi ne na tsananin zafin rana, wacce ke haskowa, tare da darkake shi babu kakkautawa.

A cikin falaki, tauraron dan Adam ba shi da inuwar da zai iya fakewa don shan inuwa. Bayan nan, shi kanshi yana dauke ne da wasu injina na roket, masu haddasa masa tsananin zafi sanadiyyar aikin da suke yi ba kakkautawa.  Abin da ke taimaka masa kawai shi ne, an yi masa wani inji da ke sanya shi mazayawa lokaci-lokaci, don baza zafi da tururin da ke damfare dashi, ta hanyar jujjuyawa.  Wanda in da a wuri guda yake tabbace a kullum, zafin  na iya haddasa masa illa mai tsanani.  Sannan idan yamma tayi, wata ya hasko, akwai tsananin sanyi da zai sake darkake shi, tare da rage masa inganci.  Bayan haka, a can sararin samaniya, ba irin nan duniya ba, akwai iska mai tsananin karfi da ke bugawa babu kakkautawa.  Idan da rana ne, wannan iska kan rikide tare da zafin rana; haka idan da dare ne, sai  ta rikide tare da sanyin dare. A daya bangaren kuma, akwai taurarin da kwanakinsu ya kare, suka farfashe, balgacen su kan warwatsu cikin falaki; wasu su fado cikin duniyarmu, kamar yadda bayanai suka gabata a baya, wasu kuma su ta shawagi a cikin falaki.  A yayin shawaginsa, tauraron dan Adam kan ci karo dasu, har su kwakkwafe shi, ko su babbale masa fuka-fukansa, ko kuma su haddasa masa wata illa babba da ka iya hana shi ci gaba da aiyukansa.

Yanayin Shigowa Duniya

Dangane da yanayin rayuwa da yin zamani a cikin falaki, tauraron dan Adam ya kasu kashi uku; akwai wadanda ke yin shawaginsu har su gama ba tare da samun wata matsala ba.  Idan suka gama rayuwa da shekaru ko muddar da aka yanke musu, sai su nemi hanyar shigowa duniya da kansu.  Da zarar sun kutso sararin samaniya (earth’s atmosphere), sai su kone  gaba daya.  Idan kuma rayuwarsu bata kare ba, amma akwai na’urorin da ake son cirewa daga garesu don sarrafa bayanan da suka taskance, sai ayi amfani da kwarewa ta kimiyya, a harbe injin da ke sarrafa tauraron, nan take sai ya rage gudunsa, ya fara saukowa cikin duniya da kansa, har a riske shi.  Sai kashi na uku, wadanda injinsu ko wasu sassansu masu muhimmanci ke lalacewa, su daina aiki, kawai sai su “haukace”, su yi ta shawagi ba-kai-ba-gindi, cikin falaki.  Wadannan su ake kira space junk, wato sun zama sharan cikin falaki kenan.  Haka za su yi ta kai-komo har su kone.

Sannan, iya girma da rashin nauyin tauraro, iya saukin da zai samu wajen shigowa duniya; iya gajarta da nauyinsa, iya wahalar da zai sha wajen shigowa, saboda tasiri da karfin iska da ke janyo jiki zuwa kasa. Iya nisan tauraro da duniya, iya yawan shekaru ko lokacin da zai iya daukawa yana shawagi.  Taurarin da ke shawagi a falakin da bai wuce nisan kilomita dari biyu ba, basu wuce mako guda zuwa watanni uku suna shawagi a ciki.  Wadanda ke iya nisan kilomita dari uku kuma, suna iya yin shekaru biyu ko fiye da haka.  Idan tauraro ya kai nisan kilomita dubu daya kuma, yana iya shawagi a cikin falaki na tsawon shekara dubu ko fiye da haka.  To ko ma dai a ina yake, da zarar kwanakinsa sun kare, dole ya nufo gida.  In ya iso lafiya alhamdulillahi.  Idan kuma kwanaki sun kare, sai ya kone a yayin shigowarsa, ko wasu sassansa su daina aiki sanadiyyar dimbin kalu-balen da ke samunsa a can, har ya zama shara, wacce iskar falaki ke dibansa na iya wani zamani, kafin ya kwanta dama.

Wannan shi ne dan abin da ya samu, kan abin da ya shafi bincike kan tauraron dan Adam da tsarin tafiyar da aiyukansa.  Abubuwa ne masu ban mamaki, kamar yadda mai karatu ya ji kuma ya karanta.  Amma abin da ya fi komai mamaki shi ne, wanda ya halicci mai wannan tunani, wato Allah.  Idan wannan bayani ya bamu mamaki, to mu san cewa ikon Allah shi yafi komai zama abin al’ajabi.  Don shi ne wanda ya halicci dan Adam din da yayi tunanin kirkiran dukkan wadannan abubuwa da bayanansu ya gabata, da kuma halittun da ake gudanar da binciken kansu.  Idan muka dubi hatta wadannan taurarin dan Adam din, sai mu ga ai kwaikwayon halittar Ubangiji aka yi, don samun ci gaba.

Allah Yai mana afuwa, Ya kuma sa mu dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.