Sakonnin Masu Karatu (2009) (7)

Daga wannan mako in Allah ya yarda zamu rika kawo wasikun da kuke aiko mana iya gwargwadon hali, don kauce wa taruwansu.  A nan zamu rika amsa wasu cikin tambayoyin da kuke yi, tare da nuna godiya kan wadanda kuka aiko don nuna gamsuwarku.  Sai a ci gaba da kasancewa tare da mu.

112

Assalamu Alaikum, ina yi maka fatan alheri tare da addu’a a gareka a bisa namijin kokarin da kake yi wajen fadakar da mu ta hanyar Intanet.  Allah kara maka kwarin gwiwa amin.  Don Allah Malam ina so kayi min bayani kan yadda duniya take juyawa, da bayani a kan “gravity”.  Sako daga Yusif Chamo, Kano: 08030413951

Malam Yusif Chamo barka da war haka, kuma muna godiya da wannan karfin gwiwa da ka kara mana.  Allah saka da alheri kai ma, amin.  Bayani kan yadda duniya ke juyawa (earth revolution) na bukatar bincike natsattse, kuma in Allah Ya so zamu yi iya abin da ya sawwaka wajen kawo hakan.  Dalili kan hakan shi ne, akwai sakamakon binciken da turawa suka yi kan haka, wanda galibi shi ake karantar da ‘ya’yanmu a makarantun zamani, wanda kuma daga baya bayanai sun nuna cewa akwai nakasar  inganci kan wadannan bincike da aka yi, shekaru da dama da suka gabata.  Har wa yau, sakamakon juya hankali da wasu kwararru suka yi daga tsarin binciken turai, zuwa bayanan da Alkur’ani ya kawo kan yadda tsarin da duniya ta samu, da yadda take gudanuwa, an samu bambancin ra’ayi da sakamako tsakanin wadannan masu bincike.  Dukkan wannan na bukatar kyakkyawar nazari da tantancewa, wanda bazai samu ba cikin dan kankanin lokaci.  Allah sa mu dace baki daya, amin.


Salamu alaikum Baban Sadiq, tambaya ta a nan ita ce, a kan tashoshin rediyo na wayar salula (mobile phone radio frequency band); na ga duk sun fi amfani da tsarin FM (Frequency Modulation), a kan AM (Amplitude Magnification).  Malam akwai masu amfani da AM kuwa?  Allah taimaki malam da daliban wannan shafi mai albarka na Kimiyya da Fasaha, amin.  Aliyu Muktar Sa’idu, Kano: 08034332200, 07025815073

Malam Aliyu barka da kokari, kamar yadda aka saba, muna kuma kara godiya ga irin kokarin da kake wajen lura da wannan shafi mai albarka.  Wato kamar yadda ka sheda, cewa akwai tsarin tashar rediyo na wayar salula mai suna FM, ba shi kadai bane, akwai wayoyin salula masu rediyo mai tsarin SW (Short Wave), wato “Gajeren Zango”, duk da yake suna da tsada kwarai da gaske. Da irinsu kana iya kama tashoshin BBC da VOA da sauran tashoshin da ke kasashen waje.  Dangane da wayoyin salula masu tsarin AM, ban taba cin karo dasu ba, kuma ban samu labari kansu ba, ta yiwu ba a fara kera irin su ba, ko ma baza a kera irinsu ba – domin tsohon yayi ne. Amma wannan baya nufin baza a iya bane, ya danganta da yanayi da kuma zurfin bincike. 

Abin da ke faruwa shi ne, duk wata sabuwar fasaha da ka ga an sanya wa wayar salula, yin hakan bai samu ba sai da aka gudanar da bincike kan yadda tsarin zai tabbata, ba tare da ya yi mummunar tasiri kan asalin aikin wayar ba.  Misali, zai yi wahala ka samu wayar salula mai tsarin sadarwar tashar rediyo ta FM da kuma SW a lokaci guda.  Mai yasa?  Watakil an gwada, sai aka lura yin hakan na iya haddasa matsalar sadarwa ga wayar baki daya, dole a cire daya a bar daya.  Ba abin mamaki bane nan gaba a samu, amma sai bayan dogon bincike, mai daukan lokaci.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu Alaikum Baban Sadik, ba abin da zan ce maka sai Allah Ya saka maka da alheri.  Domin a dalilin bayanin da kayi mana na yadda ake shiga Intanet ta hanyar wayar salula, a yanzu na kan shiga tashar Sashen Hausa na BBC don sauraran labaransu kafin ma lokacin yada shirye-shiryensu yayi.  Haka kuma nakan shiya gidan yanar sadarwa ta Harun Yahya – www.harunyahya.com – da na MTN – www.mtnonline.com – da dai sauransu.  Ba abin da zan ce maka sai Allah saka da alheri.  Daga Muhammad Abbas, Lafiyan Bare-bari, Nassarawa State: 08036647666

- Adv -

Malam Abbas, mun fi ka farin ciki da jin haka, wannan ke nuna cewa abin da ake gabatar muku a wannan shafi yana yin tasiri matuka; wanan shi ne abin da ake so, kuma dalilin assasa shafin kenan.  Sai a ci gaba da amfana da wannan tsari ta hanyar da ta dace, don samun ilimi da fadakarwa mai amfani.  Muna kara godiya da wannan wasika taka. 


Salamu alaikum Baban Sadik, ita na’ura mai kwakwalwa (computer) bata da bera ne (mouse)?  In akwai, to yaya aikinsa yake ne?  Kuma allon rubutu (keyboard) shi ma ya aikinsa yake?  Malam, idan aka ce ba daya daga cikinsu, shin kwamfuta za ta yi aiki kuwa?  Kuma wanne yafi muhimmanci gareta wajen sarrafa ta?  Daga Aliyu Muktar Sa’idu, Kano: 08034442200

Dara taci gida kenan!  Malam Aliyu shafin Kimiyya da Fasaha na mamakin samun wannan tambaya ta farko daga gareka, ai tun shekarar da ta gabata muka gabatar da bayanai shafi guda kan Beran Kwamfuta; tarihi da na’uka da kuma yadda yake aiki.  Watakil baka samu wannan kwafe ba!  Kana iya samun kasidar a wannan rariyar: http://fasahar-intanet.blogspot.com/09/2008/beran-kwamfuta-computer-mouse.html.  Dangane da allon shigar da rubutu kuma, fasaha ne mai dauke da dabarun sadarwa tsakaninsa da allon kwamfuta, wato “Motherboard”.  Shi ne shahararren hanyar shigar da bayanai cikin  kwamfuta kai tsaye.  Ai ko tantama babu; allon shigar da bayanai yafi beran kwamfuta amfani ga kwamfuta.  Domin idan babu beran kwamfuta, kana iya sarrafa kwamfuta kai tsaye; ka bude masarrafar da kake so, kayi rubutu, ka rufe, sannan in ta kama ma kana iya buga bayanan da ka rubuta (printing) cikin sauki, duk ta hanyar allon shigar da bayanai. 

Sai dai ba kowa zai iya hakan ba, musamman a yanzu da mutane suka shagwabe wajen amfani da beran kwamfuta.  Da zarar ka kawo kwamfuta babu beranta, ka sanya su cikin garari.  Idan muka yi la’akari da tsohuwar babban manhajar kwamfuta ta kamfanin Microsoft mai suna DOS (Disk Operating System), ai bata bukatar beran kwamfuta.  Da allon shigar da bayanai ake kunna ta, a shiga inda ake son shiga, sannan a fita, zuwa kashe kwamfutar.  Da fatan ka gamsu.


Salamun alaikum, da fatan kana lafiya.  Kokarin da ya kamata Malam yayi mana shi ne, dukkan littafan da aka rubuta su da Hausa kan fannin Kimiyya (da Fasaha), irinsu likitanci, da kanikanci da sauransu.  In har sun shiga hannunka, ka dora mana su a shafin Kimiyya da Fasahar a Intanet, don amfanin dukkan daliban da suke wannan makaranta, a ko ina suke a duniya.  Ka huta lafiya. Daga dalibinka Sani Abubakar (Na ‘Yan Katsare), Jas: 08026023796

Malam Sani kwana biyu mun ji ka shiru, da fata kana cikin koshin lafiya, amin.  Wannan shawara taka na da muhimmanci, musamman ganin irin bukatun da muke tattare da su kan samuwar wadannan fannoni cikin harshen Hausa.  Sai dai aiki ne mai wahala: daga abin da ya shafi samun littafan, zuwa kan kwafansu ko rubuce su a kwamfuta, zuwa tsara  gidan yanar sadarwar da zata dauke su, da dai sauran abubuwa.  Zan yi iya kokari na kan haka, amma kada a dauki wannan a matsayin alkawari mai kiyastaccen lokaci.  Sai yadda ta kasance, iya halin da na samu kai na da wadanda zasu iya taimaka mani. 

Watakila ma sai na hada da dukkan daliban wannan shafi in Allah Ya yarda.  Mun gode da wannan shawara, kuma muna mika gaisuwarmu ga dukkan daliban wannan shafi da ke garin Jas da Gumel da Kano da Kaduna da Fatakwal da Nasarawa da Bauchi da Birnin Kebbi da Sakkwato da Legas sauran wurare.  Allah sa mu dace baki daya, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.