Sakonnin Masu Karatu (2010) (1)

Sakonnin masu karatu:


Baban Sadik, don Allah ka mana bayanin abin da ke faruwa: wasu lokuta mukan ga taurari da yawa a sama, wasu lokuta kuma mu gansu kadan.  Me yasa? – Salisu Nagaidan, Jama’are: 08063461480

 

Malam Salisu a yi hakuri, a mako mai zuwa in Allah ya yarda akwai bayani kan taurari, musamman, daga cikin wannan littafi da muke fassarawa.  Kada in wuce mai kidi da rawa.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare da mu.


Salam, dan Allah yaya zan shigar da Imel dina a cikin wayata. Yau na bude Imel din nawa.  Na gode.  – 08063435035

 

Ya danganci irin wayar da ake amfani da ita. Idan babbar waya ce irinsu Blackberry, ko jerin wayoyin salula nau’in Nokia Eseries ko Nseries misali, sukan zo da manhajar Imel ta musamman, wacce ake amfani da ita don saukar da dukkan sakonnin Imel da suke shigowa cikin jakar Imel dinka/ki, a kowane lokaci ne kuwa.  Amma idan gama-garin waya ce mai amfani da Intanet, sai a shiga wannan rariyar http://mobile.yahoo.com/mail Da zarar an shiga wannan rariya, za a ga shafin Imel na Yahoo, sai a matsa inda aka rubuta “Mail”, a shigar da suna da kuma kalmomin iznin shiga (Username & Password), za a samu sakonnin Imel din da aka turo.  Da fatan ka/kin gamsu.


Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina fatan an tashi lafiya.  Don Allah ina neman shawara gare ka.  Ina son in karanci kwas din Farfajiyar Sararin Samani, amma ban san wane Jama’i zan je ba.  Na gode.  – 07066094903

 

Wato al’amari makamancin wannan yana bukatar bincike ne cikin jerin kwasakwasan da kowace Jami’a ke gudanarwa a nan kasar.  Hakan zai zama maka da sauki idan ka dauki littafin jadawalin kwasakwasai da Hukumar JAMB ke baiwa dalibai masu rubuta jarabawar shiga Jami’a, wato Universities Course Brochure.  Allah sa a dace, ya kuma ba da sa’ar karatu lafiya, amin.


Salam Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Dan Allah mene ne bambancin wayar Blackberry da sauran wayoyin Nokia masu Intanet?  Shin, da akwai wani abu ne da ke cikin wayar Blackberry wanda babu a cikin wayar Nokia?  Idan akwai, to mene ne wannan abin? Sannan kuma mene ne amfanin wayar Blackberry din? – Ibrahim Aminiya: 07065601581

 

Malam Ibrahim ai wannan tambaya taka tuni muka amsa ta cikin kasidar da muka gabatar kan wayoyin salula nau’in Blackberry. Don haka in da hali, ka je shafin Mudawwanarmu da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com don samun wannan kasida.  In kuma ba hali ka aiko da adireshin Imel dinka sai in tura maka kasidar baki dayanta. Ina saurarenka.  

Baban Sadik

Baban Sadik marubuci ne, kuma mai bincike a fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani da tasirinsu ga al'umma a kasashen Afrika, musamman Najeriya. Ya tanadi wannan shafi ne don taskance dukkan kasidun da yake gabatarwa a shafinsa na jaridar AMINIYA mai take: "Kimiyya da Kere-kere," wanda ya faro tun shekarar 2006; shekaru goma kenan a takaice. Bayan kasidun shafin jarida, wannan shafi har wa yau yana dauke da wasu kasidun da ya gabatar a tarurruka da aka gayyace shi, ko wasu hirarraki da gidan rediyon BBC Hausa yayi dashi a lokuta daban-daban. Baban Sadik na zaune ne a birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *