Sakonnin Masu Karatu (2010) (10)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

115

Dan Allah Baban Sadik ina son ka yi min bayani a kan hanyar kasuwanci ta na’ura mai kwakwalwa, watau “Forex Trading”.  –    Usman Aliyu Gobirawa Sokoto

Malam Usman barka da warhaka, da fatan ana lafiya.  A gaskiya bayani kan yadda ake tafiyar da “Forex Trading” na bukatar dogon bayani don samun gamsuwa.  Don haka idan Allah Ya kai mu bayan Salla za mu gabatar da bayanai kan amfani da hadarorin da ke tattare da wannan tsarin kasuwanci da dai sauransu.  Allah sa mu dace, amin.


Salamu Alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: me ye bambancin motoci masu sitiyari a hannun hagu (left  driver) da masu sitiyari a hannun dama (right driver)?  – Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT), Kano) 08034332200

Malam aliyu ai bambancinsu a bayyane yake.  Idan kuma kana nufin dalilin samuwar hakan ne, to labarin ba a nesa yake ba.  A farkon lamari an fara kera motoci ne masu sitiyari a hannun dama, watau “Right Driver” kenan.  Dalilin yin hakan kuwa shi ne don sawwake wa direbobi tsarin tuki, ba tare da sun yi ta kartar dangan gidaje ko fadawa cikin kwatami ba a yayin da suke kokarin shiga kwana, ko kuma suka samu kansu cikin wani lungu.  Domin idan direba yana kusa da dangan da ke hannunsa na dama, to zai samu saukin ganin yadda tukinsa ke gudanuwa ba tare da matsala ba. 

Amma daga baya sai wasu kamfanonin kera motoci suka lura cewa, idan direba yana bangaren dama yana tuki, zai iya samun matsala a duk sadda ya zo yin kiliya (overtaking) ga wata motar da ke gefensa.  Watau maimakon ya zama yana kallon tsakiyar hanya don hango motar da ke tafe a yayin da yake yin kiliya, hakan ba ya yiwuwa saboda kasancewarsa a bangaren dama.  Don haka sai aka fara kera motoci masu sitiyari a hannin hagu, don sawwake wa direba a yayin da yake tuki  a babban titi.  Da fatan ka gamsu.


Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: me ye alfanun da ke tattare da umarnin da Hukumar Sadarwa ta Kasa, watau NCC ta baiwa kamfanonin sadarwa masu zaman kansu cewa su fara yin rajistan katin SIM din mutane; yaya tsarin abin yake, kuma ko wasu kasashe na da irin wannan tsarin?  – Aliyu Muktar Sa’idu (IT) Kano: 08034332200

Malam Aliyu wannan umarni da Hukumar NCC ta baiwa kamfanonin waya masu zaman kansu dai shi ne su fara yin rajistan katin SIM din kwastomominsu nan take, sannan kuma nan gaba duk wani katin SIM da za su sayar, to dole ne ya zama sun masa rajista kafin sayarwa ga jama’a.  Amfanin yin hakan dai shi ne don rage yawan zamba cikin aminci da sace-sace da kuma manyan miyagun assha da wasu bata-gari ke yi ta hanyar wayar salula. Domin a yanzu ba abu bane mai wuya mutum ya sayi katin SIM sabo, ya aikata aika-aikan da yake son yi  da shi, bayan ya gama ya jefar ko kona shi.  Hakan ne ya sawwake wa da dama cikin masu yin wannan assha samun saukin aiwatar da tsiyatakunsu. Domin babu yadda za a iya gano ko waye mai lambar kati kaza da kaza. 

To amma da wannan sabon tsari, duk wanda ya sayi katin SIM sabo, ko kuma yaje yayi rajistar katin da yake amfani da shi, to sunansa zai kasance cikin manhajar kamfanin wayar da yake amfani da katinsa.  Kuma nan take ana iya gano ko waye; da sunansa, da adireshinsa, da kuma tambarin hannunsa.  Akwai wannan tsari a kasashe da yawa, ba wai kasar nan ne kadai ta fara amfani da shi ba.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Assalaamu Alaikum Abban Sadik, wane bambanci ke tsakanin tsarin sadarwar rediyo na AM da kuma FM?  –  Khaleel Nasir Kuriwa Kiru, Kano: 07069191677

Malam Khaleel wadannan tsare-tsare ne guda biyu masu matukar tasiri wajen sadar da siginar rediyo da shirye-shiryensu tsakanin tashar sadarwa zuwa akwatunan rediyon jama’a.  Tsarin “Amplitude Modulation” ko “AM” a gajarce dai, shi ne tsarin da ke sadar da shirye-shirye a tashoshin da ke kadadar sadarwar da tazararsa ke tsakanin KiloHerzt 535 zuwa 1605.  Hakan kuma na yiwuwa ne ta hanyar cilla sauti ko murya a sigar maganadisun lantarki.  Duk wani akwatin rediyo da ke tsakanin wannan kadadar sadarwa (watau 535kHZ zuwa 1605kHz) duk zai iya kama wadannan shirye-shirye.  A daya bangaren kuma, tsarin “Frequency Modulation” ko “FM” a gajarce, yana aiwatar da sadarwa ne a kadadan sadarwar da ke tsakanin 88mHz zuwa 108mHz. Kuma sakonnin murya ko sautin na isa ga akwatunan rediyon ne ta hanyar maganadisun lantarki, kamar yadda yake a tsarin AM.

Daga bayanan da suka gabata, za mu fahimci bambanci wajen uku da ke tsakanin wadannan tsarin sadarwa guda biyu.  Na farko shi ne bambancin kadadan sadarwa; tsarin AM na tazarar 535kHz ne zuwa 1605kHz, a yayin da tsarin FM ke kadadar da ke tazarar 88mHz zuwa 108mHz.  Na biyu, tsarin AM na amfani ne da ma’aunin tazarar aika sauti na “KiloHerzt”, a yayin da tsarin FM ke amfani da ma’aunin aika sauti na “MegaHerzt”. Bambanci na uku kuma shi ne, dangane da tazara da saurin maimaituwa, tsarin AM ya fi cin dogon zango, wanda kuma hakan tasa iska ke cakuduwa da sautin da ake aikawa. Shi kuma tsarin FM yana aiwatar da sadarwa ne a gajeren zango, wanda kuma hakan ya haddasa masa saurin maimaituwa wajen aikawa da sautin, kuma aka wayi gari tsarinsa ya fi na AM ingancin sauti da tagomshi.  Da fatan an gamsu.


Assalaamu Alaikum, barka da warhaka Baban Sadik.  Wai shin, mene ne tasiri da illan gurbatattan mai (crude oil) din da ke malala a tekun Mexico (Gulf of Mexico) da ke Amurka ne?  Kuma ko wannan man da ake yadewa a saman tekun zai yi amfani in an sarrafa shi, ko kuma ya lalace kenan har abada?  – Uncle Bash, Jimeta, Yola: 07037133338.

Malam Bash barka da warhaka kai ma, kuma da fatan kuna cikin koshin lafiya.  Wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci, kuma tun sadda ka aiko nake ta kokarin tanadin gabatar da gamsasshen jawabi a sigar kasida ko makala mai dan tsawo.  Domin hakan ne zai taimaka wa mai karatu fahimtar yadda lamarin yake.  Don haka yanzu ma ba amsa zan baka ba, sai dai mu dan dada hakuri, akwai kasidu na tanada da zan yi nazari don fitar da makala mai kyau, mai dan tsawo kuma mai fa’idantarwa sama da jawabin da watakila zan bayar a dan kankanin shafin nan, in hakan na yi.  A min hakuri zuwa bayan hutun Salla.  Na gode.


Sallama, da fatan alheri ga Baban Sadik.  Shin, ko zan iya sanin shiyyar da wanda ya aiko min da sakon Imel yake?  –  Khaleel Nasir Kuriwa Kiru, Kano: 07069191677

Sanin shiyyar da aka aiko maka da sakon Imel abu ne mai wahala, musamman idan ba kwararre bane kai a fannin hada alaka a tsakanin kwamfuta da yadda tsarin sadarwa ke aukuwa a tsakaninsu.  Sannan kuma ya danganci irin manhajar Imel din da abokin huldarka ko wanda ya aiko maka da sakon yake amfani da ita wajen yin hakan.  Da farko dai, muddin kana son sanin daga ina aka aiko maka sakon Imel, to dole ne ka san tsurar adireshin kwamfutar da aka yi amfani da ita, watau “IP Address” kenan – gundarin adireshin kwamfutar nake nufi.  Kowace kwamfuta na dauke ne da adireshi wanda yake a jerin lambobi (misali: 235.75.4.9.0).  Da wadannan lambobi ne take amfani wajen aika sako ga wata kwamfuta ‘yar uwarta; a giza-gizan sadarwa ne ko a zangon sadarwa tsakanin gida ko ofis ko wata jiha ta musamman.

Idan daga Intanet aka aiko maka da sakon, to dole ne ka san wadannan lambobi, sai ka sansu sannan za ka iya sanin a inda kwamfutar take.  Domin dukkan kwamfutocin da ke dauke da gidajen yanar sadarwa a Intanet suna da adireshin da ke nuna daga kasar da suke, kamar yadda ka san kowace kasa tana da tsarin adireshinta na musamman.  Idan ba wadannan lambobi ka gani ba, kuma har ka iya tacewa tare da fahimtar kasar da ake danganta adireshin da ita ba, to  ba ka iya sanin haka.  Kuma ko da ma ka san kasar, ba lallai bane ya zama wanda ya aiko da sakon a kasar yake. 

Misali, akwai kamfanoni masu adana shafukan yanar gizo ko bayar da damar mu’amala da fasahar Intanet ta amfani da tauraron dan Adam, ire-iren wadannan kamfanoni a kasashen Turai suke, amma za ka samu galibin kamfanoninmu a nan na amfani da adireshin Nijeria ne (na gidajen yanar sadarwarsu) amma kwamfutocin da ke dauke da gidajen yanar sadarwar na wasu kasashe ne daban.  A irin wannan yanayin kuwa, sai dai kayi ta kirdado, amma ba wai ka san hakikanin inda aka aiko maka ba.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.