Sakonnin Masu Karatu (2010) (5)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

65

Assalamu alaikum, da fatan ka yi sallah lafiya.  Na karanta amsarka dangane da rajistan katin SIM.  To idan mutum ya ba da sunan karya da kuma adireshin karya ya zasu iya gane inda yake idan ya aikata mummunan halin shi?  Haka kuma wasu ma suna bayar da layin su ne aje a musu. Kuma za’a iya sace wayan wani aje a aikata abin da ake so da shi.  Wanda yin haka zai shigar da wanda bai san hawa ba bai san sauka ba cikin damuwa ya kuma tserar da mai laifin.  Kadan kenan daga cikin matsalolin yin rajistan SIM.  Ko hakan ma za’a iya hanawa? Suleiman Modibbo Jimeta. Yola, Adamawa.

Malam Suleiman wannan tsokaci naka yana da muhimmanci, kuma ma ban dauke shi a matsayin tambaya ba, domin amsar a fili take.  Tuni na tara bayanai don gabatar da kasidu kashi biyu kan wannan tsari da gwamnati ta kawo na yin rajistan Katin SIM, tare da matsalolin da ke tattare da yin hakan a Nijeriyance.  Don haka a dakace ni nan da ‘yan makonni.  Allah sa mu dace, amin.


Assalam alaikum Baba Sadik, rajistan layi na MTN, sai mutum ya je kamfanin MTN ko zai, iya kiran sashen kwamstoma ya yi rajista?   Daga Bashiru Umar Achida Iddo

Malam Basharu kowane kamfanin waya na da nashi tsarin na yin rajista, wanda kuma ya sha bamban da na sauran.  Kamar yadda na fada ne a sama, akwai bayanai da ke tafe masu gamsarwa kan wannan tsari.  Ban gama gudanar da binciken da nake kan yi bane shi yasa.  A dan yi hakuri zuwa wani lokaci kadan nan gaba.  Na gode.


- Adv -

Sallama da fatan alkhairi. Mallam wai meye takamaiman aikin Compass ne? Sannan kuma yar wayar nan ta yan sanda da kuma ta sojoji, tana da bukatar sai an zuba mata kudi ne (phone card)? Ka huta lafiya. Khaleel Nasir Kuriwa Kiru 07069191677

Malam Khaleel, abin da ake nufi da “Compass” dai wata na’ura ce mai kwakwalwar gano bigire, daga inda mutum yake rike da ita.  Sau tari sojoji da matafiya, da kuma masallata kan yi amfani da ita.  A wasu  lokuta idan kaje wasu Otal a kasashen gabas ko kasashen larabawa, za ka ga an ajiye maka ita a dakinka.  Idan kana son gano bigiren da kake nema; gabas, ko yamma, ko arewa, ko kudu, sai ka rike na’urar, za ka ga ta nuna maka bigiren da kake fuskanta.  Idan gabas kake fuskanta, za ta nuna maka gabas ta hanyar wani karamin sanda mai kan kibiya.  Wannan, a takaice, ita ce na’urar Compass.

Dangane da wayoyin oba oba da sojoji ko ‘yan sanda ke amfani da su kuwa, ba a sanya musu kudi ta hanyar kati kamar yadda muke yi da wayoyinmu a yanzu.  Sai dai zuwa kamfani ake yi a biya kudin layi ko cajin Magana da ake yi da su. Ire-iren wadannan wayoyi su ake kira Walkie-Talkie a turance, kuma a asali guda biyu kawai ake bayarwa, sai a rika aiwatar da sadarwa a tsakani, wato Two-way Radio kenan.

Amma daga baya sai aka samar da tsarin hada ire-iren wadannan wayoyi su rika sadarwa a tsakaninsu ko da kuwa sun kai dubu ne.  Bayan haka, wadanan wayoyi sun sha bamban da irin na zamani, domin suna da takaitacciyar tazarar sadarwa, wato Network Coverage.  Galibi ba su wuce tsakanin birni daya.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.