Sakonnin Masu Karatu (2011) (10)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

109

Salam Baban Sadik, don Allah ya zan bude “Memory Card” di na; duk wayar da na sa sai ta tambayeni “enter password”.  Daga Haruna Hotoro 08035307128

Malam Haruna, samun wannan sako a duk sadda ka yi kokarin bude wannan kati naka, alama ce da ke nuna cewa an tsare ta da wasu kalmomin sirri.  Idan sabuwa ce ka saya, kana da zabi; ko dai ka koma musu da ita su canza maka da wata, ko kuma ka matsa “Options” a jikin wayar idan ka zo inda tambarin katin yake, za ka ga inda aka rubuta “Format Memory Card”, sai ka matsa. Da zarar ka matsa, za a sanar da kai cewa duk bayanan da ke ciki za su goge, za ka ci gaba?  Sai ka ce eh.  Nan take katin za ta koma sabuwa, babu komai a ciki, kuma ba za a kara tambayar ka shigar da “password” ba.  Da fatan an gamsu.


Assalamu alaikum, suna na Umar Honestman, Numan, Jihar Adamawa. Baban Sadik don AllaH ina son ayi min bayani game da tauraron dan adam; ya yake? Kuma ya ake yi a turashi sararin samaniya da sauran abubuwan da yake tare da shi?

Malam Umar ai ka makara.  Watakila lokacin da muka kawo kasidu na gugan kasidu har wajen uku ko hudu kan Tauraron Dan Adam, ba ka kusa.  In da hali kana iya zuwa shafinmu da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com, don neman kasidar da muka rubuta kan haka shekaru biyu da suka gabata.  A ciki za ka samu cikakkun bayanai gamsassu dangane da wannan fasaha.  Ayi hakuri da dan abin da ya samu.  Na gode.


Babban sadik, yaya ake bude shafin facebook na kungiya? Ana kuma iya juyar da sakonni kan katin sim?  Ka huta lafiya. A.w. Ayagi

Baban Waraqaat barka da warhaka.  Bude shafin Kungiya a facebook ba shi da wahala. Ida ka shiga shafinka, ka je settings, ko ka duba daga hannun hagu can kasa, za ka ga inda aka rubuta “Create Group”, sai ka matsa.  Kana iya shigar da dukkan abokananka nan take.  Saukar da sakonni zuwa katin SIM kuma ban fahimci tambayar ba sosai.  Shin, sakonnin tes na wayar salula, ko sakonnin shafin facebook?  In dai na wayar salula ne ai ba wahala wannan, kana iya amfani da masarrafar wayar.  Idan Nokia ce kana iya amfani da “Nokia Suite” don saukar da su duka.  Amma idan na facebook ne, sai dai ka adana (save) shafin da ke dauke da sakonnin zuwa cikin wayarka, don ka rika budewa a duk sadda kake so.  Da fatan Baban Waraqaat ya gamsu.


Salam Baban Sadik, da fatan alkhairi. Dan Allah ina so kai min bayani kan yadda ruwan rijiya yake samuwa. Ka huta lafiya.  Da Usman s/mainagge: 08020731981

Malam Usman ruwan rijiya na samuwa ne asali daga ruwan sama da ke saukowa.  Idan ruwan sama ya sauka yakan kasu zuwa kashi uku ne a takaice; kashi na farko mutane da dabbobi su yi amfani dashi – mutane suna tara ne su sha ko yi harkokin gida da su, su kuma dabbobi su sha wanda ke taruwa a kududdufai da gulabe – kashi na biyu kuma ya jike kasa don ya shayar da shuke-shuke, su amfani da shi su ma, kashi na uku kuma ya shige can cikin kasa, shi ne wanda idan muka tashi hako rijiya muke samu.  Sannan daga irin wannan kaso ne ake samun idaniyar ruwa da ke bubbuga ba tare da an hako ta ba.  Akwai kashi na karshe wanda ruwa a saman tekuna da koguna a halin saukansa. 

- Adv -

Shi wannan kashi yana komawa ne ta hanyar iska, kamar yadda bayanai kan haka sun gabata tuni idan teku bai antayo shi cikin kasa ba kenan.  Idan kana son fahimtar wannan tsari cikin sauki ka shiga cikin Suratuz Zumar aya ta 21, za ka ga abin cikin sauki, musamman idan ka karanta ko saurari tafsirin wannan aya daga kwararren malami.  Wannan zai ba ka bayani kan asalin yadda lamarin yake, wanda shi ne asali kan dukkan bayanan da malaman kimiyya suka yi.  Da fatan an gamsu.


Asslaamu alaikum. Ina son don Allah mallam ya aiko min kasida, akan banbamci da ke tsakanin ayyukan wayar Nokia da Blackberry. Ga addreshin e-mail na: bashariibrahimgumel@gmail.com

Malam Bashir na san za ka ga shiru, wai malam ya ci shirwa.  A gaskiya babu wani bambanci na cancan nesa a tsakanin wayoyin biyu.  Na san ka karanta kasidar da muka gabatar kan wayoyin salula nau’ukan Blackberry, da kuma kasidar da aka gabatar kan Ayyukan Wayar Salula.  Bambancin da ke tsakaninsu kawai shahararru su ne kan tsarin gudanar da kira. Su wayoyin Blackberry idan ka buga lambar mutum don kiransa, sai ta cilla lambarsa zuwa na’urorin kamfanin wayar Blackberry da ke kasar Kanada, wato Research in Motion (RIM), daga nan kuma kamfanin ya cilla lambar zuwa kamfanin wayar da abokinka ke amfani da layinsu, sannan su kuma su nemo maka shi ta hanyar tsarin sadarwarsu, wato Network Service.  Sai kuma bambancin masarrafai da ke tsakaninsu, wannan kuwa wani abu ne da hatta a tsakanin wayoyin salula na kamfanin Nokia akwai bambanci.  Da fatan an gamsu da dan abin da ya samu.


Salam, dan Allah inaso ayi min cikakken bayani kan yadda ake amfani da “modem,” da kuma yadda zan iya bude blog di na a shafin intanet. Dr. R. M. Haidar Kano

Malam Haidar, shi Modem, ko makalutun sadarwa, wata na’ura ce da ke taimakawa wajen sadar da kwamfuta ko wayar salula da shafukan Intanet da ke giza-gizan sadarwa ta duniya. Idan ka makala wa kwamfuta wannan na’ura, ka nemi isa zuwa wani shafin Intanet misali, za ta karbo maka shafin ne ta hanyar wayar R11 da ke makale a jikinta, wato irin wayar da ake aiwatar da sadarwar tarho da ita kenan. Da zarar ta debo bayanan shafukan a matsayin bayanai, sai ta narkar maka dasu a fuskar kwamfuta dinka a matsayin rubutu ko hotuna ko bidyo, kamar yadda suke a asalin shafin.  A yanzu galibin kwamfutoci kan zo da wannan na’ura ne a cikinsu, ba wani abu bane da za ka iya gani a waje, musamman idan kana shiga shafin Intanet ta hanyar Gajeren Zangon Sadarwa wato Local Area Network. 

Amma idan na kamfanin waya ne ka siyo, to wannan kam dole sai ka makala wa kwamfutarka shi, don ka samu shiga.  Sannan har wa yau kana iya amfani da wayar salularka idan kana da kwamfuta, wajen shiga Intanet. Sai ka dauko wayar shigar da bayanai da ta zo da shi, wato USB cable, ka makala mata.  Kafin nan, dole ka tabbata akwai masarrafar wayar a kwamfutarka.  Misali idan wayar Nokia ce, ka tabbata akwai masarrafar “Nokia Suite” a cikin kwamfutar. Ta nan za ka je ka matsa alamar “Connect to the Internet”, don samun shiga.  Bayani kan yadda ake kera Blog kuma ya sha maimaituwa a wannan shafi. Sai dai a yi hakuri a je shafinmu da ke Intanet don neman kasidar. Da fatan za a yi hakuri da dan abin da ya samu.


Salamu alaikum Baban Sadiq, da fatan an wuni lafiya? Allah yasa haka amin summa amin. Dan Allah ina son katemakamun namanta password na Imail di na. User ID: bbycopshon@yahoo.com, kuma da wannan ID ne nake facebook. Dan girman Allah inda yadda za a yi a taimaka min a gaya min yadda zan yi na samo, ko kuma a binciko min. Wassalam ka huta lafiya.

Malam Ibrahim kamar yadda muka yi Magana a waya, har Allah yasa aka shawo kan lamarin na gyara maka ba wata matsala, zuwa nan gaba duk sadda ka manta kalmomin shiganka na kamfanin masarrafar Imel, ba za ka iya shawo kan lamarin ba sai ka san shekarar haihuwarka da ka shigar a lokacin da kake bude Imel din a farko, da tambayoyi guda biyu da ka yi wa kanka sannan ka amsa su, da amsar tambayoyin, wato “Security Question and Answer.”  Duk sadda mutum ya mance kalmomin shigansa, sai ya matsa inda aka rubuta: “Forgot Your Password?” ya shiga, za a bijiro masa da wadannan tambayoyi guda uku, sai ya amsa su sannan a bashi daman canza wasu sababbin kalmomin shigansa. Suna yin haka ne don tsaro, da kuma tabbatar da cewa lallai kai ne mai akwatin Imel din, ba wai wani bane yake son ya kwace maka ta hanyar canza su.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.