Sakonnin Masu Karatu (2011) (11)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

53

Salam, Baban Sadik tambaya ta ita ce: wai shin hasken walkiya ko cida suna da tasiri a kan irinsu janareto, da wayar salula, da talabijin, da dai sauransu?  Allah ya kara maka basira ameen. Daga Abdulmajid Saleh Gumel(Abu sa’ad)

Baban Sa’adu lallai hasken walkiya da cida suna da wannan tasiri mai girman gaske kuwa a kan wadannan na’urori da ka ambata.  Ba komai ya kawo haka ba sai don kasancewar su wadannan na’urori suna amfani da wasu hanyoyin sadarwa ne na musamman da suka shafi aikawa da sakonni ta hanyar iska da haske.  Wadannan abubuwa guda biyu kuwa suna da tafarkinsu da suke bi ne a sararin saman duniyan da muke rayuwa a cikinta. Abin da ya shafi wayar salula da talabijin da na’urar tauraron dan adam (wato Decorder), da wayoyin wutar lantarki, duk suna karba ko aikawa da sakonnin makamashin sadarwa ne ta hanyar siginar rediyo, wato “Radio Waves,” kuma duk wani abin da ya shigo tafarkin wannan tsarin sadarwa wanda ba jinsinsa bane, to yana yin tasiri mai girma a kanshi wajen jirkita shi ko canza masa amo da kima ko tsarin tafiya, tunda haske ne da ke cikin iska. 

Shi yasa idan ka kamo gidan rediyon Kaduna a misali sadda ake cida da walkiya, za ka ji tashar tana “cacacau…cacacau…kurrrrr,” da dai sauransu.  Alamar cewa an samu mishkila a tafarkin tsarin sadarwarta.  Su kuma na’urorin tashoshin tauraron dan adam, wato Decorder, sukan kone ne idan aka yi tsawa mai tsanani a halin suna kunne, ko da ba aiki suke yi ba.  Shi yasa yake da muhimmanci idan ana ruwa da tsawa, to ka kashe su, ka kashe rediyonka, in dai ba tashar FM kake sauraro ba, ka kuma kashe janaretonka, muddin ba wani abu mai muhimmanci kake yi ba.  Duk da cewa idan ba tsawa bane mai tsanani, bai cika tasiri a kan janareto ba.  Da fatan an gamsu.


Baban sadiq sannu da kokari, wai da gaske ne ruwan sama yana zuwa da kasa?  Musa mohd, b-dogo yankaba kano.

Malam Musa ban taba jin wanann bayani ba, ban kuma taba karanta hakan a ilmance ba.  Abin da na san ruwan sama kan zo da shi shi ne kankara, kamar yadda na san ka san wannan.  Amma ruwan sama ya zo da kasa, wannan ban karanta ko ji shi a ilmance ba.  Da fatan an gamsu.


Bayan gaisuwa, ina fatan kana lafiya. Ina son shiga shafin ‘Facebook’ da kuma yin ma’amala da shi. Yaya zan yi? Da fatan za ka taimaka mani. Abdulhamid Iliya

Malam Abdulhamid na san ya zuwa yanzu ka karanta amsoshi makamanta wannan da dama a wannan shafi, don haka ba sai na kara jaddadawa ba.  Musamman ma ganin cewa baka yi bayanin ta wace hanya kake son aiwatar da wanann mu’amala ba.  Ko ma ta wace hanya ce, bayanai dai sun gabata.  Don haka ne ma daga yanzu zan daina buga dukkan sakonni makamanta wannan, saboda maimaici ne.  Ina shawartan masu karatu cewa a duk sadda suka ga bayani kan wani abin da suke da sha’awa wanda wani ya tambaya aka bashi amsa, to su gamsu da amsar da aka bashi musamman in har abin da suke so na bayani iri daya ne da irin wanda aka amsa. 

Domin na sha amsa tambaya makamanciyar wannan, amma a duk sadda aka buga amsar tambayar, sai wani ya sake aiko tambaya irinta, a makon da aka buga; wanda hakan ke tabbatar da cewa wancan amsa ce ya gani, kuma yake son a bashi amsar tasa tambayar daban. Mu rika hakuri da abin da muka samu. Abin da yawa, wai mutuwa a kasuwa.


Baban Sadik ya aiki ya jama’a? Na ga tallarku ta GOOGLE+ a jarida, gaskiya na ji dadin haka. Dan Allah in an fara muna so a sanar da mu ta hanyar wannan lamba: 08038272720

Ai ba talla bace, fadakarwa ce irin wacce aka saba yi a shafin, kan duk wani abu sabo da ke samuwa a fannin sadarwa da kimiyya.  Don haka wancan kasida da ka/kika karanta fadakarwa ce, cewa ga wata sabuwar masarrafar Dandalin Abota da Zumunta ta samu, amma ana gwaji.  Don haka kana/kina iya ziyartar shafin masarrafar lokaci zuwa lokaci, don tabbatar da an fara amfani da ita ko a a.  Shafin na: http://plus.google.com da fatan an gamsu.


Allah ya saka maka da alheri, Allah kuma ya bamu irinku da yawa, amin.

- Adv -

Mun gode, mu ma muna godiya da wannan addu’a. Allah saka da alheri, ya kuma albarkace mu baki daya da albarkokin da ke cikin wannan wata mai alfarma, amin.


Salam. Ina fatan kana lafiya. Hakika ina da sha’awar zama mai ilmin sarrafa na’urar kwamfuta, wane matakin farko ne zan soma dauka? (Bin uwaisu).

To, matakin farko dai shi ne kaje makaranta ko duk wata cibiya da ake karantar da ilmin kwamfuta.  Dole sai ka fara samun karamar shahadar karatu, wato “Certificate” a fannin kwamfuta, sannan ka zabi bangaren da kake son kwarewa a kai. Don duk inda ake karantar da wannan ilmi, daga kwalejin fasaha har zuwa jami’a, da kuma cibiyoyin karantar da ilmi na masu zaman kansu, duk kana iya samu wannan kwarewa. Allah taimaka, ya kuma yawaita mana irinku a cikin al’umma, amin.


Asalamu alaikum Baban Sadik, na saita wayata a tsarin GPRS kamar yanda na ga kayi bayani a filinka, na kuma samu nasara.  Domin ina shiga facebook, amma sauran shafukan ba sa budewa. Shin ya zama dole sai na bude adireshin Imel?  Zakiru Elgusawiy, Suleja

Malam Zakiru ba ka’ida bace dole sai ana da adireshin Imel sannan ake iya mu’amala da fasahar Intanet a waya.  In akwai tsarin Intanet a wayar, kana iya aiwatarwa ba matsala.  Watakila dai baka sanya adireshin shafin da kake son shiga bane daidai.  Amma in za ka iya shiga shafin Facebook, wannan alama ce da ke nuna cewa lallai za ka iya shiga wasu shafukan ma. Ka dai dada duba adireshin shafin da ka shigar.  Da fatan an gamsu.


Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: kwanakin baya Najeriya ta taba jefa tauraron dan adam ya bace, ga wani za a sake jefawa.  Ai fashin-baki game da yadda ake jefa shi, ko kuskure aka samu a na baya ne?   Aliyu MukhtarSa’idu (I.T) Kano Email= aliitpro2020@yahoo.com 08034332200 08099109200

Malam Aliyu ai bayani kan yadda ake jefa tauraron dan adam zuwa sararin samaniya ya gabata da tsawo ma kuwa a wannan shafi, ina ganin dai so kake a yi bayanin irin tsarin da aka bi wajen tafiyar da namu tauraron da ya samu matsala.  Idan ba a mance ba, na kawo bayanai masu nuna cewa wancan tauraro mai suna “NigComSat 1” da aka ce ya bace a sararin samaniya, ba bacewa yayi ba. Ya dai samu matsala ne da fikafikansa masu taimaka masa da makamashin hasken rana, wato “Solar Panel” kenan.  Wannan ta sa ya daina aiki, har ya zama kamar “sharar sararin samaniya” wato “Space Junk” kamar yadda malaman ilmin sararin samaniya ke cewa.  A yanzu haka an dakatar da shi, yana can a sararin samaniya, haka zai gama shawaginsa ya kacalcale ya zama buraguzai har a rasa shi. 

Cikin makon da ya gabata ne aka jefa wasu guda biyu; da “NigeriaSat 2” da kuma “NigeriaSat R” daga kasar Rasha, don samun cinma manufofin habaka Najeriya a fannin kimiyyar sadarwa da likitanci da yada ilmi mai inganci a zamanance, kamar yadda shugaban kasa ya tabbatar a ranar da aka cilla wadannan taurari guda biyu.  Allah fisshe su da mu baki daya, amin. Da fatan Malam Aliyu ya gamsu.


Assalamu alaikum wa rahmatullah, Baban Sadiq barka da yau. Da fatan su Sadiq suna lafiya. Don Allah tambayata ita ce, na sayi laptop window 7, amma ba ta karbar printer 1020 leaserjet, kuma duk memory card na waya idan na sanya sai ta bata shi. Don Allah ina neman shawara. Wassalam. Daga Nu’uman Usman Katsina State.

Malam Nu’uman da farko dai ina neman afuwa, domin na so in baka amsar tambayarka daidai lokacin da ka aiko, amma ina shagalce sannan, kuma daga baya sai shedan ya mantar da ni, sai sadda na zo fitar da wasikun masu karatu zan amsa sannan na hango taka.  Dan Allah a gafarce ni.  Abu na farko dai shi ne, su na’urar Printer suna zuwa ne da faifan CD da ke dauke da “Drivers” dinsu, wato masarrafar hada alaka tsakanin kwamfuta da na’urar dabba’a bayanai kenan.  Shin, ka sanya wa kwamfutarka wannan “Drivers” din?  In har ka sa mata su, ya kamata a ce ta baka daman buga samfuriin shafin gwaji, wato “Test Page” kenan. Amma in har haka kawai ne ka makala mata na’urar don ka dabba’a bayani, ba yadda za a yi ta karba ai, tunda babu abin da ke hada alaka a tsakanin kwamfutar da abin da ka makala mata.  Ka sani, babbar manhajar Windows ta XP, ita ce kadai ke zuwa da ire-iren wadannan masarrafai kyauta a cikinta.  Amma Windows 7 sabuwar manhaja ce, kuma idan ka dubi na’urar LaserJet 1020, za ka ga tsohuwar Printer ce, ba lallai bane a samu masarrafanta a ciki. 

To amma kamar yadda na fada a baya, in har ka sa, amma ta ki amincewa da shi, to ya kamataka nemi kwararre kan harkar kwamfuta ya sa maka.  Idan shi ma ya buga abin yaki, ga  kuma matsalar bata katin MMC, to dole ne ka mayar da ita inda ka siyo, su canja maka da wata. Amma idan a hannun wani ka sayo bayan ya yi amfani da ita, to watakila daman can tana da matsala, musamman matsalar kwayar cutar kwamfuta, wato Virus. Wannan shi ne abin da nake tsammani.  Sai ka kai a sanya maka masarrafar kariya, wato “Anti-Virus”, sannan a goge su.  Allah sa a dace.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.