Sakonnin Masu Karatu (2011) (12)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

68

Dan Allah Baban Sadik ina bukatar dan takaitaccen bayani a kan layin nan na jikin taswirar duniya {equator}.  Bello Aliyu, belloaliyumani@googlemail.com

Malam Bello wannan layi na Equator da ake iya gani a jikin taswirar duniya, wato Global Map, wani layi ne da ba a iya gani a zahiri (Imagery Line), wanda ya raba kwallon duniya zuwa gida biyu a kwance; aka samu arewaci da kudancin duniya, wato “Northern and Southern Hemisphere.”  Wannan layi ya raba duniya ne daidai wa daida, daga wadannan bigirori guda biyu.  Masana sun zana wannan layi ne a jikin taswirar duniya sanadiyyar lura da aka yi cewa a duk shekara, rana kan cilla haskenta daga mafi kololuwar saman duniyarmu (wato “Zenith”) zuwa mafi karancin nisanta a kasa (wato “Nadir”), cikin dukkan watannin Maris da Satunba, daga fitowarta zuwa faduwanta. 

Wannan layi na Equator dai ya faro ne daga yammacin duniya zuwa gabashinta a kwance, inda ya raba kwallon duniyarmu zuwa gida biyu; daya a sama daya kasa misali.  Bangaren arewaci ne a sama, shi kuma bangaren kudanci yana kasa. Idan rana ta cillo ta kan maye kwallon duniyan da wannan layi yake kai ne; daga kasar Burazil, da Tekun Atilantika idan ka shigo nahirar Afirka, zuwa kasar Kenya, da Kongo Zayar, da Tekun Indiya (wato “Indian Ocean”), da Indonesiya, da Ekwado, da French Guina.  Tazarar nisan wannan layi na Equator daga inda aka kaddara farko zuwa karshensa dai ya kai nisan tazarar kilomita 40,030.20.  Kuma duk da cewa ba a ganin wannan layi a zahiri kamar yadda na sanar a farko, sai dai akwai alamu da wasu kasashe suka sa a daidai inda wannan layi na Equator ya ratsa kasashensu. 

A kasar Kenya akwai alamar da aka sa a garin Nanyuki, don nuna inda wannan layi ya ratsa.  A kasar Indonesiya akwai inda aka sa alamar a garin Pontianak, don nuna inda layin ya ratsa.  Idan muka je Tsibirin Sao Tome & Principe ma akwai alamar a garin Ilheu das Rolas.  A kasar Burazil akwai alamar mai suna “Marco Zero” da ke garin Macapa, inda layin ya ratsa. Masana sun tabbatar da cewa, akan samu ruwan sama mai yawa a duk shekara daidai inda wannan layi ya ratsa. Wannan shi ne dan abin da ya samu.  Da fatan an gamsu.


 Salam, Malam dafatan kana lafiya ya aiki da sauran hidimomi? Allah ya kara taimakawa. Na rubuto ne dan in kara jinjina maka a kan irin kokarin da kake yi. Allah ya kara basira, amin. A karshe muna addu’ar Allah ya bar mana kai dan cigaba da irin wanan kokarin. Daga almajirinka Hamza M. Djibo Niyame Jamhuriyar Nijar: alhamza_mjn@yahoo.fr

- Adv -

Alhaji Hamza muna amsawa kuma muna godiya da addu’o’inka kamar yadda ka saba.  Allah saka maka da alheri kaima, ya kuma albarkace mu baki daya, amin.  mun gode.  Mun gode. Mun gode.


Baban Sadik don Allah in Google+ sun ba da dama a bude shafi don Allah ka gaya min  ko da ta amiya ne. ahassanabba@yahoo.com

Malam Abba inshallah zan yi kokarin haka idan suka bayar da dama ga kowa da kowa.  Amma kafin nan, me zai hana ka je shafinsu da ke: http://plus.google.com don shigar da adireshinka na Gmail idan kana da ita, da zarar sun bude ga kowa da kowa, za su sanar da  kai.  Da yawa cikin mutane sun bayar da adireshinsu don a tuntube su. Domin ina iya shagala a matsayi na na dan adam. Da fatan za ka yi hakan, don ya fi tabbaci.  Allah sa mu dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, ina mika godiya a gareka a kan amsa tambayoyi da kasidun da kake rubutowa a  jaridar aminiya, da fatan Allah ya saka maka da alheri amin. Haka kuma ina rokonka da ka sanya ni a cikin wadanda kake tura wa kasidu masu ilimantarwa ta hanyar Imel. Da fatan za a duba wannan roko nawa. Bissalam. Sani Idris Kawo. Imel:  sandris67@yahoo.com

Malam Sani na samu bukatarka, sai dai kuma a halin yanzu babu wata rajista da na ajiye don yin haka.  Illa dai duk wanda ke bukatar wata kasida ta musamman wacce na san an dade da bugawa a shafin, wanda kuma watakila neman kasidar a shafin Intanet zai zama masa da wahala, sai in aika masa.  Amma babu wadanda nake aika wa kasidu ta Imel a duk mako. Domin idan na dauki wannan tafarki ba zan iya tabbata a kanshi ba, saboda yanayin aiki na.  Sai dai in har za ka iya, ka rika shiga shafinmu da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com don samun wadannan kasidun.  Hakan zai fi sauki.  Duk da cewa na dade ban loda wadanda aka ba tun farkon wannan shekara, zan yi kokarin yin hakan bayan sallah in Allah ya yarda, don baiwa irinka daman samun kasidun cikin sauki. Amma a yanzu kam a gafarce ni.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.