Sakonnin Masu Karatu (2011) (3)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

89

Gaisuwa ga Baban Sadik.  Dan allah me ye ke kawo kwayoyin cutar kwamfuta (Virus) a waya?  Daga zahra’u Kawo, Kano state.

Malama Zahra’u akwai dalilai masu yawa da ke haddasa samuwar kwayoyin cutar kwamfuta a jikin wayar salula.  Wasu daga cikinsu su ne, idan aka kwafa bayanai ta hanyar Bluetooth, muddin wayar da ke bayar da sakon tana dauke da wadannan kwayoyin cuta, to mai karba ma za ta kamu nan take.  Haka idan ta fasahar Infra-red ne.  Haka idan aka yi amfani da wayar debo bayanai a kwamfuta zuwa wayar salula, wato USB Cable. Idan kwamfutar da za ta bayar da bayanan ita ma tana dauke da kwayoyin cutar, dole wannan waya ta kamu nan take.

Haka idan kika yi amfani da ma’adanar bayanai ta wayar salula, wato “Memory Card” mai dauke da kwayoyin cutar a wayarki, nan take wayar za ta kamu.  Wadannan, a takaice, su ne shahararrun hanyoyin da wayar salule ke iya kamuwa da wadannan kwayoyin cutar kwamfuta, wato Virus.  Da fatan Malama ta gamsu.


Assalamu alaikum Malam, shin da gaske ne kowanne dan adam kalar zanen yatsunsa daban suke da na sauran yan adam?  Daga Sabiu Uba, New Nigeria, Jimeta/Yola

Malam Sabi’u wannan zance haka yake.  Kowane dan adam da ka gani yatsun tafukan hannunsa sun sha bamban da na wani daban, ko a ina yake kuwa. Kai ba ma wannan ba kadai, a duniya ba za ka taba samun mutane biyu masu kama ta kowane bangare ba, ko da kuwa ‘yan biyu ne. Idan ka kalle su kyakkyawar kallo sai ka gane akwai bambancin kira da tsarin jiki a tsakaninsu.  Wannan aya ce mafi girma da Allah ya samar a jikin dan adam, don yayi nazari kansu, ya san Ubangijinsa shi ne wanda ya cancanci bauta tabbas, ba wani ba.  Sanin hakan kuwa daga jikinsa shi yafi sauki. 

Wannan ne har wa yau ta sa masana suka kirkiri hanyoyin tantance zanen yatsun hannu ta hanyar amfani da na’urorin zamani.  Domin a duniya, kamar yadda ka ji, babu mutane biyu masu zanen hannu iri daya. Ba a taba ba ko a baya, ba a yi ba halin yanzu, sannan nan gaba ma Allah ba zai taba halittar mutane biyu masu zanen hannu iri daya ba.  Wannan na daga cikin cikakkun hikimomin Ubangiji a tsakanin halittarsa.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, don Allah Malam Abdullah ina neman karin bayani dangane da ilimin sararin samaniya, shin mene ne shi da turanci? Sannan mene ne “Girka” ko “Girkanci”? Daga Kabiru Yusuf Illela LG, Sokoto State.

Malam Kabiru, abin da kalmar “Ilmin Sararin Samaniya” ke nufi a harshen Turanci shi ne “Astronomy”, kuma shi ne fannin ilmin da ke lura da halittar duniya baki daya; da rana, da wata, da taurari, da dukkan halittun da Allah Ya sanya a tsakaninsu.  Kalmar “Girka” kuma, tana nufin kasar “Greece” ce ta yau.  “Girkanci” kuma na nufin harshen “Greek”; daya ne daga cikin harsunan duniya da suka fi dadewa.  Da fatan an gamsu.


- Adv -

Assalamu alaikum don Allah Baban Sadik ina son a min bayanin yanda ake yin hasashen rana da na ruwa? Allah ya kara basira. Daga Umar Honest man Numan, Jihar Adamawa.

Malam Umar bayani kan yadda ake hasashen yanayi gaba daya, ba abu ne da za a iya yinshi a wannan muhalli da yanayi.  Hakan na bukatar bincike da tantancewa.  Don haka idan Allah ya so za mu yi bincike na musamman kan hakan, don samar da abin dogaro na ilmi a kimiyyance, kuma cikin sauki.  A gafarce ni.


Baban Sadik barka da warhaka. Wata rana cikin shekarar 1995, muna kasar Chadi misalin shabiyu da rabi na dare, a cikin dokar daji, muna shan irin shayinsu sai wani abu ya bi ta samanmu yana huci, a guje. Yana  gudu fiye da gudun jirgi. Tsawonsa bai fi zira’i biyu ba, haskensa farin haske ne. Idan ya wuce inda kuke ganinka zai dauke gaba daya saboda tsananin haske. Ga kuma ban tsoro. Ko mene ne kuma wannan?  Daga Babangida: 08033966164

Ire-iren wadannan al’amura suna nan da yawa, wadanda a gaskiya babu wanda zai iya maka bayani cikakke kan ko mene ne, musamman idan ba a wurin yake ba. Akwai abubuwan mamaki masu faruwa a dukkan lokuta, kawai ya danganci wanda ka gani ne. Wani Malami dan kasar Masar mai suna Sheikh Ibrahim Ibrahim Al-Kurdee, ya rubuta wani littafi mai suna “Allamanil Kur’an, Min Aina Ataitu, Wa Ila Aina Aseeru”, inda a ciki ya taskance ire-iren wadannan abubuwan al’ajabi da suka faru da shi lokacin da yake yaro dan karami, ko waninsa, ko kuma wadanda ya karanta a jaridu, da wadanda masana kimiyya suka labarta da dai sauransu.

A takaice dai, ire-iren wadannan abubuwa ba kowa bane zai iya maka bayanin me suka kunsa, hatta cikin malaman kimiyya kwararru, sai da bincike, da bin kwakkwafi.  Allah sa mu dace, amin.


Dan Allah Baban Sadiq yaya zan yi wa wayata don mu’amala da fasahar Intanet. Domin duk sadda na shiga zan yi sai ta rubuto min cewa: GPRS not subscribed, ko kuma ta rubuto min: Connection failed.  Dan Allah yaya zan yi na magance wannan matsalar? Allah ya magance mana amin. Daga Shamsuddeenn Hamisu Maishinku Kano

Malam Shamsuddeen ai tuni wayar ta sanar da kai matsalar da take fuskanta.  Abin da ya rage shi ne, ka yi kokari ka bukaci tsare-tsaren waya masu taimakawa a yi mu’amala da Intanet, wato “Configuration Settings”, daga kamfanin wayarka.  Idan MTN ne kake amfani da shi, sai ka rubuta SETTINGS ka tura zuwa wannan lambar 3888. Nan take za a turo maka wadannan tsare-tsare.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik da fatan kana lafiya. Wato ni makarancin shafinka ne na Kimiyya da Kere-kere. A yau ina duba shafinka na bayanin kwakwalwar dan adam shi ne na ga inda kace “silbi” ne ko kuma “saibi” domin kalmar “saibi” bakuwa ce a Hausa.

To, Malam na gode da wannan gyara naka.  Sai dai kuma da ka sanar da ni cewa kalmar “saibi” (ba “silbi” ba rubuta ba) bakuwa ce, baka sanar da ni wacce ce ta dace in yi amfani da ita ba.  Sannan, ina ganin duk da cewa kalmar bakuwa ce, hakan ba ya hana a yi amfani da ita, muddin an sanya ta a muhallin da mai karatu ko mai sauraro zai fahimci sakon da ke cikinta.  Domin galibin kalmomin Hausa ai duk baki ne, wasu daga larabci, wasu kuma daga turanci.  Duk da haka na gode da wannan tsokaci naka.  Allah saka da alheri.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.