Sakonnin Masu Karatu (2013) (8)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

118

Salaamun alaikumu, ina fatan kana cikin koshin lafiya tare da iyali.  Ina daya daga cikin masu yabawa da kuma farin ciki da shafinka na kimiyya da kere-kere (shafi na 32) a jaridar AMINIYA.  Ina amfana matuka da dumbin  iliminka da baiwarka, a matsayina na dalibin harshen Hausa kuma mai sha’awar ilimin fasahar sadarwa ta zamani.  Tabbas!  Shafin ya dade da zama makarantar kimiyya da kere-keren AMINIYA ga Amintattun Daliban Hausa da Masu sha’awar Hausa da kimiyya da kere-kere.  Allah ya kara sani da daukaka, amin.  –  Aminu M. B. Umar, birnin Zariya: 08081224683

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Aminu. Na gode matuka da wannan sako naka. Kuma ina farin ciki matuka da ya zama abin da nake yi yana yin tasiri ta hanyoyi da wuraren da ban taba tunani ba. Bayan wannan tabbaci naka, a baya na samu sakonni da dama makamantan wannan. Akwai daliban harshen Hausa dake wasu daga cikin manyan Jami’o’in arewacin Najeriya da suka bukaci kusan dukkan kasidun da na rubuta a baya kan wasu fannoni, don amfani dasu cikin rubuce-rubucensu na karasa karatu. Allah yasa mu dace baki daya, ya kuma amfanar damu abin da muke karantawa a dukkan fannonin ilimi, amin. Na gode matuka.


Assalaamu alaikum, da fatan alheri, da kuma fatan samun babban rabo duniya da lahira.  Don Allah ina son sanin yadda ake neman bayanai ta Intanet; idan naje Google ko Wikipedia misali, zan shigar da Kalmar da nake neman bayani ne ko kuwa akwai wani tsari ne da ake bi?  – Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Tunshama Quarters, Kano: 0809558832

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Yahuza. Lallai neman bayanai a Intanet yana da tsari na musamman.  Abu na farko kuwa shi ne ka san me kake nema? Me kake so?  Wasu irin bayanai kake nema? Wasu kalmomi za ka yi amfani dasu don samun fa’ida kan haka?  Sannan a ina za ka samu manhajar da za ta saukake maka neman wadannan bayanai?  Dukkan wadannan tambayoyi suna bukatar amsa gamsasshiya, domin da zarar ka kuskure su, tun nan za ka rasa abin da kake so. Da farko dai, bayan ka haddade nau’in bayanan da kake nema, sai ka doshi gidan yanar sadarwa na musamman da aka tanada don neman bayanai. Wannan gidan yanar sadarwa yana dauke ne da manhajar neman bayanai cikin sauki, wadda ke iya fahimtar irin abin da kake nema ta hanyar kalmomi ko lambobi ko alamun da kayi amfani da su ko ka shigar.

Shahararre daga cikin ire-iren wadannan gidajen yanar sadarwar neman bayanai kuwa kamar yadda ka sani, shi ne gidana yanar sadarwar Matambayi Ba Ya Bata na kamfanin google, wato: Google Search Engine. Idan ka shiga sai ka sa kalma, ko kalmomi, ko jumlar da ke dauke da irin bayanan da kake so. A kiyaye, kada kayi amfani da doguwar jumla, domin ba za ka samu fa’ida ba. Haka idan shafin Babban Kamus din Intanet ka shiga, wato Wikipedia, za ka ga inda aka tanadi hanyar shigar da kalma ko kalmomi don tambayar irin bayanan da kake so. Sai ka shigar a wurin, ka matsa maballin “Enter” da ke jikin allon shigar da bayanan kwamfutarka, nan take za ka samu amsa. Allah sa a dace.


- Adv -

Assalaamu alaikum, barka da warhaka.  Allah ya taimaka.  Don Allah ina so a taimaka a turo mini bayani kan “Samuwar Bacci da Mafarki a Mahangar Kimiyya.”  Ga adireshin Imel di na: mlawan0@yahoo.com  –  08037156498

Wa alaikumus salaam, barka da warhaka. Sai ka/ki duba jakar Imel dinka/ki, na tura tuni. Allah sa a dace, ya kuma amfanar damu abin da ke muke karantawa. Na gode.


Assalaamu Alaikum Baban Sadik, Allah ya albarkaci zuriya da karin basira.  Rokona shi ne: da fatan za ka tattara dukkan kasidun da ka gabatar a kundin littafi na musamman don amfanin masu karatu.  – Jamilu Aliyu, Lafiya, Nassarawa: 08036927722

Wa alaikumusam, Malam Jamilu na gode da addu’o’i, Allah saka da alheri. A halin yanzu dai akwai kundun dukkan kasidun a shafinmu da ke Intanet, wanda adireshinsa ke saman wannan shafi. Dangane da abin da ya shafi buga littafi na musamman kuma sai nan tunani kan haka zai tsayu. Allah sa mu dace baki daya, amin.



Salaamun alaikum, ina da waya nau’in Sony Ericsson W800i mai dauke da babban katin ma’adanar waya mai fadi (extended memory card), ban son rabuwa da ita  saboda ma’adanar wayar, ko akwai wayar da ke irin wannan nau’in ma’adana?  –  08036799735

Wa alaikumus salaam, a gaskiya har yanzu ban ci karo da wata wayar salula mai dauke da nau’in ma’adanar SonyEricsson W800i ba, domin tsohuwar waya ce. Tun shekarar 2005 aka kera wayar. Haka ma ma’adanar tsohuwar yayi ce; yanzu an daina kera ire-irensu. A duk sadda kwanaki suka ci gaba da maimaituwa, kayayyakin kimiyyar sadarwa na dada tsukewa ne zuwa kanana, saboda samun saukin mu’amala da su.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.