Sakonnin Masu Karatu (2014) (1)

Yau ma kamar yadda aka saba, za mu duba sakonninku ne. Allah sa a dace, amin.

95

Barka da Sallah!

A yau ga mu dauke da wasu daga cikin tambayoyinku da na tattaro daga wurare da dama.  Akwai wadanda suka aiko tambayoyi ta hanyar lambar wayar dake wannan shafi, amma kasancewar katin SIM din ba a wayar salula yake ba (yana cikin Phantom Pad N9 ne, wata na’urar sarrafa bayanai mai kama da iPad), na samu hatsari irin na cikin gida, inda na’urar ta fadi kasa, shafin gilashinta na gaba (screen) ya yi raga-raga.  Ko na kunna ba na iya ganin komai.  Kuma wannan hatsari ya faru ne kwanaki biyu kafin tattaro wadannan sakonni, wannan yasa ban samu kaiwa ga wadancan tambayoyi naku da kuka aiko ta katin SIM ba.  Wanda kuma, abin baki ciki, su ne suka yawa.  Don Allah a gafarce ni.  Ba wai shikenan ba, bayan sallah zan kai ofishin kamfanin da ya kera na’urar don a canza mini wannan gilashi, sai in tattaro su.

Bayan haka, ina son jama’a su rika yawaita tambayoyi kan wasu fannonin ilimi da bayanansu ke gudana a wannan shafi, ba wai fannin kimiyya da fasahar sadarwa kadai ba.  Duk da cewa na san tasirin yaduwar na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani ne kan sa haka, kasancewar kowa na amfani da su kuma akan samu matsaloli yau da kullum.

A karshe, ina mana addu’ar Allha ya karbi ayyukanmu kyawawa da muka gudanar cikin wannan wata mai alfarma da yake mana bankwana, ya sa muna cikin ‘yan tattun wannan wata, amin.  Ina mana murnar BARKA DA SALLAH da ke tafe nan da ‘yan sa’o’i in Allah ya so.


Assalamu Alaikum, da fatan Baban Sadik na cikin koshin lafiya.  Don Allah yaushe za a ci gaba da fassara mana littafin “Why Astronomy”? – Faisal Muhammad

Wa alaikumus salaam Malam Faisal.  A gaskiya mun dakatar da batun fassara littafin a wannan shafi saboda wasu dalilai.  Amma akwai kokari na musamman don ci gaba da fassara shi, da kuma bugawa don yada shi cikin al’umma in Allah ya so.  Idan na gama tattaunawa da marubucin asalin littafin, wato Dakta Adnan Abdulhamid, in Allah ya yarda za a ci gaba da aikin a wannan tsari, ba a tsarin baya ba.  Ma’ana, idan batun bugawa ne, da zarar an buga zan sanar.  Akwai masu da dama suka tuntubeni kan wannan batu ba da jimawa ba, wasu ma sun bukaci in tura musu bangaren da na fara fassarawa wanda aka sa a shafin wannan jarida tamu mai albarka, na kuma tura musu.  Don haka da zarar na samu wani karin bayani da ba wannan ba, za ka ji ni ta wannan shafi ko ta dukkan shafukan da nake fadakar da masu karatun wannan shafi a duniya.  Da fatan ka gamsu


Assalamu Alaikum Baban Sadik, yaya azumi?  Ina fatan kana cikin koshin lafiya da kai da iyalanka?  Don Allah ina son ka banbanta mini tsakanin “Computer Laptop,” da “Computer Desktop” wajen mu’amala da keyboad, da mouse.  Sannan, wacce tafi saukin aiki? – Muhammad Auwal Koko Danbaba

Wa alaikumus salaam Malam Muhammad, barka da warhaka.  Da fatan kaima kana cikin koshin lafiya.  Idan aka ce: “Laptop Computer” ana nufin kwamfutar tafi-da-gidanka kenan, wacce za ka iya sanyawa a cikin jaka kayi tafiya da ita, sannan idan a zaune kake kana iya dora ta a kan cinyarka kayi amfani da ita.  Babban abin da take samar shi ne saukin mu’amala a lokuta daban-daban.  Shi yasa take dauke da batir mai taskance makamashin lantarki na wasu sa’o’i, kuma sauran bangarorinta duk an takaita su, don baiwa mai ita samun rike ta, da daukanta, da tafiya da ita, da kuma mu’amala da ita ko a cikin jirgin sama yake, cikin sauki da gamsuwa. 

- Adv -

A dayan bangaren kuma, idan aka ce: “Desktop Computer” ana nufin kwamfuta ce wacce ke dauke da dukkan bangorinta ko kamatsenta, daban-daban, wacce ba a iya mu’amala da wani bangarenta shi kadai kawai, dole sai da sauran bangarorin a wuri daya kuma a lokaci guda.  Galibi a saman tebur ake dora ta, shi yasa ake kiranta “Desptop” wato “Wadda ake dorawa a saman teburi.”  Sabanin kwamfuta nau’in tafi-da-gidanka (wato Laptop), ita “Desptop” galibin bangarorinta daban suke; sai an tashi mu’amala da ita ake jojjona mata su.  Kamar su allon shigar da bayanai (Keyboard), da Monita (Monitor), da uwar kwamfutar (System Unit), da beran kwamfuta (Mourse) da sauran komatse masu alaka da ita.

Tsarin mu’amala dangane da abin da ya shafi allon shigar da bayanai (Keyboard) da beran kwamfuta (Mouse) kamar yadda ka bukata, a fili yake.  Ita kwamfutar tafi-da-gidanka komai nata a wuri guda yake.  Duk da cewa za ka iya jona mata na’urar Beran kwamfuta don karin saukaka mu’amala, amma ko babu shi kana iya mu’amala da ita.  Amma a bangaren asalin kwamfuta kuwa, dole sai da Beran kwamfuta, sai in kwararre ne kai wajen iya mu’amala da kwamfuta.  Kowannensu na da saukin mu’amala, illa ya danganci kwarewarka ne.  Idan ka kware wajen iya amfani da kwamfuta kana iya samun gamsuwa wajen mu’amala da nau’in tafi-da-gidanka, wato “Laptop” kenan, domin za ka fi jin dadinta sama da asalin kwamfuta, sai in kana da wasu ayyuka na musamman da kake son yi a kan wancan babbar. 

Amma idan makoyi ne kai, zan bayar da shawarar ka lazimci nau’in “Desktop”, wato ta kan teburi kenan.  Ga makoyi, ta fi saukin mu’amala, kuma ta fi baka damar fahimtar hatta su kansu bangarorin kwamfutar, da aikin kowanne daga cikinsu.  Amma ita tafi-da-gidanka komai nata a matse yake, a hade yake, a cure yake.  Sai kwararre ke iya bambance su.  Sannan ko gyaran kwamfuta za ka koyi, dole sai da kwamfutar kan teburi za a fara koya maka, saboda galibin bangarorinta na bukatar karantarwa ta musamman, don su ma bukata na iya sa a nemi gyara su idan suka lalace.  Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum wa rahmatullah. Ina yi maka fatan alheri.  Malam ina tambaya akan yadda ake hada wayar tafidagidanka da kwamfuta domin yin kira na bidiyo.  Sannan wace waya ke iya wannan amfanin? – Aminu Umar Galadi

Wa alaikumus salam, Malam Aminu barka dai.  Ai ba na tunanin akwai wani tsari na sadarwa da kawai za ka iya don aiwatar da kiran bidiyo (Video Call) a tsakanin wayar salula da kwamfuta.  Sai in kana nufin masu dauke da Intanet ne da kuma masarrafar da ake iya aiwatar da kiran dasu.  Amma haka kawai, tsurar wayar salula da tsurar kwamfuta ba ka iya aiwatar da kira, dole sai da tsarin sadarwa na wayar salula (Mobile Network) da kuma yanayin sadarwa na Intanet da zai hada wadannan na’urori guda biyu da masarrafai ko manhajar da ke dauke a cikinsu.

A hakikanin gaskiya, da wayar salula da kwamfuta dukkansu tituna ne kawai.  Manhaja ko masarrafar (Applications) da ke dauke a cikinsu ne ke aiwatar da hakikanin abin da ake muradi na sadarwa.  Don haka, idan kana da wayar salula mai dauke manhajar kiran bidiyo (Video Call App), kana iya kiran abokinka da ke kan shafinsa na Facebook ta hanyar manhajar “Facebook Chat” wato masarrafar hirar ga-ni-ga-ka da ke shafin Facebook.  Idan ka budo windon dake dauke da sunan abokinka a wannan manhaja, ka duba sama daga bangaren dama maso tsakiya, za ka ga tambarin na’urar bidiyo sai ka matsa. Muddin yana da na’urar daukan hoto a kwamfutarsa (Webcam), nan take za a sanar dashi cewa: “Wane yana son hira da kai ta hanyar na’urar kira da bidiyo.”  Da zarar ya amince shikenan, sai ka fara ganin fuskarsa shi ma yana ganin naka, kuma hira ba matsala; iya gwargwadon karfin yanayin sadarwar intanet dake dauke cikin na’urorin naku.

To, ka ga a nan, ka aiwatar da wannan kira na bidiyo ne tsakanin wayarka da kwamfutar abokinka, amma dole hakan bai yiwu ba sai ta dalilin samuwar manhajar kira na bidiyo (Video Call App) da ke wayarka, da samuwar na’urar daukan hoto a kan kwamfutarsa, da kuma samuwar tsarin sadarwa na intanet a kan dukkan na’urorin naku gaba daya.

Bayan tsarin kiran bidiyo dake dauke a shafin Facebook, akwai masarrafai da yawa da aka gina masu iya gudanar da kira a tsarin bidiyo a kan wayoyin salula irin na zamani.  Akwai masarrafar Skype, wacce ta shahara a duniya, kuma da wannan masarrafa galibin tashoshin yada labarai na duniya na talabijin ke amfani don hira da jama’ar da ba za su iya riskuwa da su ba ta dadi sanadiyyar tazarar tafiya ko kurewar lokaci.  Akwai masarrafar Skype da ke kwamfuta, sannan akwai ta wayar salula.  Bayan Skype akwai masarrafar Vibo da ke galibin wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Android a halin yanzu.  Ba wadannan kadai ba, akwai wasu da yawa da idan ka bincika “Play Store” (idan kana amfani da Android ne) ko “Store” (idan kana amfani da Windows Mobile ne) za ka same su; wasu kyauta ne, wasu kuma sai ka biya.

Bazan iya gaya maka sunayen wadannan wayoyi ba don suna da yawa.  Illa dai a duk sadda kaje sayen waya kana iya gaya musu cewa kana bukatar wacce ke iya aiwatar da kira a tsarin bidiyo ne, za su baka.  Domin sun yawaita sosai kuma farashinsu ya sha bamban.  Ina iya gaya maka wata ya zama kudinka bazai iya mallaka ba, ko kuma za ka iya saya, amma ya zama tsarinta wajen kerawa da kamfanin da ya kera wayar bai maka ba.  Da fatan ka gamsu da wannan takaitaccen bayani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.