Sakonnin Masu Karatu (2014) (17)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

156

Salaamun alaikum, Baban Sadik Allah saka maka da alheri.  A gaskiya muna karuwa sosai da shafinka.  Bayan haka, wacce matsala ce take hana sako isa inda da aka tura?  Daga wayar salular ce, ko daga wajen wanda aka tura masa ne?  Na gode.  –  Muhammad Sharada, Kano.

Wa alaikumus salam Malam Muhammad, da fatan kana lafiya kaima.  Dalilan dake hana sakon tes isa ga inda aka aika shi suna da yawa.  Na farko, ko dai babu kudi ne isasshe a wayar, sakon bazai je ba.  Domin kamfanin waya na cajan kudin aikinsa ne da zarar ka baiwa wayar umarni wajen aika rubutaccen sako ko kira.  Idan akwai kudi isasshe a wayar, watakila babu yanayi mai kyau ne, wato “Mobile Network” kenan.  Don haka, kana iya nemo yanayi ta hanyar tsare-tsaren wayar, wato “Settings” ko ka kashe wayar ka sake kunna ta, za ta nemo da kanta.

Dalili na uku, in har akwai yanayin sadarwa mai inganci amma sakon ya ki zuwa, ta yiwu wajen latse-latsenka ko wani, ka goge lambar cibiyar sadarwar sakonnin tes, wato: “Message Center Number” kenan.  Idan lamba guda ta goge daga cikin lambobin dake wannan cibiyar karba da aika sakonnin tes, ko cikin kuskure ka kara wata lamba, to, babu yadda za ayi sako ya tafi. Wayar za ta rasa dalili, don haka sai ta daburce, ta ajiye maka sakonka a bakin kofa, wato “Outbox.”  Idan kana son gane haka, kaje “Settings” ka zarce “Messages”, sai kaje “Options”, za ka ga “Message Settings,” daga nan sai ka shiga.  A nan ne za ka ci karo da “Message Center” ka shiga.

Ya danganci nau’in wayarka da nau’in babbar manhajar wayar.  Idan ka shiga “Message Center”, idan wayar mai SIM biyu ce, za ka ga dukkan kamfanonin wayar (MTN da Etisalat, misali), sai ka matsa wanda ka tura sakon daga gare ta.  Idan MTN ce, za ka ga lambobi kamar haka: +234803000000.  Idan Etisalat ce, za ka ga: +2348090001518.  Idan Airtel ce, za ka ga: +2348020000009.  Idan kuma Glo ce, za ka ga: +2348050001501.  Wadannan su ne lambobin cibiyoyin aika sakonni na kamfanonin wayoyin da sunayensu ke biye dasu.  Sai ka kirga ka gani, duk wanda bai yi daidai ba, sai ka gyara.  Da zarar ka gyara, kana aikawa nan take sakon zai tafi, in Allah yaso.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, don Allah ina son ka turo mini da kasidar “Tsibirin Bamuda” ta wannan adireshin:  nafiubaliyu@gmail.com.  Allah taimakeka, na gode. 

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nafi’u, ka duba jakar Imel dinka, na aika maka kasidar tuni. Allah amfanar damu baki daya, amin.


Assalaamu alaikum, Allah ya taimaki Baban Sadik.  Don Allah ina son sanin ko ka wallafa littafi kan “Tsarin Mu’amala da Kwamfuta” (Computer Operations) da harshen Hausa?  In kuma ka wallafa, to a ina zan samu littafin? – Aminu Ringim.

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  A gaskiya kam ban rubuta wani littafi na musamman kan koyon mu’amala da kwamfuta ba.  Na dai rubuta kan tsarin mu’amala da fasahar Intanet, kuma shi ma ba a buga ko ba.  Akwai yunkurin buga kasidun da suka bayyana a wannan shafi, wanda shi ne abin da nake aiki a kai a halin yanzu.  Sannan akwai kokari wajen samar da kasida guda daya ta musamman, mai bayani kan abin da kake tambaya akai, dalla-dalla, don fahimtar Malam Bahaushe, wanda bai taba sanin mece ce kwamfuta ba.  Wadannan su ne abubuwan da na sa a gaba, ban kuma sa lokaci ba, saboda yanayin aikina.  Sai dai a ci gaba da bibiya ta lokaci zuwa lokaci. Allah sa mu dace baki daya, amin.


- Adv -

Assalaamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka.  Ina so ne ka mini tsokaci kadan kan Nokia samfurin Lumia, wato Windows Phone.  Ka huta lafiya.  – Aminu Muhammad

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Bayanai kan wannan nau’in waya ya sha maimaituwa a wannan shafi. Kayi hakuri, idan kana da kudura wajen iya mu’amala da fasahar Intanet, kana iya zuwa shafinmu dake Dandalin Facebook, wato “Dandalin Kimiyya da Fasahar Sadarwa” da ke wannan adireshi: http://www.facebook.com/kimiyyadafasaharsadarwa, don samun kasidu da amsoshin da na bayar kan wannan tambaya ko nau’in wayar salula.  Allah sa mu dace baki daya, amin.


Salam Baban Sadik, dan Allah ina so ayi mini karin bayani; ina da waya nau’in Tecno, amma a duk sadda na neni shiga Intanet sai ace mini: “Unsupported scripts in content.”  Daga baya kuma sai ace mini: “Memory full.”  Don Allah kayi mini karin bayani ta waya ta, domin a kauye nake, ban samun jaridar AMINIYA  a inda nake.  –  Babangida Kurma, ‘Yandaka, Ruma.

Wa alaikumus salam Malam Babangida, da fatan an wuni lafiya. Na fahimci sakonka sai dai za ka min uzuri, domin bayan cire sakonka daga waya ta, sai na mance ban adana lambarka ba, shi yasa na buga a jarida. Fata na shi ne Allah sa wani na kusa dakai ya gani don nusar dakai, ko kuma a dace ka ci karo da shafin.

Wannan sako da wayarka ke baka a duk sadda kayi kokarin shiga Intanet, ishara ne dake nuna ko dai babu cikakken ma’adana a wayarka (ma’ana, ma’adanar wayarka ta cike), ko kuma nau’in bayanan da kake son saukar wa wayar, bai dace da nau’in babbar manhajar dake wayarka ba.  Wannan shi ake kira “Incompatibility,” kuma hanya mafi sauki da za ka bi wajen ganin warware wannan matsala ita ce: ko dai ka share bayanan da ba ka bukata, wadanda suka yi babakere a ma’adanr.  In har matsalar rashin isasshen ma’adana ne, hakan zai warware matsalar nan take.  Amma idan kayi haka kuma ba a samu natija ba, to, sai dai kayi “Resetting” wayar, kuma dukkan bayananka za su goge, domin wayar za ta koma yadda aka kero ta asali ne.

In kana son yin hakan abu ne mai sauki; kaje “Settings”, ka gangara “Security” sai ka shiga.  A can karshe za ka ga “Restore to Factory Settings” ko wani abu makamancin haka, ya danganci kamfanin da ya kera wayar ko nau’in babbar manhajar.  Kana matsa “Restore to Factory Settings,” nan take za ta aiwatar.  Za ta kashe kanta, bayan ta gama kintsawa, sannan ta sake kunna kanta.  Sai ka saurara mata.

Muddin matsalar bata warware ba bayan bin wadannan hanyoyi, to a nan kam sai dai a hakura; domin alama ce dake nuna cewa dabi’ar wayar ko babbar manhajar wayar bata dace bane da nau’in bayanan da kake son saukarwa ko shigar wa wayar.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum, ranka ya dade.  Abubuwan alherin da kake yi muna godiya ga Allah ya kara tsare ka, ya kuma daukaka ka.  Wassalam. Daga mai goyon bayanka, Danazumi Gimba, Kankara. Ka huta lafiya.

Wa alaikumus salam, godiya nake matuka kan wannan tallafi na addu’a da karin kwarin gwiwa.  Allah saka maka da alheri kaima, ya kuma karbi ayyukanmu kyawawa, amin.  Na gode!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.