Sakonnin Masu Karatu (2016) (9)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

120

Assalamu alaikum Malam barka da warhaka.  Yaya aiki?  Allah mana jagora.  Malama, a ranar Talata, 20 ga watan Satumba, ina sauraron wata kafar yada labarai a wani shiri na gidan rediyon Freedom dake tabo siyasar duniya, sai naji sun tabo batun zuwan mamallakin kamfanin nan na sada zumunta na Facebook, wato: Mark Zukerberge da batun zuwansa Najeriya.  A nan naji mai gabatar da shirin na cewa: “Ya zo (wato Mark Zukerberge) amma ya karkata wani yanki na kasar har da masu gidan rana (kudi), amma babu wanda ya amfana a yankinmu na arewa.”  Sannan ya ce: Mark  ya ce za su duba yiwuwar sa wannan harshen a Hausa, duba da miliyoyin Hausawa masu karakaina a wancan dandali.  Shin, Malam wani kalubale ke gaban ‘yan arewa ta fuskar shugabanci da Magana da murya daya?  Kuma me hakan yake nufi ga wannan yanzu?  Domin ga mu dai da dimbin yawa a wannan dandali wanda mamallakinsa ya ce ya ga yawanmu?  Daga: Yahuza Idris Hotoron Arewa, Wuro Bogga, Kano: yahuzaii@yahoo.com

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Yahuza.  Bazan iya cewa komai kan batun zuwa da kudade da Mark yayi wannan kasa ba a yayin ziyararsa, domin ba ni da wata masaniya kan haka.  Dangane da batunka na biyu cewa akwai al’ummar Hausawa a wannan dandali kuma kamfanin na yunkurin zuba harshen Hausa cikin sahun harsunan dake kan dandalin, ko akwai wani yunkuri da muke yi a al’ummance don ganin cin nasarar wannan al’amari, in har na fahimci zance da kyau, zan iya cewa babu.  Domin ba wai a hukumance ko a al’ummance kamfanin Facebook ya bukaci ayi hakan ba.  Ka sani, kamfanin Facebook kamfani ne na kasuwanci, kuma yana da ‘yancin yabi hanyar da yake ganin ta dace da tsarin kasuwancinsa don neman kasuwa ko cin nasara.  Wannan ko kadan ba wani laifi bane.  Domin kamfanoni irin su Google da Microsoft sun yi ko ince suna ma yi.

A halin yanzu kamfanin Facebook ya samar da mahalli na musamman ga masu sha’awar fassara manhajojinsa zuwa harshen Hausa, don amfanin kansa da kuma fa’idar da yake tunanin al’ummar Hausawa na iya samu.  Amma tsari ne wanda kamar yadda na fada, ya samar dashi ne a bude; duk mai sha’awa yaje yayi.  Kwanakin baya Shashen Hausa na BBC dake Abuja sun tuntubeni kan wannan tsari da Facebook ya assasa, na kuma gaya musu ra’ayina.  Al’amari irin wannan yana tattare da bangarori biyu ne, ko manufofi iri biyu; na farko shi ne manufar inganta harshen Hausa, ta hanyar gyatta shi daidai da daidaitacciyar Hausa.

Manufa ta biyu ita ce don inganta tsarin kasuwancin kamfanin da ya samar da wannan tsari, saboda masu magana da harshen su samu hanya mafi sauki wajen ta’ammali da manhajarsa, shi kuma, a daya bangaren, ya samu karuwar jama’a wanda wannan zai taimaka wajen fadada masa kasuwancinsa.  Wannan manufa ta biyu, ita ce manufar kamfanin Facebook wajen samar da wannan tsari na fassara manhajarsa zuwa harshen Hausa.

Abin da ke tabbatar da hakan kuwa shi ne, bai samar da wani tsari na “tantance” kalmomin ba, ko jimlolin da ake zubawa a matsayin fassarar kalmomin turancin da yake amfani dasu a manhajar ba.  Wannan abu ne mai matukar hadari ga harshen Hausa.  Me yasa na fadi haka?

Na farko dai, harshen Hausa kamar sauran harsuna, yana da nasa ka’idoji da dokoki na ilimi da aka tabbatar dasu.  Dole ne duk wani harshe da za a fassara kalmominsa zuwa harshen Hausawa, ya dace da wadannan ka’idoji.  Hatta a fagen salon zance da karin Magana da sauransu, akwai ka’idar fassara mai suna: “Cultural Equivalence,” wanda ka’ida ce dake maye gurbin al’adun dake cikin harshen da ake fassarawa, da irin al’adun da ake fassara harshen zuwa gare shi, wajen ma’ana, ba tare da la’akari da ma’anar kalmar dake tabbatar da al’adar wancan harshe ba.  A halin yanzu dai ban ga wani tsari da zai lura da wannan bangare ba.  Kawai suna amfani da fahimtar masu amfani da wannan manhaja ne wajen yin hakan, ba masana harshen Hausa ba.

- Adv -

Abu na biyu shi ne, ko da an samu kwararre a harshen Hausa, dole akwai bukatar ya zama yana da sanayya mai zurfi, ba wai sani irin na kan titi ba, dangane da tsari da kintsi da kuma fannin sadarwa na zamani, musamman na’urorin da hanyoyin.  Galibin masu fassara wadannan kalmomi na manhajar Facebook jama’a ne kawai masu sha’awar abin, kadan daga cikinsu ne suka san kalmomin da suka dace ayi amfani dasu wajen fassara kalmomin.  Shi yasa ma sadda ma’aikatan BBC suka gayyace ni don tattaunawa kan wannan al’amari, suka ce sun duba wannan fassara da aka fara yi ta hanyar canza harshen manhajarsu ta Facebook daga Turanci zuwa Hausa, don ganin yadda abin ke tafiya, sai suka rikice, suka kasa fahimtar abin gaya daya.  Dole haka ta faru, domin masu yin wannan fassara ba su da sanayya kan  tsari da gudanuwar wadannan manhajoji da ma fannin baki daya.

Misali, wajen kalmar “Settings” sai na ga an fassara shi da kalmar “Saituna.”  Sai abin ya ban dariya.  Domin ba wanda zai fahimci abin da ake nufi da kalmar “Saituna”, saboda zahirin fassara ce aka yi wa kalmar “Settings”, ta hanyar aronta da jam’antata.  Wannan hadari ne mai girman gaske a rayuwar harshe.

Abu na uku, a ka’ida ko kwararre ka baiwa aikin fassara, dole ne ya zama ka samu wanda zai yi bitar fassarar, don tabbatar da cewa komai ya tafi daidai.  Wannan ba ya cikin tsarin kamfanin Facebook.  Dalilin kuwa daya ne, na kuma fada a sama, cewa manufar kamfanin Facebook shi ne don habbakawa da kuma inganta kasuwancinsa, ba don ci gaban harshen Hausa ba.  Ba ina nuna cewa hakan bai dace bane ayi, a a, ina nuna cewa hanyar da aka dauka ba dole bane ta samar da cikakkiyar fa’ida ga al’ummar Hausawa a Hausance, a ilimance.  Saboda manufar mai yin hakan ba shi ne inganta Hausa ba.

Don haka, ya rage ga al’ummar Hausawa ne su samar da wani tsari na musamman, wanda zai rika taimaka wa duk wani kamfani, na gida ne ko na waje, dake son shigar da harshen Hausa cikin tsarinsa na kasuwanci ta hanyar fassara, don samar da ingantaccen tsarin harshen Hausa wanda zai dace da zamani da kuma tsari da ka’idojin harshe a ilimance.  Wannan kuwa bazai yiwu ba sai an samu hadin gwiwa tsarin Malaman jami’a masana a harshen Hausa, da kuma kwararru a sauran fannonin ilimi daban-daban.  Amfanin malaman jami’a shi ne su tabbatar ba a yi wa harshen Hausa karan-tsaye cikin fassara ba, tare da bayar da kariya wajen taskance sababbin tsare-tsaren da suka shafi sababbin kalmomin da suka shafi fannonin ilimi daban-daban na zamani.

A nasu bangaren su kuma, sauran kwararru za su taimaka ne wajen bayyana hakikanin ma’anonin dake cikin kalmomin da suka danganci fanninsu na sana’a ko rayuwa.  Wannan shi ne kadai zai samar da tsari cikin lamarin.  Domin a halin yanzu bance akwai wani tsari da masana harshen Hausa a jami’o’inmu suka tanada wajen taskance sababbin kalmomi a fannonin ilimi na zamani ba.  Mun taba wannan hira da daya daga cikin malaman harshen Hausa a jami’ar Ahmadu Bello Zariya, inda ya sanar dani cewa lallai babu wani abu makamancin haka.

A sauran kasashe da suka ci gaba tuni sun yi nisa.  Sababbin kalmomin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani da kwamfuta, duk galibi an shigar dasu cikin manyan kamus na turanci da faransanci.  A wasu lokuta ma hatta kamus na wani fanni na musamman akwai.  Misali, akwai kamus na kalmomin Intanet zalla, wanda wasu masana suka rubuta.  Duk wata kalma da ta danganci fasahar Intanet an taskanceta a kamus din.  Amma mu a nan, sai dai kowa yayi ta yin kan gabansa.  Wasu ma ba su so a san sun samu wata kwangila na fassara; suna da kwarewar yi, ba su da kwarewar yi, wannan kuma sai sun gama an fitar duniya ake iya ganewa.  Wasu ma sau tari kalmomin da wasu suka rubuta suke kwashewa su zuba da sunan nasu.  Idan muka dubi galibin allunan tallace-tallace (Bill Boards) dake manyan biranen Arewacin kasar nan, kana ganin fassarar ka san wadanda suka fassara su, ko kadan, ba su da kwarewa a harshen.

A karshe, wannan shi ne kalubale da ke fuskantarmu a matsayinmu na al’umma.  Idan muka bari abin yaci gaba a haka, za a wayi gari ‘ya’yanmu da jikokinmu sun rasa madogara a harshen.  Domin galibin abin da ake karantar da mu a jami’o’i kan ka’idojin harshe ne; ta wace hanya za mu iya aron sababbin kalmomi, wani suna ya kamata a baiwa kalma da ta kebanci wani fanni, wasu ma’auni suka kamata ayi amfani dasu, me ya kamata ayi wajen taskance wadannan bakin kalmomi?  Wannan kuma watakila sai daga baya za mu fara tunanin yin hakan.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.