Sakonnin Masu Karatu (2017) (10)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

198

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan an sha ruwa lafiya.  Don Allah ina so ka turomin bayanan da kayi akan fannin “Tsarin Gadon Dabi’u da Siffofin Halitta” wato: “Genetics”.  Daga dalibinka Hassan Muhammmad Sani:  sanihassan727@gmail.com

Wa a alaikumus salam Malam Hassan, barka dai.  Kamar yadda nayi ta sanarwa a baya, a halin yanzu akwai shafi da na tanada a Intanet dauke da dukkan kasidun da suka bayyana a wannan na jaridar Aminiya, tun shekaru goma da suka gabata.  Don haka, kana iya zuwa wannan shafi don saukar da kasidar da kake bukata.  Idan kana bukatar kasidar a dunkule ne, kaje wannan rariyar dake: https://babansadik.com/dunkulallun-kasidu, akwai jadawali dake dauke da taken dunkulallun kasidu, ciki har da wanda kake bukata, daga hannun dama can kurya za ga shudiyar alama mai take: “Saukar,”  kana latsawa kasidar za ta sauka a kan wayarka ko kwamfutarka nan take.  Idan kuma karantawa kadai kake son yi a shafin, akwai daidaikum kasidu.  Kana iya faraway da na kashi farko dake wannan rariya: https://babansadik.com/tsarin-gadon-dabiu-da-siffofin-halitta-1, kana zuwa kasan kasidar, za ka ga taken kashi na biyu, a haka har zuwa sauran kasidar.

Allah sa a dace tare da amfana da abin da ake koyo, amin.  Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadik, Ubangiji Allah ya kara basira da kuma fahimta. Ni suna na Badamasi Alhassan Shanono, masoyinka.  elbassian@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Badamasi.  Ina godiya matuka da addu’o’inku tare da dimbin kauna da ake nuna mini.  Ina rokon Allah ya hada fuskokinmu da alheri, tare da kara dankon zumunci.  Na gode matuka.


- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik barka da aiki, ya azumi?  Da fatan za ka sha ruwa lafiya. Baban Sadik lambobin da ake samarwa na katin waya wani irin lissafi ne ake amfani da shi? A gaida min da Sadik.  nasirukainuwahadejia1@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Nasiru, fatan kana cikin koshin lafiya.  Ina kuma godiya da addu’o’i kamar yadda aka saba.  Akwai hanyoyin samar da lambobi mabambanta a lokaci guda kuma a hargitse, da yawa.  Wannan tsari shi ake kira: “Random Number Generation,” kuma dukkan yarukan gina manhajar kwamfuta (Programming Language) suna da wadannan hanyoyi.  Ban iya sanin da wani yaren gina manhaja ne aka gina wadannan manhajoji da ake amfani dasu wajen samar da wannan lambobi.  Sai dai abin da yake bayyane shi ne, lallai akwai wannan tsari a bangaren yarukan gina manhaja.  Kamar yadda na sha fada a baya, wannan aiki ba wani abu bane mai wahala ga kwamfuta.  Masana sun sha nanata cewa in akwai wani aikin da bai wa kwamfuta wahala, to, shi ne lissafi ko kuma samar da lambobi kai tsaye.

Wadannan lambobi da ke wakiltar kudin katin waya (Recharge Card Credit Unit), ana samar dasu ne a hargitse (wato: “Randomly”), bayan an rubuta farashin da ake so su wakilta kenan.  Ma’ana, idan ana bukatar samar da lambobin da zasu wakilci katin cajin waya na naira 500 misali, za a fara shigar da farashin ne, sannan a umarni kwamfuta ta samar da lambobi a rukuni kaza (misali rukuni 4: 2152-3656-5866-7878), guda kaza (wato yawan katin kenan).

Sannan kowane kamfanin waya ya kebanta da nashi ne.  Kowane rukun lambobi dake wakiltar kudin katin waya yana kebantuwa ne da kamfanin da ya samar dashi.  Shi yasa baza ka iya daukan lambar katin wayar kamfanin MTN ka shigar wa kamfanin Airtel ba.


Assalamu alaikum Da fatan kana lafiya Allah yasa hakan amin.  Don Allah a taimaka min da kasidar “Bamuda Triangle”.  Daga Imrana Lawan Gwammaja. imrn148@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Imrana.  Za ka iya samun wannan kasida a shafin da na kebance don taskance dukkan kasidun da na rubuta a wannan jarida mai albarka.  Idan gaba dayan kasidar kake so a dunkule, kana iya ziyartar sashin da na tanadi dunkulallun kasidu don saukar da wannan shahararriyar kasida, a wannan rariyar likau: https://babansadik.com/dunkulallun-kasidu, sai ka gangara cikin taken kasidun, idan kaci karo da wanda kake nema, sai ka duba can kurya daga dama, akwai alama mai dauke da: “Sauke”, kana latsawa za a saukar maka da kasidar a kan waya ko kwamfutarka.  Idan kuma kana son kasidar kashi-kashi ne, kana iya cin karo da kashi na daya a wannan rariya: https://babansadik.com/binciken-malaman-kimiyya-kan-tsibirin-bamuda-1.  A karshen kasidar za ka ci karo da taken kashi na 2, har zuwa kashi na karshe dai.  Allah sa a dace ya kuma amfanar da mu abin da ake koyo, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Maman Abdulsamad says

    Salamu Alaikum, Sannu Da Kokari Baban Sadik, Babu Wata Kalma Da Zata Iya Fayyace Murnata Da Godiya Akan Wannan Gagarumin Aiki Da Kayi Awannan Shafi Mai Albarka Da Matikar Amfanarwa Ga Al’umma Musamman Dalibai Kai Da Ma Daukacin Jama’a La’akari Da Yadda Mu’amala Da Kwamfuta Da Wayar Salula. Allah Ya Kara Maka Fahimta Da Hikima,ilimi Da Basira, Masha Allah Barakallah Fika. Mungode Mungode Mungode. Daga Maman Abdulsamad Gombe State

Leave A Reply

Your email address will not be published.