Sakonnin Masu Karatu (2017) (27)

Ci gaban sakonnin masu karatu. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

88

Salaamun alaikum. Da fatan alheri a garemu baki daya.  Kwamfiyuta ta ce kirar “DELL”, kwana biyu take min wani abin da ba na ganewa.  Idan na kunna ta da safe ba zata kawo ba sai ta dauki lokaci kamar wajen awa daya ko fiye da haka kafin ta kawo.  Sannan ta sake daukan lokaci kafin ta bude.  Na kai wajen gyara akace mini wai  “PROCESOR” na ne ya lalace, aka canja.   Amma duk da haka bata daina ba na koma aka sake cewa wai “POWER PACK” ne ya samu damuwa shi ma aka canza, amma duk da haka bata daina ba.  Meye abin yi?

Wa alaikumus salam, barka dai.  Daga bayananka, akwai alamar kwamfutarka ta kusan kwanta dama.  Ma’ana ta kusa mutuwa murus.  A ka’ida bai kamata a ce kwamfuta na daukan kusan awa guda ba, kafin ta gama kunnuwa.  Kamar yadda kace, a karon farko masu gyara sun ce laifin “Processor” ne, daga baya kuma suka ce laifin “Power Pack” (ko kuma “Power Supply Unit” – PSU), hakan na nuna cewa matsalar da kwamfutar ke fuskanta ba daya bace; matsaloli ne masu dimbin yawa.  Kasancewar baka min bayani nau’in kwamfutar ba, da nau’in babbar manhajarta ba, da kuma tun yaushe ta fara wannan dabi’a ba, bazan iya cewa ga hakikanin abin da ke damunta ba. 

Zai iya yiwuwa tsohuwar kwamfuta ce da zamaninta ya shude, amma aka dora mata babbar manhajar kwamfuta na zamanin yau.  Wannan zai iya jefa ta cikin wannan yanayi.  Zai iya yiwuwa kuma ka yi ‘yan shige-shige ne da ita a Intanet, ko ka jojjona mata ma’adanar Filash ko babbar ma’adanar kwamfuta na waje (External Hard Drive) masu dauke da kwayar cutar kwamfuta (Computer Virus) har suka cakume ta; wannan na iya jefa ta cikin wannan yanayi.  Har wa yau zai iya yiwuwa kuma duk ba dayan wadannan dalilai, tana dai fama ne da karancin ma’adanar wucin-gadi (RAM), shi ma yana iya jefa ta yanayi makamancin wannan.  Wadannan kari ne, kan wadancan dalilai guda biyu da mai gyara ya baka.

Ni dai shawarata ita ce, in dai tsohuwar kwamfuta ce wacce ta ji jiki, to, canza ta kawai shi yafi zaman lafiya.  Amma kuma idan ba tsohuwa bace can, kana iya canza wajen mai gyara, ka samu wani kwararre wanda ya san kan kwamfuta, ba wanda zai rika kirdadon matsalarta ba, don gano hakikanin abin da ke damunta, ko kuma, a karshe, ya baka shawarar kan abin da ya kamata kayi.

Wannan shi ne abin da zan iya cewa.  Ina maka fatan alheri da dacewa wajen samun maslaha ga wannan baiwar Allah mai fama da cututtuka kala-kala.  Da fatan ka gamsu da gajeren jawabina.  Na gode. 


Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya tare da iyalanka, allahumma amen.  Ni ma’abocin karanta kasidarka ne a shafukanka da dama.  A halin yanzu ina da takardar shedar gama sakandare kuma ina da sha’awan karatun kwamfuta ta zamo ita ce ta gaba, duk da kuwa bani da wata masaniya game da kwamfuta a aikace sai dai a karance, ta hanyar kasidunka da nake karantawa.  Wannan dalili yasa nake neman shawara a gareka da ta ina ya kamata in fara?  Ni ne dalibinka:  Amiru Usman, daga Lafia Nasarawa State

- Adv -

Wa alaikumus salam, Malam Amiru Usman.  Na yi farin jin irin tasirin da wannan shafi namu yayi a kanka wajen zaburar dakai don neman karin ilimi a wannan fage mai matukar tasiri a duniyar yau.  Shawarata ita ce, akwai makarantu ko wuraren horar da masu sha’awa a wannan fanni, a aikace, wato: “Computer Training Centers” kenan.  A wadannan wurare kana iya yin ‘Certificate’ ko “Diploma” a fannin, kuma a aikace.  Ma’ana, kafin ka gama, za ka iya sarrafa kwamfuta wajen kunnawa da kashewa, da yin rubutu da lissafi da zane da kuma yadda ake taskance bayanai da fitar dasu ta hanyar na’urar buga bayanai, wato: “Printer.”

Halartar wannan cibiya zai taimaka maka ta bangare biyu.  Bangaren farko shi ne, za ka samu kwarewa a aikace, tare da shedar gama karatu.  Bangare na biyu kuma za ka samu karin sha’awa da son abin a zuciyarka.  Idan kana ganin baka san komai bane, sai ka je wurin za ka ga wadanda ka fi su.  Da zarar ka samu wannan kwarewa, ba sai na gaya maka abin da zaka yi nan gaba ba.  Tuni za ka samu shawarwari daga wajen malaman da suka koyar daku.

Wannan ita ce shawarata gare ka.  Fanni ne da ke bukatar aikata abin da aka koya ko karanta.  Nazari a takarda kadai ba ya isarwa ko gamsar da dalibi.  Ina maka fatan alheri a duk inda ka samu kanka, tare da rokon Allah ya baka juriya da jajircewa a wannan fage.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya amin. A baya na maka tambaya amma baka amsa ba.  To ga ni tafe da wata tambayar. A kasidunka da kayi bayani game da yadda za’a koyi ilimin gina manhajar kwamfuta wato “Programing,” ka ce sai mutum yana da wata kwarewa na sarrafa kwamfuta kafin ya kai kansa ga koyon wannan bangare.  Sai dai baka fadi wata irin kwarewa ya kamata ace mutum ya samu kafin ya fara koyon ba. Kuma, mutumin da yake da kwarewa da ake samu a makarantun nan na kan titi zai iya afkawa ga koyon wannan bangare ko kuma akwai matakin da ya kamata mutum ya kai kafin ya kai kansa ga koyon wannan bangare na programming?  Ka huta lafiya.  Dalibinka wato: Amiru Usman

Wa alaikumus salam Malam Amiru.  Lallai watakila baka ci karo da cikakken jawabin da na baiwa mai tambaya ba.  Na tabbatar da cewa dole sai ka iya sarrafa kwamfuta, wajen kunnawa da kashewa da iya rubutu a kai tare da sanin yadda ake sarrafa ta tukun.  Afka wa ilimin “Programming” ba tare da sanin yadda ake iya sarrafa kwamfuta ba, zai zama tsallen badake.  Kamar mutum ne bai iya tuka mota ba, amma yayi rajista a makarantar tsere da motoci.  Ka ga ganganci ne wannan, kuma babu wata fa’ida da za a iya samu, sai ma cutarwa.

Dangane da tambayarka ta biyu cewa ko mutum na iya wadatuwa da irin horaswar da ake samu a makarantun kwamfuta na kan titi, amsar ita ce: eh.  Muddin ka san yadda ake sarrafa kwamfuta da yadda take aiki, musamman yadda ake shigar mata da bayanai da yadda ake nemo su, babu laifi.  Bayanin yaya za ayi mutum ya fara wannan karatu kuwa yana cikin jawabin tambayarka ta farko, wacce ke saman wannan amsar.  Da fatan ka gamsu, kuma Allah sa a dace, amin summa amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.